Ko Trump zai yi afuwa ga mutanen da suka yi tarzoma saboda shi a 2020?

Magoya bayan Donald Trump kenan lokacin da suka fantsama cikin ginin Capitol ranar 6 ga watan Janairun 2020

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mike Wendling
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Daga cikin duka magoya bayan Donald Trump, Derrick Evans na da dalili na musamman da zai saka shi farin ciki da sakamakon zaɓen Amurka - yana fatan shugaban zai yi masa afuwa game da shiga tarzomar ranar 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokoki na US Capitol.

"Afuwar za ta sauya min rayuwata," in ji Evans, wanda mamba ne daga West Virginia lokacin da shi da kuma wasu mutum 2,000 suka auka wa ginin a 2021.

Sun yi yunƙurin sauya sakamakon zaɓen Amurka na 2020 ne, wanda mai gidansu Trump ya sha kaye a hannun Joe Biden na jam'iyyar Democrat.

Ya cim ma yarjejeniya da masu shigar da ƙara, inda ya amsa laifukansa na tayar da hankali kuma ya yi zaman gidan yari na wata uku a 2022.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, Trump ya sha cewa zai yi wa masu tarzomar afuwa, waɗanda ya kira da "'yan kishin ƙasa" da kuma "fursunonin siyasa".

Amma har yanzu ba san wa za a yi wa afuwar ba takamaimai - kuma yaushe.

"Ina tabbacin cewa mutum ne mai cika alƙawari," kamar yadda Evans ya fada wa BBC.

A watan Maris, Trump ya rubuta a shafinsa na dandalinsa mai suna Truth Social cewa ɗaya daga cikin abubuwan da zai aiwatar shi ne "sakin masu tarzoma da aka yi garkuwa kuma aka kulle su bisa kuskure".

Ya sake nanata alwashin yayin ganawa da ƙungiyar 'yanjarida baƙar fata a Chicago cikin watan Yuli.

"E tabbas, zan yi hakan," a cewarsa. "Idan ba su aikata laifi ba, zan yi musu afuwa."

Amma kuma bai ce zai yi wa dukkansu afuwa ba, inda ya faɗa wa CCN cewa: "Ina da aniyar na yi wa da yawansu afuwa. Ba zan ce dukkansu ba, saboda wasunsu ƙila sun wuce iyaka."

Har yanzu ana kama mutane

Magoya bayan Donald Trump kenan lokacin da suka fantsama cikin ginin Capitol ranar 6 ga watan Janairun 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Magoya bayan Donald Trump kenan lokacin da suka fantsama cikin ginin Capitol ranar 6 ga watan Janairun 2020
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abubuwan da suka faru ranar 6 ga watan Janairu sun jawo ɗaya daga cikin bincike daga gwamnatin tarayya mafiya girma a tarihin Amurka.

An tuhumi kusan mutum 600 da kai hari, da daƙile aikin 'yansanda, da ƙin ba da haɗin kai.

Waɗanda aka yanke wa ɗauri mai tsawo kamar 'yan ƙungiyar Oath Keepers, Stewart Rhodes, da shugaban Proud Boys Enrique Tarrio ba su shiga rikicin a cikin ginin ba. A madadin haka, an ɗaure su kan haɗa baki wajen raba kan ƙasa saboda shirya tarzomar.

Har yanzu ana kama mutane. Cikin ƙarin bayanin da aka samu a makon da ya gabata, hukumar tsaro ta FBI ta ce har yanzu tana neman mutum tara da take zargi tayar da fitina da kai wa 'yansanda hari.

Amma bayan dawowar Trump, wanda har yanzu ke iƙirari ba tare da hujja ba cewa shi ne ya cinye zaɓen na 2020, babu tabbas game da ci gaban binciken.

Kafar yaɗa labarai ta NBC ta ruwaito cewa jami'ai na mayar da hankali wajen gurfanar da "mafiya girma" a cikin tuhume-tuhumen kafin a rantsar da Trump ranar 20 ga watan Janairu.

Jinkirta shari'a

Yayin da wannan ke faruwa, da yawa daga cikin waɗanda ake tuhuma sun nemi a jinkirta sauraron shari'ar saboda suna tsammanin za a yi musu afuwa.

Daga cikinsu akwai Christopher Carnell, wanda aka samu da laifuka da suka shafi tarzoma a farkon shekarar nan.

Lauyoyinsa sun nemi a ɗaga sauraron sharia'rsa makon da ya gabata saboda "akwai samun rangwame game da lamarinsa", amma ba a amince da buƙatar ba.

Jonathanpeter Klein tare da ɗan'uwansa Matthew sun amsa laifuka a watan Yuli, kuma ya nemi ɗaga zaman yanke masa hukunci da aka tsara ranar 15 ga Nuwamba. Wannan buƙatar ma ba a amince da ita ba.

Akwai Jake Lang, wanda ake tuhuma da laifuka ciki har da kai wa 'yansanda hari, kuma yana yawan wallafa abubuwa a shafukan zumunta daga gidan yarinsa a New York.

Bayan Trump ya yi nasara, ya rubuta a dandalin X cewa: "Zan dawo gida!!! Fursunonin 6 ga watan Janairu na kan hanyar komawa gida!!!"

Iya taku

A watan Janairu ne wasu Amurkawa da ba su ji daɗin sakamakon zaɓen 2020 suka mamaye majalisa.

Asalin hoton, Getty Images

Cibiyar GPAHE ta kuma gano cewa wasu ƙungiyoyi na shirye-shirye a ɓoye har zuwa lokacin da Trump zai sha rantsuwa kuma a yi musu afuwa a hukumance.

Wani saƙo da aka wallafa a shafin wasu ƙungiyoyi da ake kira "Proud Boys" a Telegram ya nuna cewa mambobin ƙungiyoyin su guje wa rantsuwar kama aikin Trump a watan janairu.

Sai dai wani saƙo ya ce kwatanta batun yin afuwar da " cin mutumcin ɓangaren shari'ar ƙasar ne saboda hakan zai sa waɗanda suka yi tarzomar su yi tunanin cewa bore ya halatta a lokacin da aka samu akasi sakamakon da suke son gani ba shi ya bayyana ba."

A yanzu dai sakin duk wani wanda ya shiga cikin wannan bore da kuma aka tuhuma da laifukan tayar da tarzoma ba abu ne mai kamar yiwuwa ba to amma sauran waɗanda ba su tayar da zaune tsaye ba kamar Derrick Evans sun yi kira da a saki irinsu da dama.

Ya kuma bayar da shawarar cewa ba wai kawai a yi masa afuwa ba tare da wasu ya kamata ma a ba su diyyar tsawon lokacin da suka kwashe a tsare.