Me ya sa ake alaƙanta masu sana'ar gwangwan da tafka laifuka?

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, wani abu da ya dade yana ci wa mutane tuwo a ƙwarya a yanzu shi ne sace-sacen kayan amfanin gida, musamman masu nauyi irin ƙarafa, abin da a lokuta da dama ake alakantawa da masu sana’ar tarawa da sayar da karafa, wato gwangwan.

Matsalar ta fi kamari ne a birane ko kuma garuruwa masu yawan al’umma.

An sha samun labaran inda ake zuwa gida a sace ƙarafa ko tukunyar abinci ko wasu kayan gidan da ake amfani.

A lokuta da dama, idan aka samu wata matsala ko aka yi wata sata a unguwa, akan zargi ƴan gwangwan ɗin ko ƴan bola, wanda haka ya sa wurare da dama suke sa musu ido idan an gansu, wasu lokutan ma wasu sukan nuna kyara ga mabarata ko kuma duk wani wanda aka gani da dauɗa.

Ana dai yawan ɗora zargin laifin sata da wasu laifuka kan matasa ƴan gwangwan ɗin, lamarin da jagororinsu suka musanta.

Me ya sa ake musu kallon haka?

A watan Nuwamban 2023 ne Ministan Abuja, Nyesome Wike ya ƙaddamar da matakin kama mabarata, waɗanda ya ce sun cika titunan Abuja, har ma sun zama barazana ga tsaron birnin, kuma suna zubar da mutuncin Najeriya.

Lamarin, wanda ya ƙara fitowa bayan wani lauya mai kare haƙƙin ɗan'adam, Abba Hikima ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar matakin, ya ƙara jawo muhawara kan ayyukan ƴan gwangwan da sauran ƴan bola jari.

Haka kuma a makon nan ne rundunar ƴansandan Najeriya reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum 50 da take zargi da ɓallewa tare da sace murafai na kwatamin titunan birnin.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukan zumunta ta ce samamen da ta kai ne ya ba ta nasarar kama mutanen, inda kuma dakarunta suka ƙwato murafai 25.

Birnin na Abuja ya daɗe yana fama da waɗannan sace-sace, inda ake yawan cire murafen da ke tsakiya ko gefen titi.

"Bincike ya tabbatar cewa masu satar na aiki ne a matsayin wani gungu da ke sayar da murafan ga dillalan ƙarafa," in ji sanarwar wadda ta lissafo sunayen mutum 50 ɗin.

Daga cikin abubuwan da ta ce ta ƙwace a hannun mutanen har da turakun lantarki masu amfani da hasken rana na gefen titi, da ababen hawa uku, da rodin gina gadodji, da sauran abubuwan da suke amfani da su wajen lalata kayan gwamnati.

Daga baya kuma ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja ta ce an gano masu sayen murafan, inda ta ce wani kamfani ne yake saya wurin dillalan ƙarafa.

Muna ƙoƙarin tsabtace harkokinmu - Shugaban ƴan gwangwan

Ƙungiyar ƴan gwangwan masu sayen ƙarafa waɗanda ba a amfani da su a Najeriya sun ɗauki matsaya, tun bayan samun ƙaruwar rahotannin satar ƙarafa da kadarorin gwamnati a faɗin ƙasar.

Shugabannin ƙungiyar sun bayar da sanarwar tsauraran matakai don tunkarar wannan lamari, da suka haɗa da rajistar mambobin ƙungiyar da ba da riga ta bai ɗaya da kuma gabatar da iyayen gidansu da za su zama wakilansu cikin harkokin kasuwancinsu.

Shugaban riƙon-ƙwarya na ƙungiyar na ƙasa Alhaji Ibrahim Ɗan Soja ya bayyana wa BBC waɗannan sababbin matakan za su taimaka wajen nesanta kansu daga masu aikata laifuka tare da inganta ayyukan daƙile satar kadarorin gwamnati da dawo da martabar sana'ar tasu.

Ya bayyana cewa suna takaicin yadda ɓatagari suke shigo cikin harkokinsu suna ɓata musu suna, inda ya ce suna rajista da gwamnati.

A game da tambayar abin da zai ce kan yawan zargin ƴan gwan-gwan da sace-sace ciki har da na kayan gwamnati, sai ya ce, "Mai ɗaki shi ya san inda ruwa yake zuba, amma wannan kayan na gwamnati da ake magana ba zan ce babu mutanenmu a ciki, kuma ba zan ce akwai su ba. Amma dai ba za mu bar ɓatagari sun shigo su ɓata mana suna ba."

Ya ƙara da cewa, "Muna kira ga duk wani mai harkar gwan-gwan, ya zo ya yi rajista da mu domin gwamnati ta san cewa mu ba ɓatagari ba ne kuma tsarin da muka ɗauko shi ne dole ka zo ka yi rajista," in ji shi.

Ya ce wanda bai yi ba jami'ansu za su kama su, su miƙa su ga gwamnati, "saboda ɓata mana suna da suke yi cewa su ƴan gwan-gwan ne, alhalin ba ƴan gwan-gwan ba ne."

A Najeriya kaɗai ake samun haka?

Ba a Najeriya kaɗai aka daɗe ana zargin masu harkar gwan-gwan ɗin da aikata laifuka ba.

Ko a watan Janairun shekarar 2022, Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya haramta sayar da tarkacen tsoffin ƙarafuna saboda yawaitar satar kayayyakin ƙarafuna da ake yi a kasar.

Ya ɗauki matakin ne a lokacin saboda ɓarnata muhimman kayayyakin gwamnati da ake yi domin a sayar da ƙarafunansu.