Amurka za ta yafe wa miliyoyin ɗalibai bashin karatu

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Shugaba Biden ta ce za ta yafe bashin dala biliyan 39 a kan dalubai fiye da dubu 800 a sassan Amurka.
Ma’aikatar Ilimi ta ce, wannan daban ne daga gagarumin shirin da shugaban ya yi, na yafe bashin karatun amma dai tana fatan zai samar da sa’ida ga masu karamin karfi.
Kuma ta ce ta yi hakan ne da zummar cewa matakin zai gyara kura-kuran da ake samu wajen tantance yawan kudin da daluban ke biyan bashi kowanne wata.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne ‘yan makwanni bayan da kotun koli ta yi watsi da bukatar shugaban ta yafe bashin sama da dala biliyan 400 ga miliyoyin Amurkawa da suka amfana da bashin karatun.
Tun a lokacin da Kotun Kolin Amurkar ta yi watsi da shirin na Shugaba Biden na yafe wa daliban bashin karatun, wanda shiri ne da shugaban ya yi yakin neman zabe da shi, a 2020, Mista Biden ya ce gwamnatinsa za ta koma ta sake nazari da tsari kan yadda za ta bullo wa lamarin ta wata siga.
A don haka wannan sanarwa da ta yi, ta ce ta yi ta ne bayan da ta yi wasu sauye-sauye a ainahin babban shirin yafe bashin karatun.
Da wannan sanarwa a yanzu nan da ‘yan makwanni Ma’aikatar Ilimi ta Amurkar ta ce, za a sanar da masu bashin a kansu wadanda za su ci wannan gajiya.
A sanarwar da ya fitar mai dauke da bayanin shirin, Ministan Ilimi, Miguel Cardona ya ce tsawon lokaci masu cin bashin sun kasance tsamo-tsamo a cikin tsarin da ya gurgunce, wanda ya gaza adana cikakkun bayanai na kan cigabansu na cin moriyar yafiyar.
Jami’an ma’aikatar sun ce masu cin bashin za su cancanci yafiyar ne bayan shekara 20 ko 25 suna biya, wanda hakan ya dogara ga tsarin biyan nasu.
Gwamnatin Amurkar dai na bayar da hanyoyi ko tsare-tsare da dama na samun kudin da dalibi zai rika biyan bashin, duk wata, daidai da abin da yake samu, har tsawon shekara 20 ko 25.
Da farko gwamnatin ta Biden ta sanar da shirin yin sauye-sauye a tsarin da ake bi wajen biyan bashin ne a watan Afirilu na bara, 2022, domin gyara kura-kuren da ta ce an dade ana tafkawa a tsarin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai kuma a kwatsam a watan da ya gabata Kotun Kolin Amurkar a hukuncin da alkalai 6 suka rinjayi 3, hukuncin da bai yi wa jama’a da yawa dadi ba, ta soke babban shirin na Shugaba Biden na yafe biliyoyin dola na bashin daliban, ga Amurkawa sama da miliyan 40.
Kotun ta ce, gwamnatin Biden ta wuce gona da iri, da shirin nata, wanda da zai yafe dala dubu goma a wani bin ba dubu ashirin da ake bin daidaikun Amurkawa da suka karbi kudin a matsayin tallafin karatun gaba da sakandire.
Jim kadan da yin wannan hukunci ne Mista Biden ya yi alkawarin lalubo wata hanyar ta daban domin yafe bashin karatun.
A lokacin ya ce, hukuncin ranar ya rufe wata kafa. Amma za su biyo ta wata hanyar daban.
Shugaban ya dauki matakai daban-daban da dama domin yafe wannan bashi na karatu, ta hanyar amfani da ikonsa tun da ya hau mulki.
Misali a bara ya soke bashin daliban har na mutum dubu 200, wadanda suka ce ko dai jami’o’insu sun cutar da su ko kuma sun zambace su.
Yanzu wannan tsarin da gwamnatin Biden ta biyo ta hanyarsa domin cimma waccan manufa da ya yi yakin neman zabe da ita, ko kadan ba ta kai ainahin yadda ya tsara shirin nasa ba na tun farko na yafe dala biyan 430 ga Amurka da suka kai miliyan 40 ba.
To amma dai da babu gara ba dadi, domin, Ma’aikatar Ilimi ta ce har yanzu tana duba wasu hanyoyin da za ta kai ga cimma ainahin shirin, amma ta ce za a iya daukar watanni kafin a kai ga samun ci-gaba.











