Abubuwa biyar da ke sanya matasan Najeriya rungumar tsattsauran ra'ayi

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙarfin da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi ke da shi a Najeriya da ma yankin Sahel baki ɗaya na barazanar ta'azzara rikicin jin ƙai da kuma rura wutar rashin zaman lafiya a duk faɗin Afirka, wanda ke haifar da babbar barazana ga tsaron ƙasashe da kuma mutanen yankin.

Durkushewar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa da ake samu a yunƙurin da ake yi na yaƙi da ta'addanci ya bar wata kafa da masu tsattsauran ra'ayi ke amfani da ita wurin yaɗa manufofinsu da kuma samun ƙarin mabiya, musamman tsakanin matasa.

Tuni dai ƙungiyoyi irin su Jama'at Nusrat al-Islam wal Muslimeen (JNIM) da Islamic State in the Greater Sahara (ISGS), da Islamic State in West African Province (ISWAP), da sauransu suka yi amfani da wannan dama, suna ƙara faɗaɗa ayyukansu, inda suke amfani da ƙasashen yankin a matsayin dandalin ƙaddamar da hare-haren kan dakarun gwamnati da fararen hula.

Masana harkokin tsaro irin su Kabiru Adamu na Kamfanin Beacon security and intelligence Limited a Najeriya sun yi ƙoƙarin duba wasu dalilan da suke taimakawa tasirin tsattsauran ra'ayi a ƙasashe irin su Najeriya da ma yankin sahel ba ki ɗaya musamman tsakanin matasan da ke waɗannan ƙasashe.

1. Talauci

Talauci da rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke jefa matasa su karkata zuwa ga tsattsauran ra'ayi. A cewar Dr Kabiru Adamu, bincike ya nuna cewa kusa kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na matasan da ke yankin arewacin Najeriya da yankin sahel baki ɗaya suna fama da matsalar talauci da rashin hanyoyin samu kuɗi.

Ya ce :''Akasarin matasan da ke wannan yankin ba su da aikin yi, kuma waɗanda ma suke da aikin yi ayyukan ba su wadatar da su ba, ma'ana abin da suke samu ba ya isar su.''

Masanin ya ƙara da cewa wannan matsala ita ke bai wa ƴan bindiga da sauran ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi damar cusa wa matasa ra'ayin da su ke so ta hanyar kwaɗaitar da su kan abubuwan da za su iya ba su ta fannin kuɗi da sauran abubuwa na rayuwa.

2. Rashin adalcin gwamnati

Matasa da yawa a fusace su ke saboda abin da suke kallo a matsayin wariya ko zalunci da ake yi musu daga hukumomi, da batun cin hanci da rashawa, da kuma ganin cewa ana ware su a siyasance. Misalan irin wannan rashin adalci zai iya zama wani zalunci da jami'an tsaro suka yi wanda zai iya ingiza matasa zuwa ga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi don samun abin da suke ganin zai ba su damar aikata ramuwar gayya.

''Bincike ya nuna cewa zargin da ake yi wa wasu jami'an tsaro na danne haƙƙin mutane ya kasance babban dalilin da ke jefa matasa cikin tsattsauran ra'ayi, soboda suna ganin ta haka ne za su iya ɗaukar fansa kan rashin adalcin da suke ganin an nuna musu,'' in jin Adamu.

3. Taɓarɓarewar tarbiyya

Sau da yawa makusantan matasa ne ke janyo hankulansu zuwa samun wata aƙida da za ta iya zama tsattsaura. Rashin samun ingantacciyar tarbiya, da rashin samun mutanen ƙwarai a dangi da za a iya koyi da su na ƙara wa matasa rauni da har za su iya sauraron masu irin wannan ra'ayi, har su iya shawo kansu.

A wasu lokutan kuma akan samu cewa daga irin tarbiyar da ake bai wa wasu tun daga gida ake cusa musu ra'ayin kuma a haka suke tasowa su girma da shi.

4. Addini

Yayin da ake yawan ambaton addini a matsayin tushen kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, Dokta Kabiru Adamu ya bayyana cewa bincike ya nuna ana amfani da addini ne a matsayin matakin janyo hankalin jama'a, amma ba shi ne ginshiƙin abin da ya ke sanya mutane shiga irin wadannan ƙungiyoyi ba. A cewarsa addini bai kai sauran dalilan da aka ambata tasiri ba.

Ya ce: ''Duk da ya ke waɗannan ƙungiyoyi suna iƙirari kuma suna amfani da addini, amma bincike ya nuna cewa ba kasafai suke nasara ba idan suka tsaya kan batun addinin kaɗai sai idan an samu sauran dalilan da muka lissafa a baya tukunna kafin su ke kai wa ga nasara.''

5. Rashin samun ababen more rayuwa daga gwamnati

Matasa da suke ganin kamar gwamnati ta manta da su ta ɓangaren samar da ababen more rayuwa ga al'ummominsu, musamman idan suna ganin kamar daman akwai alamun rashin adalci gwamnatance.

''Idan akwai wani banagare na ƙasa ko al'umma da suke ganin ba a yi da su, ko kuma ba a ba su haƙƙinsu ko kuma ba a biya musu wasu bukatunsu, wannan lamari yana bayar da dama ga ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi,'' In ji Dokta Adamu.

Matakan magance matsalar

Dokta Kabiru Adamu ya yi bayanin cewa tuni gwamnatocin ƙasashen, kamar su Najeriya suka fara shirin aiwatar da shirye-shirye na musamman da ke da niyyar magance wannan matsala ta matasa masu tsattsauran ra'ayi, inda ya ce hukumomi a Najeriya sun fitar da wata taswira wadda za ta taimaka musu wurin yaƙi da wannan matsala.

Ya ce: ''Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro sashen yaƙi da tsattsauran ra'ayi sun wallafa wani tsari da ake kira 'strategic plan 2025-2030', kuma a ƙarkashinsa an ware hanyoyi da yawa, kuma yawancinsu matakai ne na ƙoƙarin juya waɗannan abubuwa da mu ka riga muka lissafa a baya wanda suka haɗa da:

  • Yaƙi da talauci da rashin ayyukan yi
  • Hanyoyin hana cin zarafi daga ɓangarorin jami'an tsaro ko hukumomin gwamnati
  • Inganta zamantakewa na iyali da tarbiya a cikin al'umma
  • Tabbatar da malaman addini sun tantance irin wa'azi da suke yi domin shafe waɗansu aƙidu da ka iya sauya ra'ayoyin matasa.
  • Tabbatar da cewa gwamnati ta inganta al'amuranta ta hanyar samar da ababen more rayuwa da kuma yin adalci a tsakanin al'umma.