Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalaman ƙarshe na yaron da aka caka wa wuƙa saboda zargin ƙin jinin Musulmai
- Marubuci, Daga Mike Wendling
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a Bridgeview cikin jihar Illinois
"Umma, lafiyata ƙalau", su ne kalmomin ƙarshe na yaro Musulmi ɗan shekara shida da aka caccaka wa wuƙa, har sai da ya riga mu gidan gaskiya, a wani laifin da ake zargin na ƙin jinin Musulunci ne a ƙarshen mako.
Kawun yaron ne ya bayyana haka, lokacin da ɗaruruwan mutane suka taru a wurin jana'izarsa.
Ranar Litinin ne masallacin da ke ake kira Mosque Foundation a Bridgeview na wajen birnin Chicago ya tumbatsa da mutane, inda har ma wasu suka gudanar da sallah a wajen haraba.
'Yan sanda sun ce an far wa Wadea al-Fayoume ne saboda shi Musulmi ne.
An gudanar da jana'izarsa, yayin da mai gidan hayarsu ya bayyana a gaban kotu, inda aka tuhume shi da aikata kisan gilla ga ƙaramin yaro. Mutumin da ake zargi ɗan shekara 71, an yi zargin cewa ya fusata ne saboda yaƙin Isra'ila da Hamas.
Masu makoki sun fito daga sassa da dama a faɗin yankin, wasu ma daga can nesa, don bayyana alhini da takaicinsu a kan wannan kisa.
Mahaifiyar Wadea, Hanaan Shahin, mai shekara 32 ta yi matuƙar jin raunuka a harin, kuma ba ta samu halartar jana'izar ɗanta ba, daidai lokacin da take ci gaba da samun sauƙi a asibiti.
"Na kaɗu sosai, amma ban yi mamaki ba," cewar Sadia Nawab, wata mahaifiyar 'ya'ya uku da ke zaune a kusa da masallacin.
"Muna cike da fargaba game da 'ya'yanmu, da kuma ƙarin damuwa a kan yaran da ba su da wani ƙarfi daga ko'ina suke cikin faɗin duniya, amma a yanzu suke Falasɗinu, da kuma Gaza."
Kuma cikin wani take da masu makoki da yawa ke nanatawa, ta zargi shugabannin gwamnati da kafofin yada labarai da nuna son kai a kan Falasdinawa da ƙarfafa gwiwar wani yanayi mai cike ƙiyayya.
Yousef Hannon, wani kawun mamacin kuma mai magana da yawun dangin Wadea, ya ce kafin kashe yaron "babu wasu alamomi da ke nuna cewa abubuwa ba sa tafiya daidai" tsakanin mutumin da ake zargi da aika-aikar, Joseph Czuba, da kuma wadanda aka cutar.
Yaron da mahaifiyarsa na rayuwa ne a gidan haya mai daki biyu mallakar Joseph Czuba, wanda har ma ya halarci bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Wadea a 'yan makonnin da suka wuce, kamar yadda Yousef Hannon.
"Yana da faran-faran ga daukacin iyalin, musammam dai ga yaron, wanda yake daukarsa kamar wani kaka," kamar yadda Hannon ya fada wa BBC. "Ya kawo masa kyautuka, ya kawo masa wasu kayan wasan yara."
Ya ce Wadea "yana kaunar makarantarsu, yana son malamansa, kuma yana matukar kaunar mahaifiyarsa".
"Yana son rayuwa," in ji shi. "Idan ka gan shi yana rayuwa irin ta lafiyayyen yaro dan shekara shida, a ko da yaushe yana cikin murmushi."
Shi ma wani kawun marigayin, Mahmoud Yousef ya ce: "A lokacin da aka caccaka wa [Wadea] wuka kalmominsa na karshe ga mahaifiyarsa su ne, 'Umma, lafiyata kalau.' Kun san me, yana cikin koshin lafiya. Yana cikin ni'ima."
Wani mai gabatar da kara ya fada a takardun kotu cewa mai gidan hayar ya yi fushi da mahaifiyar Wadea ne "saboda abin da ke ci gaba da faruwa a birnin Kudus".
"Ta amsa masa da cewa, 'Bari mu yi fatan samun zaman lafiya,'" kamar yadda Mataimakin Babban Lauyan Gwamnati Michael Fitzgerald, ya rubuta. "Daga nan sai Joseph Czuba ya far mata da wuka."
Masu shigar da ƙara sun ce Joseph Czuba ya riƙa sauraron shirye-shiryen rediyo na masu ra'ayin 'yan mazan jiya sannan ya ƙara zama mai zabura game da kasancewar dangin Amukawa 'yan asalin Falsɗinu a gidansa. An haifi Wadea a Amurka bayan mahaifiyarsa ta je ƙasar shekara 12 da ta wuce.
A cewar takardun kotu, matar Joseph Czuba ta faɗa wa 'yan sanda cewa mijinta ya shiga jin tsoron wasu mutane 'yan asalin Gabas ta Tsakiya za su far masa, kuma ya shiga damuwa cewa wani bala'i zai auka wa babban layin wutar lantarki ta Amurka, abin da ya shi cire dala 1,000 daga banki.
Da safiyar Asabar ne, aka kira 'yan sanda gidansa da ke Plainfield, cikin jihar Illinois, mai kimanin nisan kilomita 64 kudu maso yammacin Chicago.
A cewar wasu rubutattun saƙonnin waya da dangin mai mutuwar suka bai wa Majalisar Kyautata Alaƙa tsakanin Amurka da Musulmai reshen yankin, Joseph Czuba ya yi yunƙurin shaƙe Hanaan Shahin yana cewa: "Ku Musulmai duk sai kun mutu".
Mista Czuba ya bayyana a kotu ranar Litinin, inda aka tuhume shi da kisan gilla da yunƙurin kisan gilla da matsanancin duka da mugun makami, sai kuma tuhuma a kan nuna ƙiyayya
Sanye da jan tufafin fursunoni da cukurkuɗaɗɗen farin gashin kansa, an ci gaba da tsare shi babu beli kuma an ba da umurnin cewa kada wata alaƙa ta haɗa shi mahaifiyar yaron.
Ya yi taƙaitaccen jawabi ne kawai don tabbatar da cewa zai buƙaci lauyan da zai tsaya masa bisa umarnin kotu sannan ya fahimci duk tuhume-tuhume, kafin a masa sasari, a mayar da shi gidan yari.
A wani lamari na daban kuma, ma'aikatar Shari'a a Amurka ta ce tana gudanar da bincike kan aikata laifin nuna ƙiyayya.