Me ke jawo warin baki kuma yaya za a magance shi?

Asalin hoton, Getty Images
Kana kauce wa haɗuwa ko zuwa kusa da mutane saboda bakinka na wari? Kar ka damu wannan ba wani abu ba ne na daban kuma akwai hanyoyi da dama na maganace shi
Tsaftace haƙori abu ne da kusan za a iya cewa yaƙi ne da 'yan ƙananan halittu na bakteriya da ke kama wuri su zauna a tsakanin haƙoranmu da kuma harshenmu, da ba ranar daina shi.
Idan ba ka kawar da waɗannan 'yan ƙananan halittu na bakteriya ba za su hayayyafa ne a nan har su janyo maka cutar da za ta yi illa sosai ga dadashinka.
To amma akwai hanyoyin da za ka magance hakan.
Me ke janyo warin baki?
Yawanci babban abin da ke janyo warin baki a faɗin duniya shi ne zagwanyewar dadashi ko kuma cutar da ta shafi dadashi.
''Rabin yawan manyan mutane na kamuwa da aƙalla wani nau'in cutar dadashi,'' in ji Dr Praveen Sharma na Jami'ar Birmingham a Birtaniya a tattaunawarsa da BBC.
Likitan ya ce kusan kashi 90 cikin ɗari na warin baki, daga bakin yake, yayin da sauran kashi 10 kuma wasu abubuwa ne ke janyowa.
''Mai cutar sukarin da ba ya kula ko bin ƙa'idoji warin bakinsa daban ne,'' in ji Dr Sharma.
''Idan kana da maras lafiya da ke fama da larurar da ta shafi kayan ciki, ko wadda ke janyo amai, za ka ji warin bakin wannan mutumin tsami-tsami ne. Wannan na nuna wani warin bakin nada alaƙa da wata cutar da mutum ke fama da ita a cikin cikinsa,'' in ji likitan.
To me za a iya yi dangane da hakan?

Asalin hoton, Getty Images
- Gano ainahin matsalar
Idan ba ka raba bakinka da 'yan ƙananan halittu na bakteriya da ke maƙalewa a tsakanin haƙoranka da dadashi, za su iya haddasa maka ƙananan raunuka ta yadda za ka ga dadashinka na jini.
Wannan shi ne matakin farko-farko na cutar dadashi, to amma daɗin abin shi ne ana iya maganinta.
Likitan ya ce: ''Alamun wannan cuta za ka ga idan kana goge bakinka da burushi dadashinka ya yi ja ya kumbura sannan kuma yana jini, to wannan shi ne farko-farkon cutar.''
- Wanke baki yadda ya kamata
Dr Sharma ya ce kana buƙatar ka samu lokaci ta riƙa wanke bakinka sosai.
Kar ya kasance ka raba hankalinka biyu - kana wani abu yayin da kake wanke haƙoranka a cewar likitan.
A ƙa'ida ya kamata ka tsaya a gaban mudubi lokacin da kake goge bakinka- ka mayar da hankali sosai a kai.
Yawancin mutane masu amfani da hannun dama ba su sani ba suna wanke ɓangaren bakinsu na hagu fiye da na dama, yayin da su kuwa masu amfani da hannun hagu suke wanke ɓangaren dama fiye da na hagu - wanda wannan zai iya haifar da wannan cuta ta dadashi a bangaren da ba ya samun wankin sosai.
Saboda haka sai a lura sosai da wane ɓangare ka fi wankewa ta yadda za ka gyra ka rika wanke duka ɓangarorin biyu sosai.
- Laƙanci yadda ya kamata ka goge bakinka
Dr Shamra na ganin ya fi dacewa mutum ya fara amfani da ɗan ƙaramin burushi mai shiga tsakanin haƙori da haƙori.
Saboda wannan shi ne zai fi fitar da datti a tsakanin haƙora da kuma ƙara lafiyar dadashi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan amfani da ɗan ƙaramin burushi mai shiga tsakanin haƙora, yana da kyau kasan yadda za ka yi amfani da burushi wajen goge bakinta, ba abu ne na hanzari ba.
Ka sani cewa kowane haƙori jikinsa linki uku ne : na waje da na tauna da kuma nacan ciki. KOwannensu na buƙatar ka wanke shi cikin natsuwa.
Za ka yi mamakin cewa ana son ka wanke bakinta tsawon aƙalla minti biyu.
Sannan yadda yawancin mutane suke riƙe burushi ma a lokacin wanke baki ba daidai ba ne.
Za ka ga yawanci suna riƙe burushin ne a kwance suna gurzawa a haƙoran zuwa gaba da baya, to wannan ba daidai ba ne domin yana iya haddasa matsalar gurjewar dadashi.
A ƙa'ida ana son ka riƙe burushin ne a ɗan karkace (kusurwar digiri 45, saɓanin ta 90) kana goge haƙoran a hankali
Ana so ka riƙagoge haƙorandaga ƙasa zuwa sama, wannan zai taimaka wajen fitar da duk wani datti da ƙwayar cuta da za ta iya maƙalewa a ƙarƙashin dadashin.

Asalin hoton, Getty Images
- A goge baki a lokacin da ya dace
Da dama daga cikinmu ƙila an koyar da mu cewa wanke baki bayan cin abinci abu ne mai kyau. To amma ba haka nan ba.
"A ƙa'ida, za ka wanke bakinka ne kafin ka karya kumallo," in ji Dr Sharma.
Bai dace ba ka wanke bakinka bayan ka ci ko ka sha wani abu mai tsami ba - idan ka yi burushi a lokacin hakan zai iya rage wa haƙorinka ƙarfi.
Saboda haka goge bakinka kana kammala cin abinci abu ne da zai iya yin illa ga haƙorinka.'' In ji likitan.
Likitan ya ce : "Idan har ka fi son wanke bakinka bayan ka karya kumallo, to ya kamata ka bayar da tazara a tsakanin lokacin da ka ci abincin da kuma na wanke bakin."
Za ka iya kurkre bakinka ka jira zuwa wani ɗan lokaci kafin ka wanke shi.
Haka kuma yayin da wasu ke wanke bakinsu tsawon miniti biyu sau biyu a duk rana wasu kuwa idan suka wane sau ɗaya da kyau suna ganin ya wadatar da su.
Lokacin da kake bacci zuwan yawunka na raguwa, wanda hakan ke bayar da dama da ƙananan halittu na bakteriya su fi yi wa haƙoranka illa da daddare.
Saboda haka idan har sau ɗaya za ka wanke bakinka to lokacin da ya fi dacewa shi ne da daddare.
- Zaɓi burushi da man wanke bakin da suka fi dacewa
''Ka yi amfani da burushi mai tsaka-tsakin karfi - wato wanda ba shi da laushi sosai ko kuma mai karfi sosai.
Shi kuwa man wanke bakin ba sai wani mai tsada ba, idan dai har yana da sinadarin fuloraid (fluoride),'' in ji Dr Sharma.
Sinadarin yana ƙara ƙarfin haƙori da kuma hana shi ruɓewa.
Haka kuma yana da kyauka yi amfani da sinadarin wake baki na ruwa idan kana ganin alamun cutar dadashi, saboda yana taimaka wa wajen rage dattin haƙori da hana taruwar ƙwayoyin bakteriya.
To amma fa kada ka yi amfani da wannan ruwa bayan ka goge bakinka da burushi domin wannan ruwan zai iya wanke sinadarin da ke ƙara ƙarfin haƙori.

Asalin hoton, Getty Images
- Gane mummunar cuta da ka iya illa ga dadashi
Idan cutar dadashi ta ci gaba, za ka ga ƙofar da ke tsakanin haƙori da haƙori ta ƙaru, kuma yayin da ƙashin da ke riƙe da haƙorin ke zaizayewa, haƙorin zai iya soma rawa.
Idan ba a nemi magani ba cutar ta ci gaba to za ta iya kaiwa ga zubewar haƙora.
Bubu da ƙari bakin mutum zai kuma riƙa wari. To da ka ga waɗannan alamu ka garzaya wajen likitan haƙori kai tsaye.
A ƙarshe ga wasu hanyoyi da cikin sauri za ka iya amfani da su wajen magance warin baki:
- Ka riƙa shan ruwa sosai saboda ƙwayoyin cuta na bakteriya sun fi girma idan bakin mutum a bushe yake.
- Ka riƙa goge harshenka. Wannan na kawar da ɓurɓushin abinci da ƙwayoyin bakteriya da ƙwayoyin halitta da suka mutu, kuma duka waɗannan abubuwa ne da ke sa warin baki.
- Idan ba ka da tabbaci kan yadda bakinka yake - da wari ko ba wari to ka nemi abokinka ko wani ɗan'uwanka ya jiye maka. To amma fa ka san mutumin da za ka sa ya yi maka hakan.











