Abin da ya janyo cece-kuce kan janbaki a Chennai

Asalin hoton, Madhavi
- Marubuci, Nithya Pandian
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Tamil
- Lokacin karatu: Minti 4
Wata ma'aikaciyar gwamnati a birnin Chennai da ke kudancin Inidya ta ce an canza mata wajen aiki saboda ta jajircewa cewa dole sai ta shafa janbaki.
Lamarin ya janyo cece kuce a shafukan sada zumunta kuma ya tunzura masu rajin kare ƴancin mata. Madhavi ta shafe shekara 15 tana aiki a ƙaramar hukuma.

Asalin hoton, Madhavi
Madhavi ta zamo mace ta farko da ta riƙe muƙamin babbar mai tsaron lafiyar magajin gari a birnin, shekara uku da ta gabata. Ta samu muƙamin ne bayan Priya Rajan ta zamo mace ta farko daga Dalit da ta zamo magajin garin birnin. Al'ummar wannan yanki ta daɗe tana fuskantar wariya da rashin samun damar shiga a dama da ita a Indiya.
Babban aikin Madhavi shi ne bayar da kariya ga magajin garin, a lokacin da suka shiga cikin cunkoson jama'a.
Madhavi ta ce an fara dambarwar ne a watan Maris, bayan ta shiga wasannin da aka yi domin bikin ranar mata ta duniya, wanda ofishin magajin garin ya shirya.
Ta shaidawa BBC cewa "Sun shirya gasar nuna ƙyau da kwalliya, ni kuma na shiga aka yi da ni"
Madhavi ta yi zargin cewa nan take magajin garin ta fice daga wajen taron, amma daga baya ta tunkare ta da magana.
“Ta tambaye ne dalilin da ya sa na yi tafiyar rangwaɗa a wajen gasar. Amma babu wata tattaunawa a kan sauran abubuwan da suka faru a wajen taron,'' inji Madhavi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ƙara da cewa ''Tun daga lokacin aka fara amfani da janbakin da nake sanyawa a matsayin wani makami na yaƙi da ni''
Madhavi ta yi iƙirarin cewa tun daga lokacin sai babbar mai yiwa magajin garin aiki ta gargaɗi dukkan ma'aikatan ofishin game da sanya janbaki.
"Jikina ne kuma ina da ƴancin sanya duk abin da nake buƙata da ma irin janbakin da nake so. Wa ya basu ikon ƙayyade abin da zan yi da jikina ko wanda ba zan yi ba?"
A ranar shida ga watan Ogusta an samu Madhavi da zuwa aiki a makare domin haka aka tura mata saƙo a rubuce cewa ta yi bayanin dalilin ta na yin hakan.
BBC ta ga wasiƙar da aka aike mata, kuma a cikin ta babu inda aka zargi Madhavi da zuwa aiki a makare, a madadin haka sai aka zarge ta da rashin biyayya ga nagaba da ita da saɓa dokokin aiki.
Madhavi ta shaidawa BBC cewa ta makara zuwa office ne saboda ta karye a ƙafa lamarin da ya sa ta gaza zuwa aikin nata.
Madhavi ta bayar da amsa cewa: "Kun ce in daina shafa janbaki, ni kuma na ƙi dainawa. Idan har hakan laifi ne, to a nuna mani umarnin da gwamanti ta bayar da umarnin da ya haramta shafa janbaki'' Ta kuma shaidawa BBC cewa ofishin bai mayar mata da amsa ba.
A madadin haka ne kuma Madhavi ta ce sai aka yi mata canjin wajen aiki zuwa arewacin Chennai.

Asalin hoton, PRIYARARANDMK/IG
Magajin garin ta musanta dukkan zargin da ake mata da kuma ofishinta, ta kuma jajirce cewa babu wanda ya hana Madhavi sanya janbaki a ofishinta.
Magajin garin ta kuma shaidawa BBC cewa Madhavi ta yi ƙaurin suna wajen zuwa aiki a makare.

Asalin hoton, PRIYARAJANDMK/X
Tsari mai kyau
Mutane fiye da miliyan bakwai ke rayuwa a Chennai. Birnin yana da tarihin shigar mata a dama da su a dukkan harkokin mulki da na tattalin arziki.
Ita ma Rajan ƴar jam'iyyar DMK ce mai iƙirarin bayar da dama ga kowanne jinsi, amma dambarwar da ta taso a kan Madhavi ta jefa shakku a zukatan wasu game da matsayar jam'iyyar.
An tafka muhawara mai zafi a kafafaen sada zumunta game da canza wa Madhavi wajen aiki saboda wannan batu.
"Idan har zargin da Madhavi ta yi gasiya ne, to akwai buƙatar a binciko ko su wanene suka bayar umarnin bibiyar mace da sanya mata dokokin gudanar da rayuwa a wajen aikin gwamnati.'' inji Nivedita Louis, wata mai rajin kare haƙƙin mata a Chennai.
Louis ta ce matakin ya yi ''tsauri sosai''.

Asalin hoton, Greater Chennai Corporation
Son janbaki
Madhavi ta ce ba zata ɗauki matakin shari'a ba domin a mayar da ita muƙaminta a Chennai. Tana fatan ƙorafin mutane a kafafen sada zumunta ya isa ba sai ta kai ƙara ba.
Ta kuma ci gaba da shafa janbaki, amma a yanzu tana amfani ne da masu sauƙin kuɗi.
Ta shaidawa BBC cewa: "Ina matuƙar sha'awar kwalliya duk da cewa bana iya sayen kayan shafa masu tsada, sai irin wanda ake yi a cikin gida. Ina son janbaki sosai.''











