Girman matsalar sayar da takardun ɗaukar aiki a Najeriya

Ma'aiktan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Najeriyar ta bayar da umurnin a gudanar wani sabon shirin tantance dubban ma'aikatan gwamnatin tarayya da aka ɗauka aiki daga shekarar 2013 zuwa 2020 domin tnatance ma'aikatan bogi.

Umarnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ke ɗauke da sa hannun babban sakatare a Hukumar ɗaukar ma'aikata ta ƙasar, ta ce duk wani ma'aikaci da aka samu da takardar shaidar daukar aiki ta bogi, zai fusakanci matakin kora.

Hakan ya biyo ƙorafe-ƙorafen da ƴan ƙasar da dama ke yi dangane da badaƙalar sayar da guraben ɗaukar aikin gwamnatin Najeriya da aka tafka tsakanin shekaru bakwai.

Wannan dai zuwa ne bayan da wani jami'i a sashen ɗaukar ma'aikata na Ma'aikatar Ayyuka, Mista Martins Oghenewore, ya bayyana cewa wasu jami'an gwamnati sun shafe shekaru suna sayar da guraben aiki kan farashin kusan naira miliyan 2.5, tare da bai wa masu siya takardun bogi na ɗaukar aiki abin da ya ce har ya jawo ana masa barazana.

'Yadda aka yi min damfara'

Wani mutum da BBC ta ɓoye sunansa, wanda shi ma ya fada tarkon badaƙalar, ya shaida cewa da kuɗinsa ya ringa neman takardar aiki amma kuma bai yi dace ba.

"An sayar da kayayyaki daga gidanmu domin a haɗa kuɗin siyan aikin. Na nemi aiki a Prison Service da Immigration da Civil Defence da Ƴansanda da Kwastam da hukumar kashe gobara — amma duk na ƙarya ne. Sun ci kuɗina banza, har yanzu ban samu aikin ba," in ji shi.

Ya kara da cewa, "ina so waɗanda suka cuce ni su sani akwai gobe, kuma za mu tsaya gaban Allah. Na yi firamare, sakandire da diploma, amma duk wannan bai hana su cutar da ni ba."

'An daɗe ana yin wannan badaƙala'

Wani tsohon ma'aikacin gwamnatin Najeriya mai muƙamin direkta wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wannan badaƙala ta daɗe tana faruwa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewarsa: "Wasu za su sa mutane su cike fom da sunan neman aiki, amma daga baya ka ji an dauki wasu ba tare da ka san yadda aka yi ba. Wannan ne ya sa ayyukan gwamnati ba sa tafiya yadda ya kamata. Wasu ma'aikatan ba su da ƙwarewa saboda ba su shiga aikin bisa ka'ida ba."

Ya yi kira da cewa, ya kamata a sallame su, domin aikin gwamnati ya kamata ya kasance na masu cancanta kawai.

Ya bayyana ra'ayinsa na cewa duk wanda aka gano yana aiki da takardar bogi bayan bincike inda ya ce

"Aikin da mutum bai shiga ba ta kan ƙa'ida ba, kuma ba ka da ilimin da ya kamata dangane da wannan aiki, ai ba yadda za a yi, dole ne a fidda mutane."

Rahotanni sun ce zargin dai ya shafi ma'aikatun aikin gona da na tsaro da na ilimi da shari'a da sauransu.

An umarci ma'aikatan da abin ya shafa su hallara domin tantance su daga ranar 18 ga wannan wata na Agusta tare da sahihan takardun da aka ɗauke su aikin.

A Najeriya dai an daɗe ana zargin yadda manyan ma'aikata ke sayar da ayyukan gwamnati ga masu hali yayin da ake barin ƴaƴan talakawa hannun Rabbana abun da ke ƙara ta'azzara cin hanci da rashawa da samun babban gurbi a wasu ma'aikatu kasancewa an yi watsi da jarabawar tantancewa kafin a ɗauki aiki da aka sani tun asali.