Da gaske Faransa na tatsar ƙasashen Afirka?

Wani bidiyon ƴar siyasar Italiya Giorgia Meloni, wadda ta zama firaministar Italiya ya yi ta yawo a shafukan intanet, tana zargin Faransa da yin amfani da kuɗaɗen da take buga wa ƙasashen Afirka wurin ci gaba da yi masu 'mulkin mallaka da kuma 'tatsar' su.

A baya-bayan nan an rinƙa samun takun-saƙa tsakanin ƙasashen biyu (Faransa da Italiya) game da ƴan ci-ranin Afirka da ke zuwa turai.

Italiya ta hana jirgin ruwan ƴan gudun hijira tsayawa a bakin gaɓarta. Faransa ta zargi Italiya da aikata abin da bai kamata ba.

Bidiyon ya nuna Ms Meloni na iƙirarin cewa "kashi 50% na dukkanin kuɗin da Burkin Faso ke samu daga kayan da take fitarwa suna ƙarewa ne a lalitar Faransa." A ranar 19 ga watan Nuwamba, wata mai sharhi ta ƙasar Nethrelands Eva Vlaardingerbroek ta wallafa bidiyon a shafinta na tuwita, tana cewa "na san yanzu Emmanuel Macron na da-na-sanin taƙaddama da Giorgia Meloni".

Dubban mutane ne suka yaɗa bidiyon daga shafinta.

To amma bidiyon da aka yaɗa an samo shi ne daga shekarar 2019, lokaci mai tsawo kafin Meloni ta zama firaminista - kuma bayanan nata a wancan lokaci ba daidai ba ne.

Mene ne abubuwan da Giorgia Meloni ta yi ikirari?

An tsakuro bidiyon ne daga wata hira da Ms Meloni ta yi da wani gidan talabijin na Italiya mai suna La 7, ranar 19 ga watan Janairun 2019, a lokacin da take a matsayin ƴar majalisa ƙarƙashin jam'iyyar Brothers of Italy.

A cikin tattaunawar Meloni ta riƙe takardar kuɗi ta CFA, tana bayyana ta a matsayin "kuɗin mulkin mallakar" da Faransa ke buga wa ƙasashen Afirka 14, wadda a cewarta Faransa ke amfani da kuɗin tana 'tatsar arziƙin ƙasashen."

Daga nan kuma sai ta fito da hoton wani yaro yana aiki a wata mahaar zinare da ke a Burkin Faso, kuma ta yi iƙirarin cewa "kashi 50% na kuɗaɗen da Burkin Faso ke samu daga abubuwan da take fitarwa suna ƙarewa ne a lalitar Faransa". Ta ce "zinaren da wannan yaron ke shiga can ƙarƙashin ƙasa yana hakowa, akasarinsa na ƙarewa ne a asusun Faransa."

A ƙarshen bidiyon tana cewa "kwaso ƴan Afirka a kawo su Turai ba ita ce mafita ba, mafitar ita ce a ƴantar da Afirka daga wasu turawa da ke tatsar su."

Mun yi bincike kan irin wannan zargi a 2019, lokacin da wani ɗan siyasa na Italiya ya zargi Faransa da talauta Afirka da ingiza matsalar ƴan ci-rani zuwa Turai.

Mece ce hujjar?

Faransa ce take buga wa ƙasashen Afirka 14 takardar kuɗi ta CFA, ciki har da Burkina Faso. Ba dole ba ne shiga cikin ƙasashen da Faransar ke buga wa kuɗi. A shekarar 1940 ne aka kirƙiri takardar kuɗin ta CFA, domin amfanin da ita a ƙasashen Afirka waɗanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

A 2019 lokacin da Ms Meloni ta yi iƙirarin, Faransa na buƙatar ƙasashen Afirka masu amfanin da takardar kuɗin CFA da su zuba kashi 50% na kuɗaɗen ajiyarsu na ƙasar waje a Faransar (ba kuɗaɗen kayan da suke fitarwa ba) a bankin ƙasar Faransa, domin su samu saukin sauya kuɗi zuwa takardar kuɗin Yuro.

Ƙasashen na da damar cirar kuɗin nasu a duk lokacin da suke so, haka nan kuma Faransar tana biyan su riba.

Amma Faransa ba ta buƙaci Burkina Faso ta ba ta "kashi 50% na dukkanin abubuwan da take fitarwa waje ba."

Alƙaluman Bankin Duniya sun nuna cewa Faransa ba ta ma cikin ƙasashe biyar da Burkina Faso ta fi sayar wa kayan da take fitarwa, cikin su har da zinare, wanda shi ne ta fi fitarwa.

A 2020, Burkina Faso ta sayar da kashi 90% na zinaren da take fitarwa ne ga Switzerland.

Mun tuntuɓi ofishin Ms Meloni a kan ko har yanzu tana kan matsayarta a kan kalamanta na baya, sai dai har yanzu ba su ce komai ba.

Haka nan ma Faransa ba ta ce komai ba a lokacin da BBC ta tuntuɓe ta kan bayanan na Meloni.

Me ya sauya daga wancan lokacin?

A watan Disamba, 2019 an yi sauyi ga dokokin ƙasashe masu amfani da takardar kuɗi ta CFA, inda aka cire ɓangaren da ya ce dole ƙasashen su ajiye kashi 50% na kuɗaɗen asusun ajiyarsu na ƙetare a Faransa.

Faransa ta fara shirin mayar wa ƙasashen kuɗadensu na ajiya a 2021, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

A watan Maris na wanna shekara, asusun lamuni na duniya IMF ya ce an rufe asusun ajiya da ake sanya kuɗaɗen na ƙasashen da ke amfani da CFA a Faransa.

Inda a yanzu babban bankin ƙasashen yammacin Afirka (wanda shi ne ke kula da tsare-tsaren kuɗi na ƙasashe takwas na yankin, ciki har da Burkina Faso) ya zamo shi ne yake kula da kuɗaɗen.

Me ya sa ake ka-ce na-ce game da kuɗin da Faransa ke buga wa ƙasashen Afirka?

Masu suka sun bayyana tsarin Faransa na buga wa ƙasashen Afirka kuɗin CFA a matsayin wani nau'i na mulkin mallaka, kuma sun ce hakan ya yi tarnaki ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasashen 14.

Kuma sun ce ƙasashen ba su ta ta-cewa kan ƙa'idojin kuɗi na ƙasashen yankin Turai.

Wani bayani da cibiyar Brookings da ke Amurka ta wallafa a bara ya ce duk da cewa ƙasashen da ke amfani da kuɗin CFA ba su samu hauhawan farashin kayan masarufi ba sosai, amma tsarin ya taƙaita yadda za su iya sauya manufofinsu, musamman a lokacin da ake fama da annobar korona.

Faransa ta rinƙa kare tsarin, tana cewa yana samar da tabbas a tsarin tattalin arziƙin ƙasashen, kuma kasancewar takardar kuɗin tana dogaro ne da kuɗin Yuro na tarayyar Turai, hakan na samar wa CFA ɗin kariya daga tangal-tangal na tattalin arziƙi da rage tashin farashi.

Kuma ta ƙara da cewa ƙasashen na da damar fita daga tsarin.