Ɓacin rai na ƙaruwa yayin da Al-Sisi ke neman wa'adi na uku a Masar

    • Marubuci, Daga Sally Nabil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic, Alƙahira

Mutumin da mutane ke yi wa kallon mai ceto, shugaban Masar mai ƙarfin iko Abdul Fattah al-Sisi, yanzu ana masa wani irin kallo na daban.

Misirawan da suka hau tituna suna murna game da janar ɗin da ya zama shugaban ƙasa shekara 10 da ta wuce, yanzu ba sa farin ciki kamar yadda suka yi tsammani.

Yayin da Sisi ke neman wa'adin mulki na uku jere, a zaɓen da aka fara kaɗa ƙuri'a a ƙarshen makon jiya, matsalar koma-bayan tattalin arziƙi tana daga gaba-gaba cikin jerin abubuwan da mutane ke kuka da su a ƙasar.

Nadia na ɗaya daga cikin waɗanda ke fafutukar samun abin da za su ci, yayin da gwamnatin Al-Sisi ke ci gaba da aiwatar da abin da ta kira sauye-sauyen tattalin arziƙi.

Da ƙyar, matar mai shekara 57 da mijinta ya mutu ya bari da 'ya'ya shida, take iya samun abin kai wa baka, inda take sayar da jarida a gefen titi.

A wani ƙaramin gidanta cikin wata unguwa da ke yankuna masu yawan mutane a birnin Al-Ƙahira, Nadia ta shaida wa BBC cewa rabon ta da ta sayi nama shekara uku kenan. A wajenta, rayuwar yau da kullum tana ƙara tsanani.

"Ina fargabar in kwanta barci wasu lokutan, saboda na san cewa farashin kayayyaki a washe gari zai iya ƙara tashi," ta faɗa min haka cikin murmushi amma fuskarta cike da damuwa.

Alƙaluman hauhawar farashi na bayan-bayan nan sun nuna an samu hauhawar farashi a Masar a watan Oktoba da kashi 38.5%, wani ɗan ragi da aka samu daga kashi 40.3% idan aka kwatanta da watan da ya wuce.

Ba ma a fiye damuwa da waɗannan alƙaluman ba, a kasar ta Larabawa mafi yawan jama'a, kuma talakawan ƙasar na fuskantar tashin farashin kayayyakin sama da yadda hukumomi ke bayyanawa.

'Muna mantuwa ne'

Yayin da farashi ke kara tashi, kuɗin da Nadia ke samu ya ragu.

Sama da shekara 10 da suka gabata, tana sayar da jarida 200 a rana, amma yanzu bai fi ta sayar da 20 ba.

Nadia ta ce idan za ta yi girki a yau tana kashe fan ɗin Masar 300 zuwa 500 kwatankwacin dala 9.70, amma shekarun da suka gabata sai ka kasa kudin kaso shida tukunna.

"Ya'yan itace ma sun yi tsada sosai," kamar yadda ta shaida.

Cikin watanni tara da suka gabata, darajar fan ɗin Masar ta faɗi da kimanin kashi 50% a kan dalar Amurka.

Tattalin arzikin Masar duka ya dogara ne kan yadda ake shigo mata da kayayyaki daga ketare, farashin kayan amfanin yau da kullum ya yi tashin gauron zabi, yayin da ita kuma kasuwar bayan fage ta musayar kuɗaɗen ƙetare ke samun tagomashi.

Alƙawarin abubuwa mafiya muhimmanci

Tun lokacin da Sisi ya zama shugaban ƙasa a 2014 - shekara guda bayan ya jagoranci sojoji sun hambarar da wanda ya gada, Mohammed Morsi - an kashe kudade masu yawa kan manyan ayyukan raya ƙasa.

An gina gadojin sama an kuma faɗaɗa tituna, an kuma gina sabon babban birni da ya ci biliyoyin dala kusa da al-Ƙahira wanda zai yi wuyar zama.

Masoya shugaban sun yi amannar fadada birane zai sukaka wa mutane rayuwa kuma zai janyo masu zuba hannun jari daga ƙasashen ƙetare, wanda hakan zai sa ƙasar ta bunƙasa.

Walid Gaballah wani masanin tattalin arziki kuma mamba a wata ƙungiyar masu samar da ƙididdiga, ya yi amannar aikin ya samar da ayyuakan yi kuma ya rage matsalar rashin aikin yi da ake fama da ita a Masar.

Kuma ya ce matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a ƙasar, abu ne da ya shafi duniya baki ɗaya.

"Duka ɗan abin da gwamnati ta ajiye na sauye-sauyen da take shirin kawo wa annobar korona ta cin ye shi. Ga yaƙin Ukraine da ya tilasta wa masu zuba jari na ƙasashen waje da yawa cire kudɗensu daga bankunan Masar," in ji shi.

Gwamnati ta sha nanata cewa ana ta zuba kudi wajen ayyukan samar da walwala ga talakawa da marasa ƙarfi a Masar.

Amma mutane na ci gaba da koke kan halin da suke ciki na rayuwa na ƙara munana.

Alƙaluman hukuma sun nuna cewa kimanin kashi 30 cikin dari na adadin mutum miliyan 100 a Masar na rayuwa ne cikin ƙangin talauci. Tun 2016, gwamnati ta ari sama da dalar Amurka biliyan 20 daga Asusun Lamuni na Duniya domin taimaka wa kasafin kuɗin kasar.

An cire tallafin da gwamnati take bayarwa na wasu manyan abubuwa kamar man fetur, abin da ya sa farashin ƙara tashi.

Zaɓen mutum ɗaya

Duk da cewa akwai damuwa sosai, Misirawa ba su da wani zaɓi a wannan zaben, ganin cewa takara ce ta mutum guda.

Kungiyoyin adawa suna koken cewa ba sa iya gudanar da lamuransu yadda ya kamata saboda rashin tabbas.

Ko da yake akwai wasu ƙananan 'yan siyasa uku da suke takarar tare da shugaban, mutane da dama sun yi amannar cewa sakamakon zaɓen zai fito yadda aka saba, Mista Sisi zai ci zaɓe cikin sauki, inda zai kara yin wasu shekaru shidan a ofis.

Wani da aka yi tsammanin zai iya tabukawa a zaɓen shi ne tsohon ɗan majalisa Ahmed Tantawy, sai dai daga baya ya fita daga zaɓen saboda gaza samun abin da ake bukata.

A watan Oktoba ya zargi hukumomi da kama kimanin mutum 100 cikin magoya bayansa, domin kashe masa kwarin gwiwa a takarar da yake yi.

Yanzu ana tsare da Tantawy, bisa tuhumar fitar da takardun zaɓe da raba su ba bisa ƙa'ida ba.

Fargabar komawa gida

kamar ‘yan siyasa na bangaren adawa, masu rajin kare hakkin bil’adama su ma suna kokawa kan ka’idoji masu tsauri da ake gindayawa na tsaro. Sun ce yana da matukar wahala a iya gano abubuwa na cin zarafi.

“Kare hakkin bil’adama lamari ne mai matukar hatsari a Masar,” in ji Mina Thabet, wanda mai hankoron kare hakkin dan’adam ne, wanda ya tsere daga Masar kuma yake zama a Birtaniya tun kimanin shekara shida da suka gabata.

Har yanzu yana tuna wahalar da ya sha lokacin da aka tsare shi na wata daya a Masar a shekarar 2016, bayan an zarge shi da wasu laifuka, ciki har da kasancewa dan wata kungiya da aka haramta, da yada labaran karta, wadanda sau da yawa zarge-zarge ne da akan dora wa masu adawa da gwamnati.

Ya ce “An daure min ido, aka sa mini ankwa. Wani jami’in tsaro ya doke ni tare da yi min barazanar cewa zai yi min tsirara ya zane ni.”

Shekara daya bayan sakin shi, Mr Thabet ya tafi Birtaniya domin yin karatu. Daga nan ya yanke shawarar ba zai koma gida ba kasancewar yana jin tsoron za a sake mayar da shi gidan yari a kowane lokaci.

Ya ce “Ranar da na yi bacci har da minshari ita ce rana ta farko da na gudu daga Masar.”

Yana kallon zaɓe a matsayin wani abu da ba komai ba ne, face tsawaita manufofin zafin hannu na gwamnatin Sisi, wadda ya ce ba ta da jimirin adawa.

"Da yawan takwarorina masu kare 'yancin ɗan'adam a Masar ko dai an rufe dukiyarsu, ko kuma an sanya sunayensu cikin jerin waɗanda aka haramta wa tafiye-tafiye. Ba za ka iya yin aikinka ba, ba tare da fargabar za a gurfanar da kai a gaban kotu ko kuma a musguna maka ba."

Mista Thabet ya faɗa min cewa zai koma Masar ne kawai idan ya ji rayuwarsa tana cikin aminci da ya yi aiki a can kuma ya furta albarkacin bakinsa ba tare da yiwuwar samun martani daga gwamnati ba.

Tuni dai hukumomi suka yi watsi da irin wannan sukar lamiri da cewa siyasa ce kawai.

Sun kafa kwamitin da ya yi wa gomman fursunonin siyasa afuwar shugaban ƙasa, kuma sun yi alƙawarin ƙara jan ɗamara wajen inganta kare harkokin 'yancin ɗan'adam na ƙasar.

Sai dai ƙungiyoyin kare 'yancin ɗan'adam na gida da na ƙasashen duniya sun yi bayani game da dubun dubatar fursunonin siyasa da ake tsare da su a gidajen yari - adadin da gwamnati ta musanta.

Allunan talla ɗauke da hotunan Shugaba Sisi an kakkafe a kan dukkan tituna a birnin Alƙahira.

Yana ƙoƙari ta hanyar yaƙin neman zaɓensa, ya shawo kan masu zaɓe cewa gobe, sai ta fi yau kyau. Sai dai mutane da yawa a nan suna cike da mamaki a kan ko sake zaɓensa tabbas zai iya canza wani abu.