'Tilas ce ta sa muka je Hajji ta ɓarauniyar hanya'

Wasu alhazai kenan a kan Dutsen Arafa yayin aikin Hajji na 2023

Asalin hoton, ASHRAF AMRA/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Bayanan hoto, Wasu alhazai kenan a kan Dutsen Arafa yayin aikin Hajji na 2023

"Sun shiga gidanmu da asuba suka karya ƙofofi," a cewar "Saber" - wani matashi ɗan Masar wanda mahaifiyarsa da 'yar'uwarsa suka je aikin Hajji a bana riƙe da bizar ziyara, wadda hukumomi suka haramta zuwa Hajji da ita.

Saber wanda ba sunansa na gaskiya ba ne, ya faɗa wa BBC cewa jami'an tsaron fararen hula tare da 'yansandan Saudiyya sun ƙwanƙwasa ƙofofin gidajen da ke wani rukunin gidaje a Makka da ƙarfe 4:30 na asuba duk wanda ya ƙi buɗewa za su "karya ƙofar", kamar yadda ya bayyana.

Ya ƙara da cewa: "Dakarun sun shiga ɗakunan mata ba tare da girmama su ba kuma suka ɗauki dangina da wasu a bas bas biyu zuwa Al-Shumaisi" - babbar tashar gaɓar ruwan Makka.

Sai dai wasu 'yansanda biyu sun ce sun yi ta ƙwanƙwasa ƙofar amma ba a buɗe ba shi ya sa suka kutsa kai ciki. Mun yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumomin Saudiyya game da lamarin amma ba su ce komai ba.

Babban jami'in kula da tsaron aikin Hajji na Saudiyya, Laftanar Janar Muhammad bin Abdullah Al-Bassami, ya ce an ɗauki matakin ne don daƙile masu karya dokoki aikin Hajji.

Ya ce an samu ababen hawa kusan 98,000 da suka karya doka, sannan kuma sun mayar da mazauna ƙasar sama da 171,000 zuwa garuruwansu bayan sun shiga garin Makka ba bisa ƙa'ida ba.

Akwai mutum 4,000 da suka karya ƙa'idojin Hajji - zuwa aikin ba tare da izini ba - da kuma sama da 6,000 da ba su da izinin zama, ko na aiki, ko kuma karya ƙa'idar shige da fice.

A cewar Al-Bassami, a wannan lokacin, hukumomin Saudiyya sun daƙile kamfanoni 140 na Hajji, da kuma ababen hawa 64 da suka saɓa wa dokokin Hajjin, abin da wasu suka kwatanta da matakai masu tsauri a wannan shekarar da ba a saba gani ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ma'aikatar aikin Hajji ta ce bizar ziyara ba za ta bai wa mutum damar gudanar da aikin Hajji ba. Ta nemi baƙin da suka shiga ƙasar da irin wannan bizar kada su shiga Makka a daidai lokacin da ta hana, idan ba haka ba kuma za su fuskanci hukunci.

Duk da cewa miliyoyin Musulmi ne ke son zuwa Hajji duk shekara, mutum kamar miliyan biyu ne kacal ke iya samun damar yin hakan saboda abin da Masallacin Harami zai iya ɗauka kenan, kamar yadda wasu bayanai daga 2022 suka bayyana.

Kamfanin labarai na Saudi Press Agency ya ruwaito Ministan Hajji da Umara na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah na faɗawa wani taron manema labarai cewa mutum miliyan ɗaya da dubu 200 ne suka shiga ƙasar don gudanar da aikin ya zuwa 6 ga watan Yuni.

Sai dai kuma wannan adadi bai ƙunshi na mutanen da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya ba.

BBC ta lura da wasu bidiyo da aka dinga yaɗawa a Jordan da Masar na mutanen da suka je Hajjin ba tare da izini ba, amma jami'an tsaro sun gan su sun kama su, sun kuma mayar da su ƙasashensu.

Hukumomin Jordan sun yi gargaɗi ga mutane da "kada masu amfani da shafukan zumunta su ruɗe su da tallace-tallacen shirya tafiya aikin Hajji da bizar ziyara".

Su ma jami'an tsaron Masar sun saka tarar kuɗi daga fan miliyan ɗaya (dala 21,000) zuwa ƙasa da miliyan uku (dala 36,000) a kan duk wanda ya tafi Hajji ba bisa ƙa'ida ba.

Me ya sa wasu ke tafiya Hajji 'ba tare da izini ba'?

Hoton da BBC ta samu daga wadan suka yi Magana da su, ya nuna yadda wani jami’in civil defense tare da rakiyar yan sandan na bude wata kofa wani gida a Makka ta karfin tsiya.
Bayanan hoto, An yaɗa bidiyon yadda jami'an tsaron suka dirar wa gidajen mutanen da ake zargi da zuwa Hajji ba tare da izini ba

Yayin da hukumomin Saudiyya ke saka dokoki, wasu da yawa kan bi hanyoyin da ba su dace ba daga faɗin duniya zuwa aikin Hajji bisa wasu dalilai, daga cikinsu kuma akwai matsalar tattalin arziki.

"Kuɗin Hajji ya yi tsada sosai." Wannan ne dalilin da Abdel Hamid ya bayar na tafiya Hajji ba tare da izini ba, yana mai cewa kuɗin a Masar zai iya zarta fan 300,000 (dala 6,000), yayin da kuɗin zuwa ba tare da izini ba bai fi ɗaya bisa ukun haka ba.

A cewar cibiyar National Foundation for Hajj Facilitation ta Masar, mafi sauƙin kuɗin tafiya Hajji ta ƙasa a wannan shekarar ya kai fan 191,000 - kwatankwacin dala 4,000 kenan - yayin da tafiya ta jirgi kuma ya kai 226,000.

A Jordan, kuɗin aikin Hajjin ya kai dinar 3,000 (dala 4,200), yayin da kuɗin maniyyacin da aka yi sumoga ba tare da izini ba - da bizar ziyara - bai wuce dinar 1,000 ba (kusan dala 1,400), kamar yadda wani ɗan'uwan Muhammad da matarsa, Iman, ya bayyana.

Amma wasu na cewa kuɗin zuwa Hajjin ba bisa ƙa'ida ba kan kai dinar 2,000 a Jordan ɗin.

Sai dai kuma ba kuɗi ne kawai ke sa mutane yin hakan ba, a cewar ɗan'uwan Muhammad mai shekara 74 da kuma wani mai shekara 59, saboda shekaru ma na jawo wasu su ɗauki matakin.

Game da Saber kuma, ba matsalar kuɗi ba ce ta sa mahaifiyarsa zuwa Hajji ba bisa ƙa'ida ba, saboda ta yi ƙoƙarin zuwa har sau biyar amma ba ta samu dama ba.

Saber ya bayyana kwaɗayin da mahaifiyarsa ke da shi na zuwa Hajji: "Duk shekara mahaifiyata na kallon alhazai a talabijin kuma ta yi kuka saboda rashin samun damar."

Wannan ta sa ya fara neman bizar ziyara don cika mata burinta.

Waɗanda ke zaune a Saudiyyar sun fi fuskantar matsala, kamar yadda Saida - wata 'yar Masar da ke aiki a can.

Da take magana da BBC, Saida ta ce matsalar kuɗi ce ta "tilasta mata kauce wa ƙa'idar" in da ta sama wa ɗanta da 'yarta bizar ziyara don zuwa Hajjin.

Jaridar Okaz ta Saudiyya ta ruwaito Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara a watan Fabrairu tana cewa, kuɗin Hajjin da mazauna ƙasar za su biya ya kai kamar riyal 4,000.

Hoton da BBC ta samu daga wadan suka yi Magana da su, ya nuna yadda wani jami’in civil defense tare da rakiyar yan sandan na bude wata kofa wani gida a Makka ta karfin tsiya.

'Na yi kasada babba'

Saber ya ce yanzu lamarin na nema ya fi ƙarfinsu saboda yadda suke biyan kuɗi a kawo musu abinci har gida saboda tsoron kada su fita waje, da kuma kuɗin otel a Jeddah. Hakan ya sa kuɗin da suke kashewa ya kusa kaiwa na aikin Hajjin a hukumance.

Ya ce: "Yanzu ina tausaya wa kaina. Ban san yaya zan yi da su ba, kuma ina fargabar halin da mahaifiyata za ta shiga idan ba ta samu yin Hajjin nan ba. Abin da na fi damuwa da shi shi ne ranar Arafa, ko da minti 30 ne a bar su su zauna."

Me Shari'ar Musulunci ta ce?

Majalisar Manyan Malaman Saudiyya ta tabbatar cewa matakan da ake bi na neman izini kafin yin aikin Hajji bai saɓa wa Shari'ar Musulunci ba.

"Bai halatta ba mutum ya je aikin Hajji ba tare da samun izini ba, kuma duk wanda ya yi hakan laifi ne," in ji ta.

A Masar, Dr. Muhammad Abdel Samie wanda shi ne babban sakatare na majalisar Fatawa, ya tabbatar da cewa duk wanda ya je Umara kuma ya maƙale har zuwa lokacin aikin Hajji ya aikata zunubi saboda hakan ya saɓa wa Shari'ar Musulunci, amma kuma Umara da Hajjinsa sun yi.

Ya nanata a cikin wani bidiyo da majalisar Fatawa ta Masar ɗin ta wallafa a shafinta na Facebook cewa zuwa Hajji ba tare da izini ba na jawo matsaloli da yawa, ciki har da cunkoso da zai iya haddasa turmutsitsi.

Ya yi bayanin cewa lamarin ya yi kama da na mutumin da ya saci kwalabar ruwa don ya yi alwala, yana mai cewa sallarsa ta yi amma kuma ya samu zunubi na satar da ya yi.