Jagororin addini na Tibet masu amfani da ruhi ɗaya a ɗaruruwan shekaru

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Shugaban addini na yankin Tibet Dalai Lama, wanda ya cika shekara 90 ranar Lahadi, ya tabbatar cewa zai samu magaji idan ya rasu.
Ya ce majalisar Gaden Phodrang Trust ce kaɗai - wadda ya kafa - take da ikon yanke hukunci kan magajin nasa.
Dalai Lama na 14 ya fitar da sanarwar da aka daɗe ana jira ne a Dharamshala da ke arewacin Indiya, inda yake gudun hijira daga China.
Sanarwar na zuwa ne bayan an fara nuna fargaba cewa China za ta iya gabatar da nata ɗan takarar.
A martanin da ta mayar, China ta ce dole a samu sabon Dalai Lama a cikin ƙasar kuma sai gwamnatin tarayya ta amince tukunna.
Ƙasar China mai bin tsarin kwamunisanci ta mamaye yankin Tibet a 1951 kuma tana kallon Dalai Lama a matsayin ɗan'aware.
Wane ne Dalai Lama?

An yi imanin cewa Dalai Lama ɓurɓushin wani waliyyi ne na Tibet, wanda ake kira Avalokiteshvara ko Chenrezig.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamar mabiya addinan Hindu da Jain, mabiya addinin Buddah sun yi imanin cewa za a sake tayar da kowane mutum bayan mutuwa. A al'adar 'yan Tibet, suna ganin mutanen da suka fi ƙarfin imanin na iya zaɓar wuri da kuma lokacin da za a sake tashin su.
An haifi Dalai Lama na yanzu ranar 6 ga watan 1935, inda iyayensa talakawa ne manoma a arewa maso gabashin Tibet. Yana ɗan shekara biyu aka amince da shi a matsayin Dalai Lama na 13 ne da ya taso.
"'Yan Tibet sun yi imanin cewa ruhin Dalai Lama ne ake sake tayarwa lokaci bayan lokaci," a cewar Dr Thupten Jinpa.
Dr Jinpa tsohon mai wa'azin addinin Buddah ne, wanda ya kai har muƙami mafi ƙololuwa na malinta. Shi ne tafintan Dalai Lama a hukumance tun daga 1985.
Ya ce dukkan Dalai Lama cigaba ne kan ruhin mutum ɗaya kamar yadda al'ada ta tabbatar, amma kuma na yanzu da alama ba ya ɗabbaƙa imanin a haƙiƙa.
"Na sha jin Mai Martaban yana cewa bai yarda cewa dukkan mutum 14 da aka yi mutum ɗaya ba ne," kamar yadda Dr Jinpa ya shaida wa BBC. "Amma duk wanda yake da wannan jinin yana da wani alaƙa ta musamman da Dalai Lama."
Addinin Buddha ya yi sama da shekara 2,500 a duniya, amma jagorancin Dalai Lama ya zo ne daga baya-bayan nan.
"Yayin da aka riƙa kiran Dalai Lama na farko da sunan Gedun Drup, wanda aka haifa a 1391, tsarin tsohon malamin addinin Bhudda ya koma rayuwa a jikin wanda ya gaje shi lamari ne ya fi haka daɗewa," in ji Farfesa Martin A Mills, daraktan Cibiyar nazarin kan yankin Himalaya a Jami'ar Aberdeen.
"Wannan tsari ya samo asali aƙalla shekara 300 gabanin haka," kamar yadda ya yi bayani.
Ta yaya ake zaɓen Dalai Lama?

Asalin hoton, Christopher Michel
"Tsarin zaɓen Dalai Lama abu ne mai wahala, da sarƙaƙiya da kuma faɗi," in ji Dr Jinpa.
Za a iya ɗaukar shekaru kafin a iya gane wanda zai hau matsayin.
Manyan malaman Buddha ne ke dubawa da yin bincike domin gano yaron da aka haifa daidai lokacin da Dalai Laman da ya shuɗe ya mutu, sukan yi hakan ne ta hanyar amfani da wasu alamu.
A wani lokaci ɗaya daga cikin manyan malaman zai iya samun wasu daga cikin bayanan yaron a cikin mafarki.
Haka nan kuma ana amfani da ɓangaren da hayaƙin kona gawar tsohon Dalai Lama a matsayin wata alamar inda ruhin nasa zai shiga jikin yaron.
Da zaran aka gano yaron, za a tara masa kaya da yawa. Idan yaron ya iya gane wasu kaya mallakin tsohon Dalai Lama, manyan malaman za su ɗauki hakan a matsayin wata babbar alamar shigar ruhin.
Idan manyan malaman suka gamsu , za a zaɓi yaron sannan a fara ba shi horo kan abubuwan addini da karatu kan imani.
Dalai Lama biyu ne kawai aka taba haifa a wani wuri ba cikin yankin Tibet ba: ɗaya an haife shi ne a Mongolia, ɗaya kuma a arewa maso gabashin Indiya.
Tsoma bakin China

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 1950, China ta tura dubban dakarunta zuwa Tibet domin tabbatar da ikonta. A shekarar 1959 bayan gazawar wata tarzomar adawa da China, Dalai Lama ya tsere daga ƙasar ya koma Indiya inda ya kafa gwamnati.
Duk da cewa ya sauka daga shugabancin Tibet daga ƙetare, ana masa kallon wani ginshiƙi na nuna turjiya daga mulkin China.
A baya Dalai Lama ya bayyana cewa ruhinsa zai sauya gangar jiki ne a wani wuri ba cikin Tibet ba - wani abu da ke alamta adawa da abin da yake faruwa a Tibet ƙarƙashin ikon China.
China ta yi watsi da lamurran Dalai Lama, tare da bayyana shi a matsayin mutumin da ya yi gudun hijirar siyasa wanda ke 'ruruta wutar ayyukan turjiya ga ikon China ta hanyar fakewa da addini".
A shekarar 2007 China ta fito da wani tsari wanda ake ganin yunƙuri ne na karɓe iko da tsarin zaɓen Dalai Lama na gaba.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun sha nuna damuwa kan tsoma bakin China a cikin lamurran Tibet.
Matsi kan Tibet

Asalin hoton, Getty Images
Za a iya ɗaure duk wani mutumin Tibet da aka samu da laifin yin magana da ƴan jarida na waje ko kuma bayyana hoton Dalai Lama a fili.
Ta hanayr wani mai fafutika na Tibet mazaunin Indiya, BBC ta samu damar tattaunawa da wasu manyan malaman addini da ke rayuwa a Tibet, ɗaya daga cikinsu mabiyin Buddha ne.
Sun ce hukumomi na ɗaukar matakan hana duk wani bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Dalai Lama.
Dalai Lama na gaba

Asalin hoton, Getty Images
Dalai Lama na 14 ya nanata cewa ya kamata a kare wannan al'ada wadda ta kwashe shekara 600 ana yin ta.
Domin kare duk wani tsoma bakin China a wurin zaɓen magajinsa, Dalai Lama ya shaida wa mabiyansa cewa kada su amince da duk wani da China ta yi ƙoƙarin naɗawa kan matsayin a nan gaba.
"Mutane za su iya yin kawaici saboda ba su son su rasa rayukansu, amma ba za su taɓa amincewa da Dalai Laman da gwamnatin China ta naɗa ba," in ji Dr Jinpa.
"China za ta iya yin iko da al'umma, sai dai ba za ta iya juya ra'ayi da abin da ke cikin zukatan al'ummar Tibet ba," kamar yadda ya ƙara fada.
Beijing na ci gaba da nuna cewa ta ƴanta "bayi" tare da ɗora Tibet a kan turbar ci gaban zamani a maimakon koma-baya na addini.
Amma mabiya Dalai Lama za su ci gaba da ƙoƙarin ganin jagorancin mabiya Buddha na Tibet na cin gashin-kansa ba a karkashin ikon China ba.






