Yadda ɗan sanda ya jikkata karamin yaro bayan ya nemi taimakonsa

Iyalin wani yaro ɗan shekara 11 da wani ɗan sanda ya jikkata da bindiga bayan ya kira 'yan sanda yana neman taimako ta wayar tarho sun ce an sallame shi daga asibiti.

'Yan sandan Mississippi sun isa gidan Aderrien Murry a ranar Asabar sakamakon kiran da aka yi ta tarho, inda yaron ya nemi a kawo mu su dauki game da cin zarafin da ke faru wa a gidansu , amma sai ɗan sandan ya harbe shi a kirji, a cewar mahifiyarsa.

Ta ce yaron ya tambaye ta "me na yi?" bayan an harbe shi.

An dakatar da jami'in da ya yi wannan aika-aika daga aiki yayin da ake gudanar da bincike kan alamarin.

Rundunar 'yan sandan Indianola ta tabbatar da cewa jami'in da abin da ya shafa sunansa Greg Capers a cewar CNN.

Ofishin Bincike na Mississipi na gudanar da bincike kan alamarin.

Mahaifiyar yaron, Nakala Murry, ta bukaci a kori jami'in tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

An wuce da Aderrien zuwa wani asibiti inda ya ji rauni a hununsa da kuma wasu wurare, a cewarta.

A ranar Laraba ne aka sallame shi daga asibiti

'Yadda aka jikkata mun ɗana'

Ms Murry ta tuno da alamarin a wani taron manema labarai a ranar Litinin da ya gudana a wajan dakin taron garin Indianola.

Ta ce da sanyin safiyar Asabar ta umurci Aderrien ya kira 'yan sanda saboda ta damu da dabi'ar mahaifin ɗaya daga cikin 'yayanta, wanda ya zo gidan a "fusace".

Daga bisani Ms Murry ta fadawa CNN cewa a lokacin da jami'in ɗan sandan ya iso gidansu "ya rike bindigarsa a gaban kofar shiga cikin gidan".

Sannan ya bukaci duk wadanda suke ciki su fita.

Yayin da ɗanta ya juya kusurwar falon, sai jami'in ya bude wuta, inda ya same Aderrien a kirji, in ji ta.

Abin da ya ce bayan da aka harɓe shi shine:‘ Me ya sa ya harbe ni? Me na yi? Sai ya fara kuka," Ms Murry ta ce "Wannan ba zai iya ci gaba da faruwa ba. Wannan ba dai-dai bane".

Ta ce ta rufe raunin ɗanta da hannunta kuma jini ya taru a karkashin tafin hannunta Jami'in ya kuma taimaka mata wajen bayar da agaji har zuwa lokacin da ma'aikatan jinya suka iso in ji ta.

An wuce da Aderrien zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Mississipi inda aka saka masa naurar shakar iska.

Harbin ya kuma raunata masa huhu da hanta da karaya a hakarkarinsa .

Ms Murry da lauyanta, Carlos Moore, sun yi kira ga jami'ai da su kara daukar mataki.

Mista Moore ya ce an tilasta wa jami'in ɗan sanda zuwa hutun dole.

Mista Moore ya bukaci a ba su hoton bidiyon da kamarorin tsaro suka dauka, amma ya ce 'yan sanda sun ƙi amincewa da bukatarsa saboda binciken da ake yi.

Rundunar 'yan sanda Indianola ta shaidawa BBC cewa a yanzu ba za ta ce komai ba akan alamarin ba.

Ofishin bincike na Mississippi ya fitar da wata sanarwa a karshen makon inda ya ce hukumar a "halin yanzu na nazari kan alamarin tare da tattara shaida".

Kuma zai miƙa sakamakon binciken ga offishin babban lauyan gwamnati bayan an kammala binciken.