Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Ghana: Abubuwan da ke ran masu kaɗa ƙuri'a
- Marubuci, Brian Osweta, George Wafula & Damian Zane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Za a fafata babban zaɓe na ƙasar Ghana karo na tara tun bayan da ƙasar ta koma tsarin siyasar jam'iyyu da yawa a shekarar 1992.
Tun daga lokacin zuwa yanzu, an samu sauyin shugabanni sau uku cikin lumana, inda jam'iyyu biyu manyan na ƙasar – National Democratic Congress (NDC) da New Patriotic Party (NPP) – suka shugabanci ƙasar na shekara 16.
Ga wasu bayanai a taƙaice, inda a ciki aka bayyana abubuwan da suke zuciyar mutane a daidai lokacin da jam'iyyar NPP take neman lashe zaɓe karo na uku a jere a mulki.
Ƴan Ghana sun shiga matsananciyar tsadar kayayyaki, tun daga farko-farkon shekarar 2022, inda farashin kayayyaki ya yi tashin da ba a taɓa gani ba a sama da shekara 20 da suka gabata.
Hauhawar farashin ya kai maƙura ne a watan Disamban 2022, inda ya ƙaru da kashi 54.1. Sai dai ya ɗan sauko ƙasa, amma wasu kayayyakin masarufin sun cigaba da tashi.
Misali, farashin ƙwai da tumatur sun ƙaru da kusan ninki biyu a watan Fabrairun 2024 idan aka kwatanta da farashin a cikin shekara ɗaya.
Sai dai fitaccen abincin ƙasar - Ga kenkey (wanda ake yi da masara) da kifi - bai ƙara farashi ba sosai, amma an rage girmansa.
Hauhawar farashin ya ƙara jefa mutanen ƙasar cikin talauci, kamar yadda bankin duniya ya nuna.
A shekarar 2022, Ghana ta gaza biyan bashin da ake binta, inda ta shiga tattaunawa da hukumomin bada lamuni na duniya domin sake fasalin basussukan, wanda har yanzu ba a kawo ƙarshensa.
Su kuma masu bayar da lamunin na cikin gida an tilasta musu rage yawan kuɗaɗen da ake biyan su.
Haka kuma gwamnatin ƙasar ta buƙaci Asusun Bayar da Lamuni domin neman ɗauki da samun sauƙin biyan basussukan da kenta.
Shugaban ƙasa Nana Akufo-Addo ya tabbatar da cewa ƙasar "na cikin matsala" amma sai ya zargi wasu da hannu a lamarin.
Kuɗin da ake bin Ghana ya ƙaru a cikin shekara goma da suka gabata, musamman daga shekarar 2019 da 2022, inda ya zama gwamnatin na buƙaatar sama da kashi 70 na kasafin kuɗinta domin biyan bashi.
Taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar ya ƙara bayyana ne da rashin aikin yi a ƙasar.
A shekara 20 da suka gabata, ɗan Ghana 1 cikin mutun 20 ne ke fama da rashin aikin yi - amma yanzu ya koma mutum ɗaya cikin bakwai.
Yanzu kusan rabin ƴan ƙasar - kusan mutum miliyan 24 - waɗanda suke ƙasa da shekara 35 suna fama da ƙuncin rayuwa.
Abin da matasan ƙasar waɗanda suka isa kaɗa ƙuri'a suke tunanin zai yi tasiri wajen sauya akalar zaɓen.
A matsayin ƙasa mafi arzikin zinare a Afirka - kuma ta goma a duniya - shi ya sa batunsa ke da matuƙar muhimmanci a tattalin arzikin ƙasar.
Haƙo zinare na cikin batutuwa masu muhimmanci a zaɓen, inda ake tattauna irin illar da haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ke yi wa muhalli a ƙasar.
Zinare na taimakawa wajen samar da kuɗin shiga ta Ghana - a shekarar 2023, ƙasar ta samu $5.2bn (£4.1bn).
Bayan zinare, ƙasar na da man fetur da tagulla da lithium da sauransu.
Ƙasar kuma tana cikin ƙasashen da suke juya kasuwar cocoa a duniya, inda ta zama ta biyu wajen fitar da shi.
Waɗannan ma'adinan ne suka sauya tattalin arzikin ƙasar a shekara 30 da suka gabata, inda ta ƙara arziki, kamar yadda bankin duniya ya nuna.
Haka kuma abubuwan da ƴanƙasar ke samu ya ƙaru tun daga 2005, inda yanayin rayuwa ya inganta tun daga 2017.
Tun daga lokacin, ya ɗan dakata, sai a shekarar 2021 da ya ƙara tashi.
A yanzu da ake shirye-shiryen kaɗa ƙuri'a, ƴansiyasa suna mayar da hankalinsu kan cewa masu kaɗa ƙuri'a ba su cika amfani da tunanin abubuwan nesa ba, inda suka fi mayar da hankali kan abubuwan da za su gani a ƙasa cikin ƙanƙanin lokaci.
A cikin shekara 30 da suka gabata, zaɓukan ƙasar na gudana ne cikin lumana, kuma suna zafi matuƙa.
Hakan ya sa ake wa Ghana kallon zakarar gwajin-dafi saboda duk da fama da juyin mulki da ta sha a baya, yanzu dimokuraɗiyyarta na tafiya da kyau.
Sannan duk da cewa a wasu lokutan a kan samu masu ƙalubalantar sakamakon zaɓen, yawancin waɗanda suka sha kaye suna amincewa da shi.
Muna na sa ran samun sakamakon zaɓen na bana a cikin kwana uku daga ranar 7 ga Disamba da aka kaɗa ƙuri'a