Tinubu ya mayar wa Kwankwaso martani

.

Asalin hoton, Kwankwaso/Twitter

Musayar kalamai ta ɓarke tsakanin fadar shugaban Bola Ahmed Tinubu da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP kuma tsohon gwamanan Kano, Sanata Rabi'u Musa kwankwaso kan zargin da Kwankwason ya yi na cewar gwamantin Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Kano.

Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa "wasu sun haɗa baki da jagororin jam'iyyar APC suna ƙoƙarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci".

Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin marar tushe ballantana makama.

Fadar shugaban na Najeriya ta bakin ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasar, Abdulaziz Abdulaziz, ta ce sun yi mamakin jin irin waɗannan kalamai da suka fito daga bakin wanda ake yi wa kallon dattijon ƙasa wanda ya rike mahimman mukamai da dama a Najeriya.

"Abun mamaki ne a ce mutum kamarsa ya fito ya yi irin waɗannan kalamai, musamman zargin da ya yi na cewar ana son a saka dokar ta ɓaci a Kano ko tayar da rikici a jihar, ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya kan waɗannan zarge-zarge, kuma a matsayinmu na gwamnatin tarayya ba a taɓa yin makamanciyar wannan maganar ba". Inji Abdul Aziz Abdul'aziz

Har Ila yau ya ƙara da cewa batun masarautar Kano al’amari ne da ke gaban kotu, kuma jami’an tsaro suna bin duk wani umarnin kotu don tsare hakkin kowanne ɓangare, inda ya ƙara da cewa shugaba Tinubu na da kusancin da dukkannin mutum biyun da ake taƙaddama a kansu.

"Shugaban ƙasa na da alaƙa me kyau da waɗannan mutane biyu da ake taƙaddama a kansu, ba zai yi wani abu da zai kawo cin zarafi ko ace a matsayinsa na shugaban ƙasa, da yake da alhakin kula da kare dukiya da rayukan ƴan Najeriya a ce gwamnatinsa ta yi wani abu irin wanda Rabi'u Kwankwason ya yi zargi ba, don haka mu a ganinmu ya yi kalaman ne don kawai a harzuƙa magoya baya kuma a yi siyasa" inji Abdulaziz

Me Kwankwaso ya ce?

Wannan ce-ce-ku-ce ya kaure ne sakamakon zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewar wasu na ƙoƙarin kawo rigingimu a jihar Kano babu gaira babu dalili.

Kwankwason ya ce "dukkan wani mutumin kirki a yau da ke jihar Kano, yana tir da abubuwan da ke faruwa a jihar, a siyasance muna murna, amma a matsayinmu na masu kishin ƙasa, kuma shuwagabanni, muna ganin irin wannan abu babu abin da zai iya haifar sai fitintinu.

"Waɗansu ma suna cewa so ake su shigo da fitina shike nan a ɗauki mataki a saka doka akan gwamnatin Kano, amma ina so ku sani suma su sani, dokar da take akasa yanzu ko ka saka dokar state of emergency a jiha, gwamna ya na nan, zai kuma ci gaba da yin aiki, ba wai cire shi za'ai ba, wanna shi ne abinda da dokar ke cewa, kuma doka ce wadda da yawa ba su sani ba, inji Kwankwaso.

'A kai zuciya nesa'

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu inda Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ja hankalin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kano da cewa su lura da maslahar al’umma.

"A ko ina sai da zaman lafiya ake iya yin komai, bai kamata a ce gwamantin tarayya ko ta jiha su ringa yin abun da za su tunzura al'amarin ba, illa su zama masu samar da masalaha da zaman lafiya a tsakanin al'ummarsu" a cewarsa.

Farfesa Kamilu Fagen ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayyar da ta jihar Kano, su lura da cewar ko me ake ciki, su ne shugabanin al'umma, kuma haƙƙi ne da ya rataya a wuyansu da su yi jagoranci wajen kiyaye doka da oda", inji shi.

Wannan rikici kan masarautar Kano dai na ci gaba da ɗaukar hankali a sassan Najerya, inda al’amarin ya rage armashin bikin Babbar Sallah a bana, ko da yake Kanawa na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tamkar babu wani zaman tankiya a jihar.