Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gobara ta hallaka Falasdinawa sama da 20 a Gaza
Mutane akalla 21, wadanda suka hada da yara, gobara ta hallaka a wani gini da ke sansanin ‘yan gudun hijira mai tarin jama’a a Zirin Gaza, kamar yadda darektan wani asibiti ya shaida wa BBC.
Akwai alamun yawan wadanda wutar, wadda aka shawo kanta, ta yi sanadiyyar mutuwar tasu a sansanin Jabalia su karu in ji Dakta Salah Abu Laila.
Wani jami’in tsaro ya gaya wa BBC cewa binciken farko-farko da aka yi ya nuna cewa an samu bullar iskar gas din girki daga wani dakin dafa abinci.
Jami’in ya ce iyalan na bikin murnar wani daga cikin ‘yan uwansu ne da ya komo daga kasar waje.
Jabalia na daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira takwas a Gaza, yankin da yake da mutum miliyan biyu da dubu dari uku a cunkushe.
Dakta Abu Laila, wanda shi ne darektan ayyukan agajin gaggawa a asibitin Indonesia da ke arewacin Gaza, ya bayyana gobarar da cewa gagaruma ce.
An ga hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta da muhawara na nuna yadda wutar ta mamaye ginin gaba daya.
Wani dan yankin da ya garzaya domin bayar da taimako ya ce akwai man fetur da aka ajiye a ginin domin injin jannareto.
Wani da ya ga lamarin ya ce yanayin ba kyawun gani, ‘’ za ka ga yara da mata na cin wuta kuma ba yadda za ka iya cetarsu."
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas wanda ke zaune a yankin Gabar Yamma, wani yanki na daban na Falasdinawan daga inda gobarar ta tashi ya kira lamarin a matsayin bala’i na kasa, ya kuma ayyana Juma’a a matsayin ranar makoki.
Babban Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar fafutukar ‘yancin Falasdinawa ta PLO, Hussein Al-Sheikh, a wata sanarwa ya ce hukumar Falasdinawa ta bukaci Isra’ila ta bude mashigar Erez da ke tsakani da Gaza domin kai wadanda suka ji rauni asibiti idan har hakan ya zama dole.
Ministan tsaro na Isra’ila Benny Gantz ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ma’aikatansa za su taimaka wajen kwashe wadanda suka ji rauni zuwa asibitocin Isra’ila.
Ana yawan samun tashin mummunar gobara, wadda yawanci kyandar ke haddasawa a Gaza saboda yawan dauke wutar lantarki.
Wannan na faruwa ne kuwa saboda datse yankin da Isra’ila da Masar suka yi da kuma rikicin siyasa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa.
Gaza na da mutane miliyan biyu da dubu dari uku, abin da ya sa ta kasance daya daga cikin wuraren da suka fi cunkuson jama’a a duniya.
Kuma kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akwai ‘yan gudun hijira kusan dubu dari shida da ke zaune a sansanonin da ke da cunkoson jama’a har guda takwas.
A kiyasi akwai sama da mutum 5,700 a duk yanki mai fadin murabba’in kilomita daya.
Wanda hakan kusan daidai ne da yawan tarin al’ummar Landan, amma kuma yawan ya karu da sama da mutum 9,000 a birnin Gaza.