Yadda ya kamata ku yi tsuguno a lokacin bahaya

Ba-haya.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Lokacin amfani da banɗaki irin na zamani, ya kamata me amfani da shi ya san yadda zai zauna kan wurin da zai yi bahaya.

Wannan yana nufin cewa gwiwoyinku su kasance sun fi ƙwanƙwasonku tsawo. Wannan shi ne salon zama da ya fi dacewa yayin bahaya.

Zaune kamar mutum yana tsugune sannan bayansa yana lankwashe, zai taimaka muku yin bahaya cikin sauƙi.

Ya kamata a ɗauki iyakar mintuna goma wajen yin ba-haya. Idan ba ku ji cikinku ya ragu a lokacin ba, za ku iya sake gwadawa bayan ɗan lokaci.

Yin akasin hakan ka iya jaza wa masu tsuguno matsalar kasa bahaya.

Me ake nufi da matsala wajen yin bahaya?

Zanen ƙwarangal.

Asalin hoton, Getty Images

Abin da wahala wajen yin ba-haya ke nufi shi ne, rashin samun ba-haya cikin sauki a kowace rana.

Wannan babbar matsala ce, ko da babu wan lahani a cikin mutum.

Alamomin matsalar sun haɗa da jin zafi lokacin kashi da kuma sauya na sau nawa ake yi.

Mutane da ke fama da wannan matsalar na tsawon lokaci, na iya zarcewa zuwa kamuwa da gudawa.

Alamomi

  • Yin ba-haya ƙasa da sau uku a mako
  • Zafi da rashin sukuni lokacin bahaya
  • Yin bahaya mai tauri kuma a bushe.
  • Mutum ya riƙa jin kamar bai gama ba-haya ba
  • Ciwon ciki.

Abincin da ke taimakawa wajen yin bahaya cikin sauƙi

Idan kuna fama da matsalar rashin bahaya, ko kuma kana fuskantar wahala kafin bahaya ya fita, to sauya irin abincin da kuke ci zai iya zama mafita mai kyau.

Wahala wajen yin bahaya kan faru ne sakamakon wasu abubuwa, kamar matsala a matse-matsi, gajiya, kishirwa da kuma ɗabi'ar cin abinci maras kyau.

Mutane da dama na fuskantar wannan matsala, wanda ke faruwa sakamakon wasu dalilai da dama.

Bincike ya nuna cewa mutum ɗaya cikin bakwai na fama da wannan matsala. An fi samun ta a cikin yara, sai kuma manya.

Za a iya samun mafita kan wannan matsala ta hanyar gyara salon cin abinci.

Duk da cewa ba shi ne mafita ɗaya tilo ba ga matsalar, amma yin haka zai taimakawa jiki yadda ya dace.

Abinci mai harza

Harza da ke cikin abinci tana taka rawa wajen yin bahaya da sauki. An bayar da shawarar cin harza ko kuma dusar da ta kai giram 30 a kowace rana.

Sai dai, kashi 91 na mutane ba sa samun cin abincin da ke da datsa a kullum. Harzar da ke jikin abinci datsa na ɗauke da sinadarai da dama wanda jiki ke buƙata.

Akwai ire-irensa daba-daban, kuma alfanunsu ya bambanta.

Abincin da ke ɗauke da harza ko datsa ya kunshi burodi, shinkafa, taliya, kayan lambu da sauransu. Duka waɗannan suna da dusar da ya kamata.

Idan kana cin datsa kaɗan, to ka ƙara wadda kake ci. Yana kuma da muhimmanci a sha ruwa daidai da irin abincin da aka ci.

Abinci

Asalin hoton, Getty Images

A riƙa cin abincin da ke ɗauke da harza sosai, kamar ƴaƴan itace da ganyayyaki. Akwai buƙatar ka saka waɗannan a cikin nau'o'in abinci da kake ci a kullum.

Cin abincin nau'in kanzon alkama da shinkafa ƴar hausa mai duhu da kuma biredi na taimaka wa bahaya fita cikin sauki. Don haka yana da muhimmanci a ci su ba tare da da wuce ƙima ba.

Cin abinci mai harza da yawa kan janyo matsala wajen yin bahaya.

Maimakon haka, kanzon alkama da yoghurt da yaƴan itace na taimakawa a samu sauki wajen yin bahaya.

Baya ga waɗannan, akwai nau'in abinci da dama da ke ɗauke da sinadarin protein waɗanda suke sanya a ƙauce wa samun matsala yayin bahaya.

Shan ruwa

Shan ruwa.

Asalin hoton, Getty Images

Shan isasshen ruwa, ko kuma zama ba tare da kishirwa ba, na taimakawa wajen rage alamomin matsala wajen bahaya.

Shan kofin ruwa takwas zuwa goma a kowace rana, haɗe da kayan lemu da shayi da kuma dangin miya ɗauke da ruwa, na taimakawa wajen sanya bahaya ya yi laushi.

A rage shan barasa da kuma sinadarin caffeine. Yana da kyau a sha kofin ruwa kowane lokaci aka ci abinci.