Wani sojan ruwa ne ya jagoranci yunkurin juyin mulki a Gambia - Gwamnati

Asalin hoton, Getty Images
An bayyana cewa wani sojan ruwa ne ya jagoranci yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Gambia.
An tsare sojan ruwan mai suna Lance Corporal Sanna Fadera, tare da wasu sojoji uku - daga rundunar sojin ruwa, da bataliyar da ke gadin fadar shugaban kasa da kuma sojojin kasa, a cewar wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin kasar.
Wani tsohon sojan kasar ya ce yana ganin babu kanshin gaskiya a yunkurin juyin mulkin.
Har yanzu sojojin da ke biyayya ga gwamnati suna can suna neman sauran sojin uku da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulkin.
Babu cikakken bayani game da hakikanin abin da ya haddasa yunkurin juyin mulkin na ranar Talata da zummar kifar da gwamnatin Shugaba Adama Barrow, wanda ya yi nasara a zabe karo na biyu a shekarar da ta gabata.
An san Gambia a matsayin kasar da ake kwanciyar hankali inda masu yawon bude ido ke tururuwa cikinta domin kallon namun daji da hutawa a bakin tekuna.
Hankula a kwance suke a Banjul, babban birnin kasar, inda kowa yake gudanar da rayuwarsa kamar yadda aka saba.
Ba a ji karar harbe-harben bindiga ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa an aike da dakarun da ke biyayya ga gwamnati wurare na musamman domin ba su kariya.
Sai dai sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce an aike da sojoji cikin shirin ko-ta-kwana domin sanya idanu a wasu wurare.
"An shawo kan lamarin baki daya," in ji sanarwar.
Sojoji sun musanta yunkurin juyin mulki a yayin da labarin ya fito ranar Talata, suna masu cewa sun gudanar da "atisayen soji" ne kawai.
Mr Barrow ya doke tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh, wanda ya dade a kan mulki, a zaben da aka gudanar a watan Disambar 2016.
An tilasta wa Mr Jammeh yin gudun hijira zuwa Equatorial Guinea, ko da yake har yanzu yana da karfin fada a ji a Gambia.
Manyan jami'an soji da dama sun bar aiki bayan Mr Barrow ya sha rantsuwar kama aiki.
Ya ki sakar jiki da sojoji, kuma ma sojojin Senegal da ke makwabtaka da kasarsa ne suke tsaron lafiyarsa, yayin da sojojin Najeriya da Ghana suke gadin filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwan kasar.











