Ba'amurkiyar da ta je Saudiyya doka ta rutsa da ita

Ba'amurkiya Carly Morris sanye da nikabi

Asalin hoton, CARLY MORRIS

Bayanan hoto, Shekara uku Carly Morris na fafutukar mayar da 'yarta Amurka abin ya gagara

Iyaye mata daga Amurka da Kanada da Birtaniya da kuma wasu kasashen yammacin duniya na fafutukar ceto ‘ya’yansu mata da suka auri ‘yan Saudiyya kuma suke zaune a kasar ta Larabawa bayan auren ya mutu.

Wata mai fafutuka ta ce irin wadannan iyaye mata ba sa samun taimako da goyon bayan da suke bukata daga gwamnatocin kasashensu.

Da farko abu dai ya fara lami lafiya ba wata alamar matsala ko fargaba lokacin da Ba’amurkiya Carly Morris ta sauka a Saudiyya tare da ‘yarta mai shekara biyar, Tala.

Ta je kasar ne bisa gayyatar tsohon mijinta dan Saudiyya wanda ta aura lokacin da ya je Amurka karatu tsawon shekara bakwai, inda suka haifi ‘yar tasu.

Tsohon mijin nata ya gayyace su ne domin su kawo ziyara ta dan lokaci wadda ta haka iyayensa za su ga jikarsu a karon farko.

Abu na farko da aka fara da shi shi ne cewa dakin otal din da tsohon mijin nata ya kama mata da ‘yar, daki ne da ba shi da taga da intanet kuma waya ba ta yi a ciki.

Ta ce, ‘’bayan mako daya da zuwanmu sai ya tambayi fasfodina da takardar haihuwata domin ya fara shirin neman takardun fita da Tala idan mun tashi komawa.

To amma daga baya na gane cewa ya mayar da ‘yar tamu ce ‘yar Saudiyya,’’ in ji ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A kasar Saudiyya mutum ba ya zama dan kasa biyu don haka ne ya yi wannan, saboda haka daga nan Tala wadda aka Haifa ta kuma tashi a Amurka, ta zama ‘yar kasar Saudiyya ne kawai.

Wannan na nufin bisa tsarin muharrami na Saudiyya mahaifinta ne kadai yake da ikon bayar da damar barinta Saudiyya.

Kuma ta bayyana cewa shi kam ba zai taba barin ‘yar tasu ta fita daga Saudiyya ba.

Carly ta ce daga nan ne kuma sai ya fara zuwa yana daukar Tala daga wurinta tun da safe ba zai dawo da ita ba sai da daddare.

Tana kasancewa ita kadai a wannan daki na otal, ba tare da wani kudi mai yawa ba, ko abinci ma ta dogara ne ga wanda yake kawo mata.

A karshe dai bayan kusan shekara biyu tana ta rokonsa a kan ya bar ta ta koma da ‘yar, hakan ba ta samu ba, sai ta fara rubuta wasika ga ‘yan majalisar dokokin Amurka da sauran wasu da take fatan za su taimake ta.

Ta ce wannan mataki da ta dauka ya bata wa tsohon mijin nata rai.

Daga nan ma sai kamar yadda ta ce, ya sace ‘yar tsawon wata biyu, inda shi da iyayensa da sauran mutanen gidansu suka guda daga inda suke.

‘’A wannan lokaci sai ya shigar da kara ta neman hukuma ta ba shi damar rike ‘yar.

A takardar neman sai ya musanta zargin cewa ya sace Tala, a cewar Carly.

Bayan da ta kasa samun wata amsa mai karfafa guiwa daga ‘yan siyasar na Amurka sai ta karkata ga Fadar Gwamnatin kasar ta White House, domin neman taimako.

Inda nan ma dai ba wata nasara. Hatta lokacin da Shugaba Biden ya kai ziayara Riyadh a watan Yuli, abin da take nema bai tabbata ba, duk kuwa da yadda ta hada da rokon jami’an ofishin jakadancin Amurka a Riyadh.

Can kuma a Amurka mahaifiyar Carly wadda take kara damuwa a kan halin da ‘yar tata da jikar suke ciki, ta fahimci cewa muhimmancin Saudiyya ta fannin tattalin arziki da siyasa na nufin jami’an diflomasiyyar Amurka ba za su mayar da hankali kan lamarin ba sosai.

Saudiyya daya ce daga manyan kasashe masu samar da mai a duniya, wanda hakan yake ba ta iko da tasiri a siyasa, musamman a wannan lokacin na matsalar makamashi a duniya.

Da take magana daga gidanta a California, Mrs White ta ce ta damu matuka a kan rashin samun ilimi na jikarta, bayan da aka fada mata cewa Tala ba ta je makaranta ko da sau daya ba a cikin shekara uku.

Ita ma kuma Carly ta nuna fargabarta kan abin da zai samu ‘yar tasu a kan wannan dambarwa, ta wanda zai rike ta, a kasar da ta ce tana nesa da gidanta.

Ta ce, ‘’ba ta yarda ba ta yi wa kowa magana idan jami’an kula da jin dadin jama'a suka zo nan.

Ba ta yi wa baki magana. Idan zan yi hoton bidiyo don aika wa iyayena sai ta boye ba ta son ta fito a hoton.

Gaskiya yanayin zamantakewa da mu’amullarta sun dame ni a yanzu,’’ in ji Carly.

Mai fafutuka Bethany Alhaidari da yarinya

Asalin hoton, BETHANY ALHAIDARI

Bayanan hoto, Mai fafutuka Bethany Alhaidari, ta ce akwai iyaye mata da yawa da ke cikin irin halin Carly

Kididdiga da kungiyar kare hakkin dan-Adam da ke Amurka, Human Rights Foundation, ta yi ta nuna cewa Carly daya ce daga cikin iyaye mata Amurkawa kusan 50 da ke yakin fito da ‘ya’yansu daga Saudiyya bayan sun auri ‘yan kasar ta Saudiyya.

Bayan wannan akwai wasu matan ‘yan kasashen Birtaniya da Kanada da sauran kasashen Yamma da ke cikin irin wannan hali.

Bethany Alhaidari, ta wannan kungiya wadda ta ce ita kanta ta shafe shekara biyu tana fafutukar samun damar fitar da ‘yarta daga Saudiyya, ta ce ba wata da ta samu nasara a shekara daya da ta wuce.

Ta ce da dama daga cikin irin wadannan iyaye mata ‘yan kasashen waje ba sa samun taimakon da suke bukata daga gwamnatocinsu.

Ofishin jakadancin Amurka a Riyadh ya gaya wa BBC cewa ba abin da ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta fi bai wa fifiko kamar jin dadin ‘yan kasar.

Kuma ofishin yana magana da Carly a kai-a kai da kuma gwamnatin Saudiyya.

A karshe dai bayan doguwar dambarwar shari’a Carly ta yi nasarar samun ikon karbar Tala, amma kuma kotun ta ce kada ta sake ta bar birnin da take zaune a Saudiyyar, ba ma kasar ba.

Yadda take a yanzu ba tare da wasu isassun kudi na kanta ba, Carly ta ce ta zama ‘yar fursuna a cikin dakinta.

Ta ce, "A wannan lokaci na yi shekara biyu ba tare da na fita ko waje ba. Ina zaune a otal din nan kowa ce rana.

Ba ko mutum daya da ya ga fuskata… ko mutum daya ba wanda ya kwankwasa kofata."

Bethany Alhaidari da 'yarta

Asalin hoton, BETHANY ALHAIDARI

Bayanan hoto, Bethany Alhaidari ta ce shekara biyu ta shafe kafin ta iya karbo 'yarta

Tun bayan da ta fito fili ta yi magana a kan wannan dambarwa, hukumomin Saudiyya sun zargi Carly da laifin tayar da husuma, inda masu gabatar da kara ke neman a yanke mata hukuncin zaman gidan yari.

Bayan wannan tana kuma wata tsaka-mai-wuya ta daban a yanzu.

Tun kafin haduwa da tsohon mijin nata daman Carly ta Musulunta, inda ta ce tun bayan nan imaninta bai ragu ba.

To amma bayan ‘yan kwanaki da nasarar karbo ‘yar tata, sai mahaifin tsohon mijin nata ya zarge ta da barin Musulunci da kuma muzanta Saudiyya da dukkanin Musulmai.

Duk da rasa damar komawa da ‘yar tata gida, Amurka, yanzu kuma tana fuskantar yuwuwar hukuncin kisa, amma dai ta dora galibin laifin a kanta.

Ta ce, ‘’Daman an gargade ni. Mutane da yawa kusan sun ce min kada ki shiga wannan kasar. Idan kika shiga ba za ki taba dawowa da ‘yarki ba. Na ki sauraren gargadin… yanzu ga halin da na samu kaina a ciki bayan shekara uku.’’

An nemi jin ta bakin tsohon mijin Carly da hukumomin Saudiyya, kan lamarin amma zuwa lokacin rubuta wannan labari ba su yi magana ba.