Modric ne mafi shekaru da ya buga wa Madrid wasa a tarihi

Lokacin karatu: Minti 1

Luka Modric mai shekara 39 ya zama ɗan wasa mafi shekaru da ya taɓa buga wa Real Madrid wasa, a wasan da ta doke Celta Vigo a La Liga.

Dan ƙasar Croatia da ya shiga wasan a canji shi ne ya bai wa Vinicius kwallon da ya ci, wadda kuma ta kai ga nasarar da ƙungiyarsu ta samu a wasan.

Real Madrid yanzu tana maki daidai da Barcelona, wadda za ta fafata da Sevilla, sai dai banbanci kwallaye da kuma wasa ɗaya da Madrid ta buga sama da Barcelona.

Kocin ƙungiyar ya bayyana Modric a matsayin babban ɗan wasa mai cikakkiyar kwarewa".

"Abin alfahari ne zama kocin Modric, da kuma aiki tare da shi. Duk abin da yake son cimmawa yana kai wa ga hakan, kuma ya cancanci hakan" Kamar yadda Anceloti shaida wa gidan talabijin na Real Madrid.

Sun samu nasara ne a minti 20 bayan kwallon da Kylian Mbappe ya ci daga nesa, Camavinga ne ya ba shi kwallon ya mata taɓawa ɗaya ta shiga raga.

Madrid ba ta mamaye wasan ba kamar yadda ta saba, saboda Celta Vigo ita ma ta yi amfani da damarmakinta.

"ina jin dadi mum yi nasara bayan dawowa daga wasan ƙasashe, wanda abu ne mai kamar wuya a mafi yawan lokuta," in ji Anceloti.

Real Madrid za ta buga wasanta na gaba ne da Borussia Dortmund a gasar Champions a ranar Talata.