United ta rike wuta kan Felix, Chelsea za ta sayi Thuram

Asalin hoton, OTHER
Atletico Madrid na bukatar Manchester United ta biya fam miliyan 9.5, idan har tana son daukar Joao Felix matsayin aro, ko kuma ta biya fam miliyan 70 ta saye shi gaba daya, in ji Sunday Mirror.
Tsohon kocin Everton da Belgium Roberto Martinez ya cimma yarjejeniyar fatar baki da Portugal don horar da tawagar.(Athletic).
Sai jaridar L'Equipe, wadda tace Zinedine Zidane ya ki amsa tayin horar da tawagar kwallon kafar Amurka.
Tottenham na harin golan Everton da Ingila Jordan Pickford, don ya maye gurbin kyaftin dinta Hugo Lloris, in ji Sunday Mirror.
Al Nassr ta saki dan wasan gaban Kamaru Vincent Aboubakar, wanda Manchester United ke nema, kuma ta yi hakan ne don samar wa Cristiano Ronaldo gurbi a kungiyar.(Al-Riyadh).
Crystal Palace ta shirya gogayya da Everton wurin sayen dan wasan Aston Villa, Danny Ings. (Sun)
Ana rade radin cewa dan wasan gaban Brighton Leondro Trossard zai iya komawa Chelsea ko Newcastle.(The Athletic).
Chelsea ta fara tattaunawa da Borussia Monchenglabad don ganin yiwuwar sayen dan wasan gabanta, Marcus Thuram, a watan Janairun da ake ciki, in ji Fabrizio Romano.
A wata mai kama da haka, Shugaban Brighton Albion din Paul Barber, ya gargadi Liverpool da Chelsea cewa, duk mai son daukar Moises Caicedo daga cikinsu ya shirya biyan makudan kudi.(Metro).
Anan kuma Sky Sports ce ta ruwaio cewa Leeds na neman dan wasan gaban Hoffenheim, Georginio Rutter mai shekaru 20.











