2022 World Cup: Kasashen Afrika za su tsallaka wasan kusa da na karshe a Qatar

Daya daga cikin kasashen Afrika a wannan karon za ta je wasan kusa da daf da na karshe, matukar kasashen za su baiwa masu horaswar da suka fito daga nahiyar damar jan ragamar su, in ji Pitso Mosimane.

A karon farko tun lokacin da aka fara gasar cin kofin duniya a 1930, duka kasashen Afrika za su halarci gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar da masu horarwa na cikin gida.

Baiwa Walid Regragui ragamar kasar Morocco a watan jiya, don maye gurbin Vahid Halilhodzic na nufin duka kasashe biyar din da za su gasar, za su kasance karkshin koyarwar kociyoyin gida ne.

Tsohon kocin Wydad Casablanca Jalel Kadri da tsohon kocin Otto Addo ta Ghana da Aliou Cisse (Senegal) sai kuma Rigobert Song (Cameroon) suna ta kara shirye-shiryen tun karar World Cup ta hanyar buga wasannin sada zumunta.

"Yarda da kocin gida ba karamin abu ba ne, hakan na nuna girma da kuma ci gaban da ake samu a fannin kwallon kafar Afrika, dole hakan kuma ya dore," Mosimane ya shaida wa BBC Sports.

"Ba wai ina nuna kar a rika daukar na waje ba ne, aa ni godiya nake wa hukumar kwallon kafar nahiyarmu da suka dauki wannan mataki.

"Da yawan mutane na tambaya me yasanya kasashen Afrika ba sa tsallake zagayen 'yan takwas a gasar cin kofin duniya, na yi imanin wannan ne lokacin an dauki kuma hanya.

"A wannan karon dole ne sai kasashen Afrika sun tsallake wannan katanga, kuma dole mu bai wa kociyoyinmu duk wata dama domin suna da kyakkyawar fahimtar yadda muke gudanar da lamuranmu."