Real Madrid ta shiga gaban Man City a samun kuɗi

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta zarce Manchester City a samun kuɗin shiga, inda ta zama ƙungiya ta farko wajen samun kuɗi kamar yadda kamfanin Deloitte ya bayyana.
Real ta samu kuɗin da suka kai yuro miliyan 831 kimanin fan miliyan 710, wanda hakan ya sa ta zama da ɗaya a samun kuɗi a kakar 2022-2023.
City ta dwo matsayi na biyu duk da cewa ta samu kuɗi da suka kai yuro miliyan 826 kwatankwacin fan miliyan 705.6, wanda nasarar ɗukar FA da Premier da Champions ta kai su,
Kuɗin shigar da ƙungiyoyi 20 suka samu ya ƙaru da kashi 14 ina da yakai yro biliyan 10.5 daidai da fan biliyan 8.97.
Wannan ya haɗa dakuɗin kasuwanci da na wasanni da suka kai yuro biliyan 4.4 da kuma yro biliyan 1.9 lokaci guda.
Kuɗin kasuwanci da aka samu ya wuce na watsa labarai, mafi yawa da aka samu na haska kuɗi karon farko sama da wanda aka samu a 2015-16, banda na kakar 2019-20 da aka samu lokacin Korona, yayin da ƙungiyoyi 17 cikin 20 ke samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga kusan kowacce shekara.
Kuɗin watsa shirye-shirye ya ƙaru da kashi biyar zuwa yuro biliyan 4.2, saboda kakar 2022/23 ba a samu kuɗi daga cikin gida ba.
A mafi yawan lokaci kungiyoyi 20 ɗin ba sa samun abin da ya haura sama da yuro miliyan 500 a shekara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Real Madrid ce a saman teburi karon farko tun 2017-18 duk da cewa ba ta yi nasara ba a hannun Manchester City a wasan kusa da ƙarshe na ƙarshen Champions, kuma ta kammala La Liga a matsayi na biyu a bayan Barcelona, ko da yake ta lashe Copa del Rey da Uefa Super Cup da Fifa Club.
PSG ta samu (€802m), Barcelona ma ta samu (€800m) yayin da Manchester United ta samu (€746m) waɗanda suke cikin ƙungiyoyi biyar na farko.
Liverpool ce t fado ƙasa sosai daga matsayi na uku zuwa na bakwai inda ta samu €683m bayan kammala kakar Premier a matsayi na biyar kuma aka cire su a matsayi na ‘yan 16 a Champions.
Tottenham da Chelsea da kuma Arsenal suna cikin ƙungiyoyi 10, yayin da Newcastle da West Ham ke matsayi na 17 da na 18.
Leicester City da Leeds United da kuma Everton sun faɗo daga ƙungiyoyi 20 farko, wanda hakan yake nufin an samu raguwar ƙungiyoyin Premeir cikin jerin daga 10 zuwa 8, kamar yadda suke shekara biyu baya.
Matsayi Ƙungiya 2022-23 Kuɗi 2021-22 Kuɗi
1 Real Madrid £723m £604.4m
2 Man City £718.2m £619.1m
3 PSG £697.2m £554.1m
4 Barcelona £695.8m £540.4m
5 Man United £648.5m £583.2m
6 Bayern Munich £647m £553.5m
7 Liverpool £593.8m £594.3m
8 Tottenham £549.2m £442.8m
9 Chelsea £512.5m £481.3m
10 Arsenal £463.1m £367.1m
11 Juventus £376m £339.4m
12 Dortmund £365.3m £302.4m
13 AC Milan £335.1m £218m
14 Inter Milan £329.5m £261.2m
15 ATM £316.6m £333.6m
16 Frankfurt £255.3m £176.3m
17 Newcastle £250.3m £179.7m
18 West Ham £239.2m £255.1m
19 Napoli £232.8m £132.5m
20 Marseille £224.7m £201.2m










