Kotu ta raɗa wa yaro suna bayan shekara uku ana taƙaddama tsakanin iyaye

Stock image of a baby's foot on a white cloth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...
    • Marubuci, Imran Qureshi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ba baƙon lamari ba ne a samu saɓanin ra'ayi tsakanin miji da mata wajen raɗin sunan jariri, sai dai ba kasafai hakan ke ƙarewa a kotu ba.

Sai dai wasu ma'aurata a jihar Karnakata da ke kudancin ƙasar Indiya sun tsinci kansu a wani yanayin da suke buƙatar shiga-tsakanin kotu kan matsalar, bayan kwashe shekara uku suna taƙaddama kan sunan ɗansu.

Taƙaddamar ta ƙazance ta yadda ma'auratan biyu ke neman a raba auren nasu.

Lamarin ya faro ne a shekara ta 2021, lokacin da matar ta koma wakan jego gidan iyayenta bayan haihuwar ɗa namiji.

Zuwa gida wankan jego wata sananniyar al'ada ce a Indiya.

A al'ada, mijin ne zai je ya ɗauko matarsa bayan kammala wanka domin dawowa gida.

To amma a lokacin da matar mai shekara 21 a duniya ta ƙi amincewa da sunan da mijin nata ya raɗa wa ɗansu, sai mijin ya ƙi zuwa domin ɗauko ta - kuma har yanzu bai je ya ɗauko ta ba.

Ita dai matar ta raɗa wa ɗan nasu suna Adi - wanda ta samar ta hanyar haɗa harafin farko na sunanta da kuma wani ɓangare na sunan maigidan nata, in ji Sowmya MN, mataimakiyar mai gabatar da ƙara na yankin Hunsur.

Bayan shafe shekaru tana zaune a gidan iyayenta ba tare da mijin nata ya je ɗauko ta ba, sai matar ta shigar da ƙara a kotun garin Hunsur da ke yankin Mysuru tana neman mijin nata ya biya ta kuɗin kula da yaro.

Lauyan matar mai suna MR Harish, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya kai ga cewa a tana neman a raba auren nasu.

Da farko an shigar da ƙarar ne a wata ƙaramar kotu, inda daga bisani aka mayar da ƙarar zuwa wata kotun al'umma, inda ake iya warware matsala ta hanyar sasanci.

Duk da shawarwarin da alƙalai suka ba su, ma'auratan biyu sun dage kan ra'ayinsu - har zuwa lokacin da kotu ta yanke hukunci raɗa wa yaron suna.

A yanzu an raɗa wa yaron suna Aryavardhana, wanda ke nufin 'abu mai daraja', in ji Sowmya.

Wannan ba shi ne lokaci na farko a baya-bayan nan da kotuna a Indiya ke shiga tsakani domin warware taƙaddama kan sunan jarirai ba.

A cikin watan Satumban da ya gabata, an ƙi ɗaukar wata yarinya a amakaranta kasancewar babu suna a takardar shaidar haihuwarta.

Mahaifiyar yarinyar ta garzaya kotu, inda ta ce hukumomi sun ƙi amnicewa a raɗa mata suna kasancewar mahaifin yarinyar, wanda aurensu ya mutu, ba ya nan.

A ƙarshe, babbar kotun ta umarci a yi wa yarinyar rajista da sunan da mahaifiyar ta raɗa mata, sai a haɗa da sunan mahaifin.