Ronaldo ya zama na farko da ya ci ƙwallo 900 a tarihi

Lokacin karatu: Minti 1

Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ya ci ƙwallo 900, a wasan Nations Lig da Portugal ta yi nasara kan Croatia.

Kwallon da ɗan shekara 39 ya ci a minti na 34 a cikin yadi na shida, ya bai wa Portugal damar sa ƙwallo biyu a raga.

Ya ƙara faɗaɗa tarihinsa a Portugal ta yadda ya ci ƙwallo 131 cikin wasanni guda 209, abin da ya sanya shi kafa tarihin fin kowa cin ƙwallo da buga wasanni a ƙasarsa.

Messi ne na biyu a jerin da Ronaldo ke jan ragama sai kuma tsohon ɗan wasan Iran Ali Daei da ke da kwallo 109.

Ɗan wasan bayan Manchester United Diogo Dalot ne ya fara ci wa Portugal ƙwallo amma daga baya ya ci gida, duka hakan ya faru ne gabanin hutun rabin lokaci.

Ƙwallayensa sun haɗa da wanda ya ci a Sporting LIsbon da Manchester United da Real Madrid da Juventus da kuma ƙungiyarsa da yake bugawa yanzu Al-Nasar ta Saudiyya.

Ronaldo da ya lashe Ballon d'O sau biyar, ya bai wa abokin hamayyarsa Lionel Messi wanda ke da ƙwallo 842 bambancin ƙwallo 58. Sai ɗan wasan Brazil Pele a matsayi na uku da ƙwallo 765.

Ronaldo ya fara kai wa ƙwallo 800 ne a ƙarshen shekarar 2021 lokacin da ya koma Manchester United.

Ɗan wasan ya ci ƙwallo 769 ne a duka ƙungiyoyin da ya buga wa kwallo. Kuma har yanzu yana ci gaba da taka leda.

A wata hira da ya yi da tsohon ɗan wasan bayan Manchester United da Ingila, wanda sun taka leda a tare a baya, Rio Ferdinand ɗan wasan ya ce so yake ya kafa tarihin cin ƙwallo 1,000 a tamaula.