Rawar da Rasha ke takawa a Afirka na ƙara alaƙa da yaƙin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
Kafofin yaɗa labaran Afirka na ci gaba da tattauna ayyukan da Rasha ke yi. Tattaunawar ta yawaita tsakanin 14 zuwa 15 ga watan Disamban, 2025, inda ake alaƙanta abubuwan da ke faruwa a nahiyar da yaƙin Ukraine.
Labaran da ake yaɗawa a wannan lokaci sun nuna yadda ake ɗaukar yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine.
Yayin da labaran da aka yaɗa tun da farko suna nanata tasirin da ke cikin ƙulla hulɗa, labaran da suka fi janyo hankalin jama'a tsakanin Nuwamba da Disamba su ne waɗanda suka kwatanta Afirka a matsayin wurin faɗaɗa yaƙin kansa - ta hanyar ƙungiyoyin ɗaukar sabbin mayaƙa, aika sojoji da kuma horo.
An kuma gano cewa ayyukan Rasha a Afirka ba su ta'allaka kan diflomasiyya da yarjejeniya kan tattalin arziki ba, sai dai ta hanyar rahotanni kan tsaro, aika sojoji da kuma ɗaukar ƴan Afirka domin su je yaƙi.
Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta ci gaba da janyo hankali a kafafen sada zumunta a Afirka a wannan lokaci.
Tattaunawa da masu goyon bayan Kremlin
Tattaunawa kan batun ya ƙaru a ranar 17 ga watan Disamba, sakamakon yaɗuwar da wata tattaunawa da aka yi da ɗan siyasar Ivory Coast Rolland Kuadio kan wani dandali, wanda kuma shafin Rasha mai suna Rutube ya sake yaɗa shi.
A tattaunawar, Kuadio ya yi magana sosai kan ƴancin Afirka, wanda shi ne abin da Rasha ta fi mayar da hankali a sakonninta a faɗin nahiyar. Muhimmancin tattaunawar ta sa ƙungiyar ƴan jaridar ƙasa da ƙasa yin suka kanta da kiranta a matsayin wani dandali na farfagandar Rasha.
RSF ya ce shafin yana raba kan al'umma ta hanyar yaɗa abubuwan da ke jaddada mamayar Rasha kan Ukraine da kuma murnar tsarin harkokin wajen Moscow.
Wargaza ƙungiyar Wagner
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tattaunawa kan batun Rasha ya samu gagarumar goyon baya ne a wannan lokaci bayan da rahotanni suka ce ƙasar a karon farko, ta aika dakaru zuwa ƙasashen Afirka shida.
Janyo hankalin jama'a ya zama wani sabon babi ga Moscow na yadda za ta tinkari nahiyar, yayin da take son assasa tasirin ƙarfin tsaronta bayan wargaza ƙungiyar sojojin hayar ƙasar na Wagner.
Diflomasiyya a ɓangaren tattalin arziki ya ƙara ɗaga darajar Rasha bayan da wani kamfanin zuba jari a Habasha ya sanar ranar 14 ga watan Nuwamba cewa ya saka hannu kan yarejeniya da kamfanin samar da aluminium mafi girma a Rasha, Rusal - na samar da tan 500,000 na sinadarin aluminium.
An bayyana cewa hakan wani yunkuri ne da Addis Ababa ke yi na ƙarfafa masana'antunta da kuma hujja na rawar da Rasha ke takawa a matsayin mai hulɗa kan tattalin arziki.
Haka kuma, an bayyana yadda wargaza Wagner ya saka Rasha aika wasu dakaru zuwa Mali don taimaka wa ƙasar yaƙi da masu iƙirarin jihadi. Wani rahoto da aka fitar ya nuna yadda sojojin ƙasar ke shan wahala wajen tinƙarar masu iƙirarin jihadi da suka addabi yankunan kudanci da kuma yammacin ƙasar da hare-hare, abin da ya janyo taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro.
Waɗannan gaba-ɗaya, sun nuna yadda Rasha ke sauyawa kasancewar dakarunta a Afirka yayin da take fuskantar kalubale wajen ƙarfafa tasirinta a nahiyar.










