Indonesia ta amince da dokar tsaurara hukunci kan masu zina da aure

Ƴan majalisa a Indonesia sun amince da sabuwar dokar da ta haramta zina da aure, inda yanzu hakan ya zamo babban laifi, da kuma taƙaita 'yancin siyasa.

A ƙarƙashin sabuwar dokar laifi ne yin zina da aure, inda za a iya yanke wa mutum hukuncin sama da shekara, kuma an haramta zaman daduro kafin aure.

Bijiro da wannan doka ya biyo bayan karuwar kishin addini a ƙasar da Musulunci ya fi rinjaye.

Masu suka na ganin dokar a matsayin "babban bala'i" ga ƴancin bil adama, kuma babbar barazana ga masu zuwa yawon bude ido da zuba jari a ƙasar.

Kungiyoyi da dama galibi na matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wannan doka a wajen ginin majalisa da ke Jakarta a wannan makon. Ana tunanin za su kalubalanci sabuwar dokar a kotu.

Wannan doka ta shafi 'yan kasa da baƙi da ke zuwa ƙasar don zama ko hutu a wuraren shaƙatawa irinsu Bali.

A karkashin dokar duk mutanen da aka kama suna zina da aure za a yanke musu hukunci ɗaurin shekara guda.

An kuma haramta musu zama tare – laifin da idan aka samu mutum da aikatawa zai sha ɗauri na kusan wata shida. Sannan zina ga ma'aurata zai kasance babban laifin da za a fuskanci ɗauri.

Magoya bayan dokar a majalisa sun ce ana aiwatar da sauye-sauye domin duba korafin masu suka – kafin a gabatar da mutum dole sai idan korafin da aka shigar daga wajen yaransa ne, iyaye ko kuma mata ko mijin waɗanda ake zargi.

Ajeng, wata mata ce Musulma da ke rayuwa a yankin Depok da ke birnin Java a yamacin kasar, ta ce a yanzu tana fuskantar barazanar zama da iyayenta tsawon shekara biyar.

"Ta ce da wannan sabuwar dokar, dukkaninmu na iya shan dauri idan ɗaya daga cikin iyayenta suka shigar da kara ga 'yan sanda, kamar yada ta shaidawa BBC.

"To ya kenan idan wani daga cikin 'yan uwana suna da matsala da ni suka kuma yanke hukuncin kai ni gidan yari?

"Ina ganin zama tare ko jima'i kafin aure ba laifi ba ne. A addinina, hakan babban laifi ne. Amma ba na ganin dacewar dokar, domin aiki za ta yi a kan wani addini guda."

Ta ce ta shiga zanga-zangar gama gari a 2019 lokaci da aka soma bijiro da dokar.

Na rataɓa hannu a takardar adawa da "bai wa mutane damar ruguma, Na gudanar da gangami."

Sai dai a ranar Talata, majalisa ta amince da sabuwar dokar da bayananta ke ƙunshe cikin maƙala mai shafi sama da 600.

Kungiyoyin kare hakki sun ce sabuwar dokar zai yi tasiri kai-tsaye ne ga mata da masu maɗigo da luwaɗi da kabilu tsiraru.

'Yan kasuwa da dama su ma na adawa da wannan doka, suna masu cewa zai hana baƙi shigowa ƙasar da zuba jari. Sai dai 'yan majalisa sun yi watsi da dokar da ƙasar ta jima ta na amfani da shi tun zamanin turawan mulkin mallaka.

"Lokaci ne a gare mu na yanke shawarar da zata kafa tarihi da yi wa kudin tsarinmu kwaskwarima da watsi da kundin turawa da muka gada," kamar yadda Minista Yasonna Laoly ya shaida wa zauren majalisa.

Sabuwar dokar ta kunshe abubuwa da dama da suka shafi hukunta rashin da'a da tarbiyya da saɓo da takaita wasu ayyuka na 'yan siyasa da ra'ayi addinai.

Darakta a hukumar kare hakkin bil adama yankin Asiya, Elaine Pearson ta shaida wa BBC cewa babban koma baya ne ga ƙasar da ta jima tana bayyana kanta a matsayin mai kare 'yanci da mutunta Musulunci."

Jami'in bincike na hukumar a Jakarta, Andreas Harsano, ya ce akwai miliyoyin ma'aurata a Indonesiya da ba su da shaidar aure na satifikate "musamman ainihin 'yan kasa ko Musulmi a yankunan karkara" da suka yi aure bisa tsarin addinai daban-daban.

"Wadannan mutane za su karya wannan doka tunda zama tare zai zama laifin ɗauri na kusan watanni shida, kamar yada ya shaidawa BBC.

Ya kara da cewa binciken da suka aiwatar a ƙasashen yankin Gulf, inda ake da irin wannan doka kan jima'a da mu'amala, ya nuna cewa mata ake hukuntawa da kai wa hari da irin waɗannan dokoki, sama da maza.

Akwai dokoki da suka haramta laifuka saɓo da aka kasafta gida shida, ciki har da sauya addini. A karon farko tun bayan samun 'yanci, Indonesiya za ta haramta tursasawa mutum sauya addini.

Sannan sabuwar dokar ta haramta zargin shugaban kasa ko sukar wata manufa ta gwamnati.

Sai dai 'yan majalisa sun ce kwai kariya kan 'yanci fadin albarkacin baki da nuna adawa a madadin sauran al'umma.