Juventus ta ce kutse aka yi mata batun ɗaukar Arda Guler

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta ce an yi mata ƙutse cikin ɗaya daga shafukanta ya sada zumunta a jiya Litinin.
Hakan na zuwa ne bayan magoya bayanta sun fara murna kan bayanin da aka wallafa na ƙarya, na cewa za ta sayi ɗan wasan Real Madrid ɗan ƙasar Turkiyya Arda Guler.
Duk da cewa kasuwar musayar 'yan wasa a Turai rufe take, amma labarin ya rikita magoya bayan Juventus, saboda hoton ɗan wasan da aka sa a X, rike da jaka a filin jirgin sama ya nufi Italiya.
A saman a rubuta barka da zuwa Juventus Arda Guler.
Juventus ta ce magoya bayanta su yi watsi da labarin wanda ta ce na ƙanzon kurege ne.
Ko da Juventus na son ɗaukar ɗan wasan ba za ta iya ba har sai nan da watan Janairu saboda a lokacin ne ake sake buɗe kasuwar na wasu 'yan lokuta.
Real Madrid ta ɗauki Guler daga Fernabahce a Yulin 2023 kan kudin da aka ce sun kai yuro miliyan 20.
Ya buga wa ƙungiyar ta Spain wasa 23 kuma yana cikin tawagar Turkiyya ta Euro 2024.
Dan wasan ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya ci kwallo a wasansa na farko a gasar Turai, lokacin da ya ci wa Turkiyya kwallo ta biyu a wasan da ta ci Georgia 3-1.











