Da gaske Hamas ta yi barazanar tayar da hankali a gasar Olympics ko yaudarar Rasha ce?

Asalin hoton, Telegram channel 'Golos Mordora'
- Marubuci, Maria Korenyuk and Maria Rashed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Team and BBC Arabic
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani faifan bidiyo da ke ɗauke da wani ɗan gwagwarmayar Hamas da ke barazanar tayar da hankali a gasar Olympics da za a yi a birnin Paris ya yi ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta.
Sai dai shaidun da BBC ta tattara sun nuna cewa mai yiwuwa ƴan Rasha ne suka yi wannan bidiyon da nufin kawo cikas ga gasar.
Bidiyon wanda miliyoyin mutane suka kalla a shafukan sada zumunta, ya fito ne kwanaki kaɗan gabanin bikin bude taron da aka fara a ranar Juma'a, 26 ga watan Yuli, a birnin Paris.
A cikin faifan bidiyon, wanda ake zaton dan gwagwarmayar Hamas ne, da fuskarsa a rufe, ya yi magana a cikin harshen Larabci game da ramuwar gayya ga goyon bayan da Faransa ke yi wa Isra'ila, yana mai gargadin cewa "jini zai kwarara a kan titunan Paris."
Babban rashin daidaito a harshe
Bidiyon dai bai nuna wata dangantaka da Hamas ba duk da cewa waɗanda suka yaɗa bidiyon a shafin sada zumunta na X sun alaƙanta bidiyon da Hamas, amma kuma jagororin Hamas sun ce bidiyon ƙarya ne, ƙirƙiro shi aka yi.
Da muka yi nazari a kan bidiyon, mun gano bambamce-bambace da dama a harshe ko yaren da aka yi amfani da shi da bidiyoyin da Hamas take saki a hukumance.
Hamas dai ta kasance tana da dandali a shafin sada zumunta na Telegram inda take wallafa sanarwa da bidiyoyi kan yaƙin Gaza.
Harshen da mutumin da yayi magana a cikin bidiyon bai yi kama da na Falasɗinawa ba.
Kalamansa sun nuna cewa bai ƙware a yaran Larabci ba saɓanin masu magana da yawun Hamas.
Ko kayan da mutumin da ke iƙirarin shi ɗan Hamas ne a cikin bidiyon ya saka ba su yi kama da irin kayan da mayaƙan Hamas ke sakawa ba
Kuma yadda aka maƙala tutar Hamas a kayan wanda yake cikin bidiyon ba ta yi kama da yadda mai magana da yawun Hamas ke maƙala tutar a kan kayansa ba.
Mai magana da yawun Hamas ɗin dai na maƙala tutar Falasɗinawa a ɓangaren hannun rigarsa amma kuma mutumin da ke cikin bidiyon ya maƙala tutar ne a tsakiyar kayan ne.
Akwai wani tsohon bidiyo da aka yi ƙaryar alaƙanta shi da Hamas
Sabon bidiyon da ke harin gasar Olympics da za ake yi a birnin Paris na Faransa na nuna alaƙa da wani tsohon bidiyo da aka taɓa yaɗawa wanda aka yi ƙaryar alaƙar tata da Hamas.
Wannan tsohon bidiyon da aka yaɗa tun a watan Oktoba ya nuna wasu da aka yi iƙirarin cewa ƴan Hamas ne suna yin godiya ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky kan samar musu da makamai - zargi ne mara tushe ga Ukraine.
Wanann labarin na daga cikin gangamin yaƙi da labarun ƙarya da Kremlin ke yaɗawa a cewar masu bincike daga Jami'ar Clemson da ke kudancin jahar Carolina waɗanda suka ƙaryata

Asalin hoton, Telegram channel "Russia MyVmeste!"
BBC ta lura cewa muryoyi da tufafi da kuma wuraren da Hamas ke ɗaukar bidiyoyinta na kama da junansu, babu wani bambanci.
Dukkan bidiyoyin biyu sun nuna bango mai launin toka iri ɗaya kuma ba su da inganci me kyau. Wannan ya bambanta da faifan bidiyon ƙungiyar Hamas daga watanni tara da suka gabata, waɗanda ke da ƙima da inganci mai ƙarfi.
Wane ne ke da alhakin ƙirƙirar bidiyon?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu masu sharhi daga sabon bidiyon sun yi iƙirarin cewa Isra'ila ce ke da alhakin ƙirƙirar bidiyon amma kuma babu wata shaida da ke nuna hakan.
Amma kuma ƙwararru sun nuna cewa hanyoyin da aka bi wajen yaɗa bidiyon na nuni da Kremlin.
Bidiyon dai mai nuna ƙin jinin Faransa an fara sakin sa a ranar 21 ga watan Yuli a shafin @endzionism24 da ke X, wanda yake ɗauke da sunan "mayaƙin Hamas". Shafin ya saba sakin hotunan da ake samarwa ta hanyar ƙirƙirarriyar basira amma yanzu an daina yin hakan.
Daga baya wasu jaridun Afirka ta Yamma masu ƙawance da Larabawa sun wallafa bidiyon a shafin Telegram kamar yadda farfesa Darren Linvill daga jami'ar Clemson University.
Daga cikin shafukan Telegram da suka fara rarraba bidiyon na turanci ne na "Aussie Cossack" na wani ɗan Rasha mai farfaganda da ke zaune a Sydney, Simeon Boikov wanda yake da mabiya 80,000 da kuma kuma tashar da ke goyon bayan Rasha ta "Golos Mordora" wadda ke da mabiya 170,000.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an Faransa sun kashe watanni suna yaɗa labaran ƙanzan kurege domin yi wa gasar Olympics zagon ƙasa.
A watan Afrilu, shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce Rasha na kokarin tallata batun da ke cewa Faransa ba za ta iya karɓar ɓakuncin gasar Olympics ko kuma jama'a z su kasance cikin hatsari. Rasha dai ta yi watsi da iƙrarin.
Saboda a yaƙin da Rasha ke yi da Ukraine, aka haramata wa rashar da Belarus aike wa da tawagoginsu zuwa gasar ta Olympics a Paris.
‘Jefa tsoro a zukatan jama'a’
Cibiyar binciken abubuwa masu tsoratarwa ta kamfanin Microsoft ta nazarci bidiyon kamar yadda gidan talbijin na NBC News ya nema, inda kuma binciken ya alaƙanta bidiyon da wata kungiyar Rasha da ake kira “Storm-1516”.
Masu binciken na Microsoft sun ce kungiyar na da alaƙa da wasu ɗaiɗaikuwar mutanen da ke da alaka da ɓangaren watsa labarai na Yevgeny Prigozhin, marigayi tsohon shugaban dakarun Wagner na ƙasar Rasha.
Cibiyar ta Microsoft ta ce burin kungiyar shi ne "ganin sun raunana tallafin turain wajen samar da makamai ga Ukraine.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Ƴan Rasha ke amfani da ƙarairayi dangane da gasar Olympic a Paris.
A 2023, wani shafin Telegram mai goyon bayan Rasha ya watsa wasu fina-finai da ke kakkausar suka ga wasanni.










