Shin sinadaran ɗanɗano na abinci na da alfanu ga lafiyar jiki?

Asalin hoton, Getty Images
Sindaran ɗanɗano sun zama jigo wajen yin girki na tsawon dubban shekaru: kamar saka yaji, shan shayi mai citta, da kuma wasu sinadarai da ke jikin itatuwa.
Sai dai, a baya-bayan nan, wasu sinadaran ɗanɗano sun zama wani ɓangare da har suke da alfanu ga lafiya.
Sinadarin kurkun (wato turmeric) wanda ake amfani da shi a nahiyar Asiya na tsawon dubban shekaru, ya samo hanya zuwa cikin kantuna a faɗin duniya, kuma a lokacin annobar korona ya kasance mai "ƙara ƙarfin garkuwar jiki" da kare mutum daga cutar.
Sai dai, shin waɗannan sinadarai na da alfanu ga girke-girkenmu, suna kare mu daga cutuka, sannan suna iya lahani?
Alfanun borkono

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin sinadarin ɗanɗano da aka fi amfani da shi, shi ne borkono. Bincike da dama sun nuna irin tasirin da yake ga lafiya, mai alfanu da kuma akasin haka.
Wani na'uin borkonon da aka fi amfani shi ne capsaicin, idan aka ci sa yana aika sako zuwa ƙwaƙwalwa inda yake samar da zafi.
Wasu bincike sun nuna cewa nau'in borkonon yana taimakawa wajen yin tsawon rayuwa.
A 2019, wani bincike da aka yi a Italiya ya nuna cewa mutanen da ke cin sinadaran ɗanɗano a abinci sau huɗu a mako, yana rage barazanar mutuwa kan waɗanda suka ci borkono na'uin chili.
A 2015, masu bincike a China waɗanda suka yi bincike kan nau'in borkonon da ake ci, ya nuna yaha ragewa barazanar mutuwa.
Mutanen da suke cin sinadaran ɗanɗano a abinci a kowace rana na samun raguwar barazanar mutuwa da kashi 14 kan waɗanda suka ci sa kaɗan a mako.
Sai dai, wannan ba yana nufin cewa fara cin borkono mai yawa zai kare lafiyarka ba - ko kuma kare ka daga wasu cutuka - na takaitaccen lokaci.
Yana da kyau a gane cewa waɗannan masu bincike daga China sun yi bincike kan mutane ne na tsawon shekara bakwai. Don haka, ko da borkonon na kare mutum daga barazanar mutuwa ko ƙara lafiya, tasirinsa zai iya bayyana bayan wani lokac, maimakon cikin makonni ko watanni.
Sinadaran ɗanɗano
Sinadarai da ke bayar da ɗanɗano ga abinci ba su da lahani ga ɗan'adam, a cewar Duane Mellor, wani ƙwararre kan abinci kuma malami a makarantar kiwon lafiya a birnin Birmingham da ke Birtaniya.
"Yawancin sinadarai da kuma ɗanɗano da muke ci a abinci suna nan don kare cimaka daga ƙwari, kuma mun saba da su matuka."
A ɗaya gefen, ko da sinadaran ɗanɗano na da alfanun gaske, ba ma gane hakan da wuri saboda ba ma cinsa da yawa.

Asalin hoton, Getty Images
Alal misali, sinadarin polyphenols wanda ake samu cikin cuka yana kare ta daga ƙwari. Alfanun lafiya na sinadaran ɗanɗano ya samo asali ne sakamakon yawaitar polyphenols a cikinsa.
Sai dai, a 2014, wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa babu tabbaci cewa ko cin waɗannan sinadarai kaɗan na taƙaita alfanunsu ga lafiya.
Duk da cewa wasu bincike sun gano sakamako mai kyau, wani bincike da aka ƙara yi a 2022 ya ƙarƙare cewa babu takamaimen tasiri kan lafiya da cin waɗannan sinadarai ke yi - kuma hujjar da aka samu ba mai ƙarfi ba ce.
Alfanun kurkum (turmeric)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sinadarin Kurkum wato turmeric, wani ɗanɗanon abinci ne da yake da alfanu. Ana samun alfanun ne sakamakon wani ɗan sinadari da ke ciki mai suna curcumin - wanda yawanci ake amfani da shi wajen magance gajiya da wasu ciwuka.
Sai dai, babu wata hujja ƙwakkwara kan alfanun turmeric.
Alal misali, wani bincike a 2023, ya nuna cewa cin sinadarai nau'uin citta kan taimakawa mutane wajen magance wasu matsaloli na jiki.
A ƙasashen yammacin duniya, buƙatar amfani da sinadaran ɗanɗano na ƙaruwa, ciki har da turmeric, a matsayin gurbi na magani wanda aka yi amfani da shi tun da daɗewa, kamar yadda Farfesan tarihi a jami'ar Yale da ke Amurka, Paul Freeman ya bayyana.
"ana amfani da sinadaran ɗanɗano wajen ƙarawa abinci daɗi. Mutane sun yi imanin cewa abinci na zafi, sanyi, danshi da kuma bushewa, kuma ya kamata a kawo daidaito kan haka," in ji Paul Freeman. Alal misali, ana ɗaukar kifi a matsayin mai sanyi, yayin da na'ukan ɗanɗano kuma suka kasance masu zafi da kuma bushewa.
Batun amfani da abinci a matsayin magani da samar da daidaito a na'ukan abinci na da muhimmancin gaske, wanda aka shafe sama da shekaru dubu ana yi a Indiya.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wani abu mai alfanun gaske a turmeric, in ji shi. Haka kuma, idan aka haɗa sinadarin ɗanɗano na turmeric a cikin girki, ana ƙara shi zuwa ga sauran nau'ukan abinci.
"Turmeric na ɗauke da wani karamin ɗanɗano a cikinsa curcumin. Ana haɗa shi da wasu sinadarai domin samun alfanu."
Wata mai binciken mai suna Kathryn Nelson ta ƙara da cewa yawan cin turmeric ba shi da illa, sai dai ta ba da shawarar cewa a guji amfani da shi a matsayin magani.











