Shin ko akwai buƙatar a bai wa Trump isasshiyar kariya?

..

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, James FitzGerald
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Donald Trump ya yaba wa jami'an tsaron sirri na Amurka bayan daƙile abin da hukumar bincike ta FBI ta ce an yi yunƙurin kashe shi.

Wani jami'in tsaron sirri ne ya hango kan bindigar wanda ake zargin ya leƙo daga cikin jeji a, inda tsohon shugaban ke shaƙatawa a gidansa na Florida, mai tazarar mita 700 daga inda yake buga ƙwallon golf - kuma kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana sunansa da Ryan Routh.

Nan da nan jami'ai suka buɗe wuta kan mutumin da ake zargi, wanda ya samu damar tserewa, sai dai daga bisani an yi nasarar kama shi.

Da yake tattaunawa da BBC, wani tsohon jami'i ya ce jami'an tsaron sirri sun yi ƙoƙari, sai dai ya yi tambayar cewa ko Trump na samun kariya da ta kamata ganin cewa watanni biyu da suka wuce ma an yi yunkurin kashe shi.

Wancan lamari ya janyo murabus ɗin darektar jami'an sirri na ƙasar.

Ta yaya jami'ai suka daƙile harin na ranar Lahadi?

Jami'an tsaron sirri ne suka hango ɗan bindigar, waɗanda ke shara a filin da Trump ke buga ƙwallon golf wanda abu ne da suka saba yi.

Daga nan suka ga kan bindiga ya leƙo daga cikin jeji. A lokacin Trump yana nisan mita 275-460 daga wajen da ɗan bindigar yake tsaye, a cewar wani jami'i a lardin Sheriff Ric Bradshaw.

Ba a dai san cewa ko ɗan bindigar ya yi harbi ba.

Nan take wani jami'in sirri ya fara artabu da shi, bayan haka ne ya tsere, in ji Sheriff. "Jami'an tsaron sirrin sun yi abin da ya kamata a yi."

Jami'an sun yi ta harbi a iska bayan gano ɗan bindigar. Ya samu tserewa, inda ya bar makamansa tare da wasu abubuwa, sai dai daga baya an kama shi a cikin motarsa bayan da wani shaida ya gabatar da hoton motarsa ga hukumomin yankin.

Ƴan sanda sun samu nasarar kama shi ne da tazarar kilomita 61 daga filin da Trump ke buga kwallon Golf, kuma kafar yaɗa labaran Amurka ta bayyana sunansa da Ryan Routh.

Trump ya faɗa wa magoya bayansa cewa yana cikin koshin lafiya, kuma ya gode wa jami'an sirrim da sauran hukumomin tsaro saboda gagarumin aiki da suka yi.

Da yake tattaunawa da wani shirin BBC, wani tsohon jami'in sirri, Robert McDonald, ya amince cewa jami'ai sun yi ƙoƙari duk da cewa mutumin da ake zargi da yunkurin kashe Trump ya yi kusa da wurin da tsohon shugaban yake.

Shin akwai buƙatar Trump ya samu isasshen kariya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Trump ba ya samun kariya irin wadda shugaba mai ci ke samu, kamar yadda Sheriff Bradshaw ya bayyana. "Idan da a ce yana samun isasshen kariya, to da za a tsare ɗaukacin wajen buga kwallon Golf ɗin nan," in ji shi.

Sai dai wasu tsofaffin jami'an tsaron sirri biyu sun ce Trump na buƙatar ƙarin kariya fiye da wasu tsoffin shugabanni, ganin cewa yana sake yin takara.

"Yanzu ya kamata mu zauna mu sake yin duba,"kamar yadda Barry Donadio ya faɗa wa BBC. "Shin ya kamata duka waɗannan ƴan takara su samu tsaro irin wadda shugaban ƙasa ke samu? Ina ganin hakan shi ya kamata."

Ƴan siyasa da dama na da irin wannan ra'ayi, kamar ɗan jam'iyyar Democrat Ritchie Torres, inda ya ce Trump na buƙatar isasshen kariya".

Sai dai wani abokin Trump ya ce wajen buga kwallon Golf na tsohon shugaban na cike da barazana. Shi ma Chris Ruddy, shugaban kafar yaɗa labarai ta Newsmax, ya ce wurin yana da girman gaske kuma yana buƙatar sojoji da ɗan yawa kafin ya samu tsaron da ya kamata.

Me ya faru a hari na farko?

An sake bijiro da tambayoyi kan buƙatar bai wa Trump isasshen kariya bayan wani yunkurin sake halaka shi a wajen yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania a farkon wannan shekara.

An harbi Trump a kunnensa ranar 13 ga watan Yuli, a wajen yaƙin neman zaɓe a Butler, da ke Pennsylvania.

Ɗan bindigar mai suna Thomas Matthew Crooks, ya kuma kashe wani mutum guda tare da jikkata wasu mutum biyu.

Harin da aka kai ya janyo ɓacin rai daga jama'a, har ta kai ga murabus ɗin darektar jami'an tsaron sirri ta Amurka Kim Cheatle. Yanzu an maye gurbinta Ronald Rowe Jr.

Shugabar sashen BBC a arewacin Amurka Sarah Smith ta ce hukumar sirrin ƙasar zai fuskanci sabbin tambayoyi. Sai dai za su kalubanci cewa ba su da isassun kayan aiki - duk da cewa suna da shi fiye da na makonni takwas da suka wuce.

Me ya faru yanzu?

Abokan Trump sun yi Alla-wadai da lamarin da ya faru, ciki har da abokiyar takararsa ta Democrat Kamala Harris.

Gwamnati za ta 'tabbatar da cewa jami'an tsaron sirri na da isassun kayan aiki, kwarewa da kuma ɗaukar matakan kariya domin gudanar da aiki yadda ya kamata," in ji Harris.

Mambobin tsaro da ke bincike kan yunkurin kashe Trump a watan Yuli sun ce sun buƙaci zama da jami'an sirrin a ranar yau.

A ɗaya gefen, hukumar bincike ta FBI da kuma jihar Florida sun sanar da cewa za su yi bincike kan lamarin.

"Ya kamata a faɗa wa mutane gaskiya kan wanda ya yi yunkurin aikata kisan da kuma yadda har ya kusa da wajen da tsohon shugaban Amurkan yake (tazarar mita 700)," in ji gwamnan Florida Ron DeSantis.

Yanzu dai an tsaurara matakan tsaron a yankin da ke kusa da wajen da Trump ɗin ke buga wasan Golf da kuma gidansa da ke yankin Mar-a-Lago.