Abu bakwai da watakila ba ku sani ba kan kungiyar Commonwealth

Asalin hoton, Getty Images
Za a fara wasannin kungiyar kasashen rainon Ingila ranar Alhamis 28 ga watan Yuli a birnin Birmingham.
Sama da ‘yan wasa 5,000 za su fafata, inda suke wakiltar jihohi da suka zo daga duk fadin duniya wanda mambobin ke karskashin inuwar kungiyar commonweath.
Amma wadane kasashe ne suke cikin wannan kungiya?
1- Ita ce mazaunin kusan kaso 1 cikin 3 na duk mutanen duniya

Misali mutane biliyan 2.5 a cikin biliyan 7.9 na duniya suke zama a kasashe 56 na wannan kunigiya.
Sama da kaso 60 cikin 100 na mutanen da ke cikin commonwealth yara da matasa da ke da shekara 29 ko kasa da haka.
A duk fadin duniya, kaso 3 cikin 4 na matasa da ke da shekara tsakanin 15 zuwa 20 suna zaune ne a cikin kasashen Commonwealth.
Kasar da ke da mutane mafi yawa ita ce Indiya, wadda ke da kimanin rabin adadin jama’a a wannan kungiya.
Kasar Pakistan da Najeriya da Bangladesh su ne na gaba a yawan jama’a, sannan Ingila ita ce ta biyar.
2- Wasu mambobin ba su taɓa kasacewa a cikin daular Birtaniya ba
Kasar Rwanda ta kasance mamba a 2009 sannan Mozambique a 1995 kuma Birtaniya ba ta taba rainon su ba.

Asalin hoton, Getty Images
Gabon da Togo su ne na baya-bayannan da suka zama ‘ya’yan kungiya a watan Yunin 2021, amma duka rainon Faransa ne.
Haka zalika wasu kasashe sun fice daga kungiyar.
Kasar Afirka ta janye daga kungiyar a shekara ta 1961 bayan ta soki mambobin Commonwealth saboda manufofinsu na a kan wariyar launin fata. Ta koma shiga kungiyar a shekara ta 1994.
Pakistan ita kuma an kore ta daga kungiyar biyo bayan juyin mulki a shekara ta 1999, amma an bar ta ta kara shiga a shekara ta 2004. An kuma kara dakatar da ita daga 2007 zuwa 2008.
Tshohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya janye kasarshi daga kungiyar a shekara ta 2003 biyo bayan dakatar da kasar sakamakon rahotanni a kan magudin zabe.
Ta nemi da a dawo da ita cikin kungiyar a 2008 amma har yanzu ba a yanke shawara ba.
Kasar ta karshe da ta bar kungiyar itace Maldives a 2016 amma ta koma a 2020.
3- Sarauniyar Ingila ce Shugabar Kasa a kasashe 15 kawai
Mafi yawancin kasashen Commonwealth jamhuriyoyi ne, inda kasar Barbados ta zama ta baya bayannan lamarin da ya sa ta tube Sarauniyar daga shugabar kasa a 2021.

Kasashe biyar wadanda suka kunshi Lesotho, Swaziland, Brunei Darussalam, Malaysia da Tonga suna da nasu sarakan.
Amma har yanzu Sarauniyar Ingila ita ce shugabar kasa a Australia da Canada, sai dai an share shekara da yawa a Australia ana fafutukar mayar da ita Republic.
4- Tana da girma
Commonwealth ya kunshi kaso 1 cikin 4 na gundarin kasa da ke kewaye da tekun duniya.
Kasar da ta fi girma ita ce Canada, wadda ta kasance kasa ta biyu mafi girma a duk duniya. Indiya da Australia na da girma sosai su ma.

Asalin hoton, PA
A daya bangaren akwai kasashe da yawa da ba su da girma, kamar Nauru da Samoa da Tuvalu and Vanuatu, da Antigua and Barbuda da Dominica a Caribbean.
5- Ba Ingila ba ce take da mafi girman tattalin arziki
A cikin kasashen Commonwealth, ba Ingila ba ce tafi mafi girman tattalin arziki bisa alkaluman tattalin azriki na Asusun Lamuni na Duniya, inda Indiya ta wuce ta a karo na farko a wannan shekara.

Idan aka tara tattalin azrikin mambobin kungiyar na kasashe 56 ya haura dala tiriliyan 13.
Wannan ya ninka na Japan sau biyu dala tiriliyan biyar, amma bai kai Amurka ba da ke da dala tiriliyan 23.
Kasuwanci da kasashen Commonwealth ya kai kaso 8.7% na cinikin Birtaniya baki daya a 2020 – kusan daya kenan da adadin kasuwancin Birtaniyan da Jamus.
Fitar da kayayyaki zuwa kasashen Commonwealth daga Birtaniya a wannan shekara ya kai wajen £56bn, sannan ta shigo da kaya daga kungiyar har na fam biliyan 48.
6- Ta sauya sunanta
Kungiyar Commonwealth ta wannan zamani an samar da ita ne a 1949 bayan cire “Birtaniya” daga sunan da kuma dena saka biyayya ga malafar sarauta.

Asalin hoton, Getty Images
Mutane biyu ne suka shugabanci wannan kungiya – Sarki George VI da Queen Elizabeth II.
Wannan matsayi ba gadonshi ake ba, amma ana kyautata zaton yariman Wales zai shugabanci kungiyar idan ya zama sarki.
Ana tafiyar da harkokin kungiyar ne daga babban ofishinta da ke birnin London, tare da jagorancin sakatare janar dinta a halin yanzu Baroness Scotland.
Tana neman wa’adi na biyu duk da suka da take sha daga mambobin kungiyar dangane da kamun ludayinta.
Ragowar kasashen da ke da hannu wajen samar da kungiyar su ne Australiya da Canada da Indiya da New Zealand da Pakistan da Afirka ta Kudu da Sri Lanka.
An soki Commonwealth a matsayin wata kungiya da ke raya akidun mulkin mallaka, inda ba ta da wani tasiri a wannan zamani.
Masu goyon baya sun lamunce akan cewa kungiyar na kawo goyon bayan cigaba da hadin kai akan manufofin kasa da kasa.
7- Akwai sama da ɗaya

Asalin hoton, Reuters
Akwai kuma kungiyar Commonwealth ta kasashe masu zaman kansu, wadda Rasha ta kafa a 1991 da ke ƙunshe da tsofaffin ƙasashen Tarayyar Soviet.
Sannan kar a manta da kungiyar kasashen rainon Faransa – tarayyar kasashe da ke amfani da harshen faransanci da ke da nufin bunkasa harshen Faransanci da ƙara danƙon hadin kai da dangantaka.










