Abin da majalisar dokokin Amurka ta ce a kan Kwankwaso da Miyetti Allah

Asalin hoton, FB/Rabiu Kwankwaso
Ƴan majalisar wakilan Amurka sun gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.
Haka nan rahoton ya bayar da shawarwari kan matakan da suka kamata Amurkar ta ɗauka wajen magance matsalar.
Wasu ƴan majalisa na jam'iyyar Republican ne suka gabatar da ƙudurin, wanda a ciki suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka kan ya ayyana wasu ƙungiyoyi ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda, sannan kuma a sanya takunkumi kan wasu ƴan Najeriya.
Sauran matakan da ƙudurin ke son a ɗauka su ne hana waɗanda ake zargi da hannu a 'cin zarafin' kiristoci shiga Amurka da riƙe kadarorinsu.
Cikin waɗanda sunansu ya fito ɓaro-ɓaro a ƙudurin akwai tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da Miyetti Allah Cattle Breeders (MACBAN) da kuma abin da ƙudurin ya kira "ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai a Najeriya."
Ƙudurin, wanda aka yi wa laƙabi da 'Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026' an gabatar da shi ne da nufin shawo kan zargin da tun farko Amurka ta yi na cewa ana kashe kiristoci a Najeriya kawai saboda addininsu.
Gwamnatin Najeriya dai ta sha musanta zargin musguna wa Kiristoci a ƙasar, inda ta ce "rashin tsaro ya shafi al'umma a ƙasar ba tare da la'akari da bambancin addini ba".
Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta.
Abin da majalisar Amurka ta gano

Asalin hoton, Boko Haram
Majalisar dokokin Amurkar ta bayyana cewa bincike da ta gudanar, ya gano abubuwa da dama da aka yi wa Kiristoci a Najeriya.
Ta ce "an daɗe ana kashe Kiristoci a Najeriya, inda tun 2009 ake kashewa, garkuwa, fyaɗe da kuma tarwatsa ƙauyukan da Kiristoci ke zama".
Har ila yau, ta ce ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun tilasta wa Kiristoci da dama yin gudun hijira.
Kudurin na majalisar dokokin Amurka ya kuma kiyasta cewa Kiristoci tsakanin 50,000 zuwa 125,000 ne aka kashe saboda yin imani da addininsu daga shekara ta 2009 zuwa 2025, tare da far wa majami'u kusan 19,000.
Sai dai alƙaluma daga masu bincike da masana kan tsaro da dama sun sha bamban da irin wadanda Amurkar ke fitarwa.
Sauran abubuwan da majalisar ta ce ta gano sun haɗa da:
- Ƙungiyoyin ƴanbindiga sun kai hare-hare da dama kan al'ummomin Kirista, abin da ya janyo tarwatsa su daga matsugunansu.
- Tsakanin watan Mayun 2023 da Mayun 2025, ƙungiyoyin Fulani ɗauke da makamai sun kai munanan hare-hare a jihohin Benue Plateau.
- Garkuwa da malaman addinin Kirista waɗanda suke da'awar zaman lafiya
- An kashe shugabannin addinin Kirista sama da 250a shekaru goma da suka wuce, ciki har da rabaren Sylvester Okechukwu a 2025
- Najeriya na da kashi 72 na Kiristocin da aka kashe kan imani da addininsu a faɗin duniya
- An ɗaiɗaita Kiristocin Najeriya kusan miliyan biyar
- Kusan 343,000 ne ke gudun hijira a Tafkin Chadi
Me kudurin ke neman a yi?

Asalin hoton, Nigeria Presidency/X
- Wani ɓangare na kudurin na son a yi amfani da hanyoyin diflomasiyya da kuma na tsaro wajen matsa lamba ga gwamnatin Najeriya don kawo karshen kisan Kiristoci a Najeriya
- Kare al'ummomin Kirista, fastoci har da waɗanda ake far wa marasa galihu
- Tabbatar da cewa an kiyaye dokar ƴancin yin addini a kowane mataki na gwamnati
- Soke dokoki kan yin ɓatanci da sake fursunonin da aka tsare kan addininsu
- Kudurin na son Amurka da Najeriya su haɗa kai don samar da jin-ƙai ga jihohin yankin middle belt
- Kakaba takunkumi da suka haɗa da haramta ba da biza da ƙwace kadarorin wasu jami'an Najeriya waɗanda ke da hannu wajen kashe Kiristoci
- Amurka ta haɗa kai da Najeriya wajen yaƙi da ayyukan masu haƙar ma'adinai daga ketare kamar China da kuma daƙile biyan kuɗi da suke yi wa ƴanbindiga don samun kariya
Tura dakarun Amurka zuwa Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Kudurin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta sanar da tura dakaru kusan 200 zuwa Najeriya domin horar da sojojin ƙasar don yaƙi da masu iƙirarin jihadi, kamar yadda jami'ai suka bayyana.
Ana sa ran za su iso Najeriya a cikin makonni masu zuwa, kuma za su yi aiki tare da wata karamar runduna wadda tuni ta isa ƙasar.
Kakakin sojin Najeriyar, Janar Samaila Uba, ya tabbatar da hakan ga BBC, inda ya ce za su zo ne bayan buƙatar da Najeriya ta yi don ganin an yaƙi ƴan ta'adda.
Ya ce tuni Amurkar ta aika wasu jami'ai na musamman domin ba da shawarwari a faɗin yankuna da dama a Najeriya.
"Har yanzu sojojin Najeriya na da iko kan abubuwa, su ke ɗaukar matakai kuma su za su jagoranc dukkan wasu tsare-tsare na yaƙi da ƴanbindiga," in ji Buba.











