Katsina ta ba wa ƴan banga makamai don yaƙi da ƴan bindiga

Asalin hoton, DIKKO RADDA/FACEBOOK
Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da rundunar ƴan sintiri da ta yi wa laƙabi da Community Watch Corps domin magance matsalar tsaro a sassan jihar.
Sabuwar rundunar ƴan sintiri ta jihar Katsina wadda aka ƙaddamar ranar Talata, tana da jami’ai 1,500 waɗanda za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen wanzar da tsaron, musamman a garuruwan da ake fama da harin ƴan bindiga a Katsina.
A wani sako da ya wallafa a shafinsana Facebook jim kaɗan bayan ƙaddamar da rundunar, gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya ce ‘’A yau wani muhimmin ci gaba ne a yunkurinmu na maido da zaman lafiya a jihar Katsina''
Ya ƙara da cewa ''A bisa alkawuran da na yi a lokacin yakin neman zabe, na kaddamar da hukumar inganta tsaro ta musamman ta Katsina wato "Community Watch Corps" a hukumance. Na kuma samar da Motoci masu sulke, da motocin inganta tsaro kirar Hilux, da babura duk don tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Katsina ya inganta’
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr Nasir Babangida Muazu ya shaidawa BBC cewa an bi duk wani tsaro da doka ta gindaya wajen kafa rundunar, da kuma tantance matasan da aka ɗauka aiki a matsayin jami’an ta na farko.
Ya ce ‘’An ɗakko jami’an ne daga ƙananan hukumomi takwas da matsalar tsaro ta fi addaba a jihar Katsina; da suka hadar da Batsari da Dandume da Danmusa da Faskari da Kankara da Jibia da Sabuwa da kuma Safana. Waɗannan ƙananan hukumomi dama suke makwabtaka da daji, inda ɓarayi ke shigowa’’
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kashe kimanin naira biliyn 10 a fannin bayar da horo, da samar da kayan aiki da kuma duk wani tanadin da ake buƙata don ganin aikin nasu ya cimma nasara.
Me masana ke cewa?
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya dai na ƙara ɗugunzuma al’ummar yankin al’amarin da ya tilastawa hukumomi suka fara ɗibar matasa domin yin aiki tare da jami’na tsaro wajen fatattakar ƴan bindiga.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai masana tsaro suna cewa duk da dai shirin abin yabawa ne amma akwai abin abubuwan dubawa.
Malam Kabir Adamu, wani masanin harkokin tsaro a Najeriya ya ce wannan yunƙuri na nuna cewa gwamnatin jihar Katsina ta gano giɓin da ake samu wajen tabbatar da tsaro. Ya kuma yaba da yadda gwamnatin ta fara ɗaukar matakin samar da dokar da ta kafa wannan runduna ta ƴn sintiri kafin kafa ta.
Shi ma Audu Bulama Burkati, wani masanin tsaron ne da ke zaune a Birtaniya, kuma ya ce ‘’akwai abubuwa huɗu da ya kamata a tabbatar a cikin wannan tsari da suka haɗa da bai wa jami’an sintirin makamai masu ƙarfi da za su iya tunkarar ƴan bindigar da ke addabar yankin, da koyar da su hanyoyin tattara bayanan sirri, da tsarin bin dokoki wajen kare haƙƙin bil adama, da tattara cikakken bayanan matasan da za su yi wannan aiki ta yadda a ƙarshen aikin za a iya bibiyar su da kuma samar masu aiki na dindindin, da kuma tabbatar da ganin rundunar ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro.’’
Duk da cewa akwai jihohi da dama da suka kafa rundunar sintiri a Arewacin Najeriya, jihar Katsina ce ta farko da ta bai wa jami’an rundunar bindigogi domin gudanar da aikin ta, kuma wannan zai iya zama Zakaran gwajin dafi a tsakanin jihohin yankin masu fama da ƙalubalen tsaro.











