Me ya sa Trump ke yi wa Canada da Panama da Greenland barazana?

Kalaman Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan sun harzuƙa wasu ƙasashe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kalaman Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan sun harzuƙa wasu ƙasashe
Lokacin karatu: Minti 5

'Yan makonni kafin ya koma fadar White House, Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya firgita ƙasashe da dama saboda ƙin kawar da yiwuwar amfani da ƙarfin soja wajen karɓe iko da yankin Panama Canal da kuma na Greenland da ke Denmark.

Trump ya bayyana duka yankunan a matsayin masu muhimmanci ga tattalin arzikin Amurka.

Wannan ne karon farko da Trump ya yi irin waɗannan kalamai a bainar jama'a. Ya kuma ce zai matsa wa ƙasar Canada ta haɗe da Amurka.

Panama, da Greenland, da Denmark, da Canada duka sun mayar da zazzafan martani.

Mashigar ruwa ta Panama

Bayan jagorantar gina mashigar ruwan a farkon ƙarni na 20 da kuma shekaru ana tattaunawa, Amurka ta miƙa wa Panama iko da gaɓar ruwan a 1999.

Yanzu Trump na son ya dawo da gaɓar saboda abin da ya kira tsaron ƙasar.

"Mashigar ruwan Panama na da muhimmanci ga ƙasarmu. China ce ke gudanar da ita kuma Panama muka bai wa ikonsa; ba China ba, su kuma suka wulaƙanta ta. Sun wulaƙanta kyautar," in ji Trump.

Sai dai alƙaluman gwamnati sun yi hannun riga da wannan ra'ayi na Trump. Jiragen dakon kaya na Amurka ne suka fi zirga-zirga a wurin da kashi 72 cikin 100. Jiragen China ne na biyu da kimanin kashi 22, a cewar alƙaluman hukumar Panama Canal. China ta zuba jari mai yawa a ƙasar ta Panama.

Masu sharhi na cewa amfanin mashigar ruwan bai tsaya kan tattalin arzikin Amurka ba kawai a yankin Pacific, wuri ne mai muhimmanci idan tsautsayi ya sa yaƙi ya ɓarke tsakaninta da China.

Jiragen dakon kaya na Amurka ne suka fi hada-hada da kashi 72 cikin 100 a mashigar ruwa ta Panama Canal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jiragen dakon kaya na Amurka ne suka fi hada-hada da kashi 72 cikin 100 a mashigar ruwa ta Panama Canal

A baya ma, Trump ya zargi Panama da tsawwala wa jiragen Amurka kuɗaɗen haraji da ke amfani da mashigar.

Trump ya wallafa wani hoto a shafinsa na dandalin Truth Social ana dasa tutar Amurka a tsakiyar mashigar ta Panama Canal.

Da yake magama yayin wani taron manema labarai a Panama City, Firaministan Panama Javier Martinez-Acha ya ce 'yancin mashigar ta Panama Canal ba abin tattaunawa ba ne.

"Panama ce kaɗai ke da iko da mashigar, kuma haka abin zai ci gaba," in ji shi.

Tsibirin Greenland

Greenland yanki ne mai cin gashin kansa ƙarƙashin kulawar ƙasar Denmark, kuma yana cikin yankuna mafiya ƙanƙantar al'umma a duniya.

Trump ya so ya sayi Greenland a 2019 lokacin da yake wa'adin mulkinsa na farko.

Firaministar Denmark Mette Frederiksen ta bayyana aniyarta ta yin aiki tare da shugaban na Amurka mai jiran gado amma ta jaddada 'yancin yankin na hannun mutanenta.

"Greenland na mutanen Greenland ne. Mutane ne masu alfahari da harshensu, da al'adarsu. Kuma kamar yadda muka faɗa a baya, yankin ba na sayarwa ba ne," a cewar Frederiksen.

Yankin na da arzikin ma'adaanai. Hukumar kula da ƙasa ta Denmark, Geological Survey of Denmark, ta zayyana albarkatun da tsibirin mafi girma a duniya ke da shi. Daga ciki akwai lithium, da titanium, da uranium, da coal, da duwatsu masu daraja kamar demon.

Tsibirin Greenland na da albarkatun ƙasa sosai masu muhimmanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsibirin Greenland na da albarkatun ƙasa sosai masu muhimmanci

Ana kuma tunanin akwai albarkatun mai da iskar gas, waɗanda har yanzu ba a kai ga haƙowa ba, amma kuma ana kan hanyar yin hakan saboda yadda manyan ƙwallayen ƙanƙara ke narkewa sakamakon sauyin yanayi.

Sai dai ma'adanan ƙarafan da ake amfani da su wajen ƙera batiri ne suka fi ɗaukaka tsibirin. Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa dole ne a ninka haƙo ma'adanin sau biyar nan da 2050 idan ana so kada a yi rashinsa a duniya, kuma Amurka da China na mtuƙar nemansa.

Rasha ma na kallon yankin a matsayin mai muhimmanci saboda yana tsakiyar ƙasashen biyu. Da ma Amurka na da sansani a tsibirin ɗauke da na'urar ankararwa idan aka harba makami mai linzami mai cin dogon zango.

Ƙasar Canada

Trump ya ce yana so Canada ta tsaurara tsaro a kan iyaka saboda ta hana baƙin haure da ƙwayoyi shiga Amurkar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump ya ce yana so Canada ta tsaurara tsaro a kan iyaka saboda ta hana baƙin haure da ƙwayoyi shiga Amurkar

A 'yan makonnin nan, Trump ya sha nanata batun komawar Canada a matsayin ɗaya daga cikin jihohin Amurka.

Trump ya sha sukar cewa Amurka na kashe biliyoyin dala wajen bai wa Canada kariya. Ya kuma damu game da motocin Canada da ake shigarwa ƙasar, da kayayykain abinci.

Kamar Mexico, Canada ma na fuskantar ƙarin kashi 25 cikin 100 na harajin kayayyakin da suke shigarwa Amurka a ƙarƙashin mulkin Trump.

Yayin wani taron manema labarai, Turmp ya jaddada damuwarsa kan ƙwayoyin da ya ce suna shiga Amurka daga Mexico da Canada.

Sai dai kuma, yawan ƙwayar fentanyl da ake ƙwacewa a kan iyakar Canada da Amurka ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da iyakar Amurka ta kudanci, a cewar alƙalumar hukumomin Amurkar.

Firaministan Canada Justin Trudeau ya mayar da martani da cewa ba zai taɓa yiwuwa ba ƙasashen su haɗe.

Zance ne kawai batu na gaskiya?

James Jeffrey, tsohon mataimakin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya faɗa wa BBC cewa Trump na aika saƙo ne ga ƙasashe ƙawayen Amurka da ma magoya bayansa a gida.

Jeffrey ya kawar da yiwuwar gwabza yaƙi a lamarin.

"Ba za mu afka Greenland ba, ba za mu afka wa Canada ba, ba za mu ƙwace mashigar Panama Canal ba. Amma irin hayaniyar da hakan zai tayar shi ne abin tambayar," in ji shi.

"Ba Trump ne abin tsoro ga ƙasashen duniya ba, Rasha da China ne barazanar."

Sai dai David Maddox, editan sashen siyasa na jaridar Independent da ke Landan, na ganin ya kamata a ɗauki maganar Trump da gaske.

"Wannan Trump ɗin mai nuna ƙarfin iko ne. Yana so ne ya bunƙasa tasirin Amurka a duniya. Wannan barazanar tasa mai girma ce," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

"Za mu ga bambanci sosai tsakanin mulkinsa na farko da na biyun nan, wanda zai zama mai raba kan ƙasashen duniya," in ji Maddox.