Ƙoƙarin mayar da mata da yaran da suka yi rayuwa da IS zuwa ƙasashensu

IS
Bayanan hoto, Shukur Shermatov na koyar da matan da aka mayar gida waɗanda ake zargi IS ta ɗauka aiki
    • Marubuci, Daga Eleanora Kulenbekova da Daniel Wittenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, Kyrgyzstan

"Barka da dawowa Kyrgyzstan," in ji Shukur Shermatov, yayin da yake jawabi ga mata 20 a wani aji. Yana sanye da wata hula ta gargajiya, sai dai babu wani abu na gargajiya dangane da makarantar. Tana a tsakiyar wani shingen jami'an soji kuma ɗaliban mata ne waɗanda aka mayar gida daga sansanoni a Syria, inda suka yi rayuwa da ƙungiyar IS.

Cibiyar sake sauya musu tunani na cikin duwatsu ne a arewacin Kyrgyzstan, kuma wuri ne da mata da yara waɗanda ake zargi IS ta ɗauka suka shafe makonni shidan farko bayan dawo da su gida.

Tawagar BBC na cikin waɗanda suka fara kai ziyara wurin, kuma kamar mazauna wurin, cibiyar leƙen asirin yankin na kallon dukkan abin da muka faɗa ko yi.

Matan sun ƙasa kunne domin sauraron Shukur yayin da yake koya musu darasi na farko. Darasin ya kunshi zamantakewa, ka'idojin addini, da kuma kaucewa yin fushi.

Akwai fostoci da aka liƙa waɗanda ke bayani kan yadda mutum zai danne zuciyarsa.

Da kuma shirin ilimi, iyalai sun samu kulawa na lafiya, taimako na kwantar da hankali, da kuma - karon farko cikin shekara da yawa - samar da isasshen abinci, ruwa da kuma matsuguni.

Wasu ƙasashe sun ki mayar da irin waɗannan mata - matan da suka ce sun bi mazajensu, mahaifansu da kuma ƴan uwansu zuwa fagen yaƙi ba tare da sani ba.

Shugabanni sun ɓoye abin da ya faru da su a can - abin da suka yi, da kuma abin da suka sani. Jami'ai ne za su tabbatar da cewa ko su ne aka yi wa laifi ko kuma su suka aikata laifi yanzu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu, gwamnatin Kyrgyz ta yanke shawarar kwatanta su da IS - amma da taka tsantsan. Ana binciken tara cikin goma a cikinsu.

Bayan darasin, an kai mu cikin wani ɗaki mai gado huɗu, inda muka samu wata mata sanye da hijabi ruwan shanshambale. Muna kiranta da Fatima, wanda ba shi ne asalin sunanta ba, saboda tsaro. Ta wani karamin taga, mutum na iya ganin wurin wanda ke gefen wani tafki, da kuma ba shi da bambanci da sansanin da ta baro a Syria.

"Abu mafi muhimmanci a nan shi ne akwai kwanciyar hankali a wurin. Kowa na cikin farin ciki da hakan. Yaran suna so wurin," in ji ta.

Fatima ta bi mijinta zuwa Turkiyya a 2013 lokacin ya ce yana son aiki a can. Dukka iyalan sun tafi can, ciki har da Fatima da ƴaƴanta biyu, ƴarta da kuma jikarta. Ta ce ta gano cewa suna Siriya ne lokacin da ta ji ƙarar jirage a sama da kuma ganin jami'an IS.

Mun tambayi cewa ko ba ta san inda za su je ba, kamar sauran matan da muka haɗu da su, ta hakikance cewa ba ta matsaniya kuma ba wani aibu bane mata ta bi mijinta.

Kwanaki bayan isarsu Siriya, ta rasa mijinta da kuma ɗanta. Mijinta ya ƙone ƙurmus bayan da bam ya shafi motarsa, yayin da wani gwanin harbin laɓe ya harbe ɗanta. Jim kaɗan bayan haka, ɗaya yaronta ya kwanta rashin lafiya kuma nan take ya mutu.

Fatima
Bayanan hoto, Fatima is one of 110 women brought back from Syria in 2023 as part of Kyrgyzstan's rehabilitation programme

Matan waɗanda suka ƙasa barin wurin, sun shafe kusan shekara shida karkashin bakin mulkin IS a Iraqi da Siriya, inda ƴar Fatima ta samu ƴaƴa da yawa. Lokacin da aka fitar da mayakan IS, Fatima, ƴarta, da kuma jikokinta huɗu sun kare a al-Hol, wani sansani mafi girma da ake tsare waɗanda ake zargi mayakan IS da iyalansu. Sun shafe shekara huɗu a can, cikin tsananin buƙatar komawa gida.

"Mata na cikin rashin lafiya, yara kuma na kuka akoyaushe. Muna rokonsu da su bar mu mu tafi," in ji ta. "Mun rayu cikin wahala. Lokacin da mutane daga Kyrgyzstan suka zo don karɓar ƙungiyar mutane ta farko, kowa na cikin kaɗuwa."

A watan Okotoba, an faɗa wa ƴarta da kuma jikokinta cewa za a mayar da su gida, amma ban da Fatima.

"Na yi kuka lokacin da suka faɗa min cewa ban da ni. Me ya sa bana ciki? Ni ce mahaifiyarsu!" in ji ta. "Amma yanzu da nake nan kuma nan ba da jimawa ba zan haɗu da iyalaina, ina cikin farin ciki. Ina farin ciki jikokina za su samu ilimi. Ina son su karanta kimiyya, domin su gane duniya yadda ya kamata."

Fatima, mai shekara 57, ta kasance wadda ta fi yawan shekaru a cibiyar ta sauya tunani, tana ɗaya daga cikin mata 110 da yara 229 a Kyrgyzstan waɗanda aka mayar gida daga Siriya a 2023 a cikin wani ɓangare na shirin mayar da ƴan ƙasashen waje gida. Iraqi ce ƙasar da ta fi kowacce mayar da mutane gida a bara.

Kyrgyzstan ta shirya mayar da wasu mata 260 da yara gida, bayan shekaru da ƴan uwan waɗanda suka maƙale a Siriya suka ɗauka suna kamfe don ganin sun koma gida.

Ana binciken waɗanda aka mayar gida, kuma suna karkashin sa ido bayan kammala kwasa-kwasai kan sake sauya musu tunani.

Bayan da Elmira, wadda aka sauya wa tunani kuma a yanzu ke sake gina rayuwarta a cikin wani gari da ke wajen Bishkek, babban birnin ƙasar ta Kyrgyzstan ta amince ta tattauna da mu, mun samu haske kan yadda irin saka idon yake.

Jim kaɗan bayan mun shirya ganinta, mun samu kiran waya daga wata mai yi mata aiki, inda take shaida mana cewa ita ma za ta wurin tattaunawar. Lokacin da muka isa, wasu ƴan sanda biyu, waɗanda iyalan suka gane, su ma suna can. Bayan tattaunawa, sun amince su jira a waje.

Kyrgysztan
Bayanan hoto, Yanayin shimfiɗar ƙasar Kyrgyzstan mai yawan ƙanƙara ya sha bamban da sansanonin Siriya, inda mata da dama ke zaune

Elmira ta yi iƙirarin cewa wani mutum da ta haɗu da shi a kafofin sada zumunta ne ya yaudare ta zuwa Siriya. Ya janyo hankalinta cewa ta same shi a Turkiyya, inda ta yi tsammanin cewa za su ji daɗi tare a can, kwana huɗu bayan murnar cikarta shekara 18 da haihuwa ta tafi domin haɗu wa da shi.

Amma bayan isarta can, wani mutum na daban ne ta gani wanda ya ce shi abokin wanda take magana da shi ne, inda ya ɗauketa suka yi tafiyar kusan sa'a 17 a faɗin iyaka da Siriya. Ta ce lokacin da ta gane abin da yake faruwa, lokaci ya kure mata na juya wa baya.

Ta yi aure har sau biyu. Mijinta na farko ya mutu bayan wasu watanni, sannan ta sake auren wani mutum daga Dagetan da haifar yaro guda ɗaya. Ba ta faɗi ƙarin wani abu da ke faruwa a Siriya ba sai dai ta ce suna duba hanyar mafita kafin ya mutu a wani harin roka.

Elmira ta ce lokaci mawuyaci da ta fuskanta shi ne lokacin da ta yi tunanin cewa ƴarta ta mutu. Ta fita waje, tare da barinta a gida, lokacin da wani harin roka ya faɗa wa makwabtansu. Elmira ta tsorata inda ta ruga gida cikin hawaye.

"Kwatsam sai wani fito da ita a raye, cikin koshin lafiya, amma cikin firgici. Harin rokar ya shafi gidajen mawakbta har ta kai ga mutuwar wasu yara."

Kamar Fatima, Elmira da ƴarta sun kare a sansanin al-Hol.

"Ban san yadda muka samu kan mu a sansanin ba. Wasu lokutan ina tashi cikin dare kuma ban san cewa ko mafarki nake yi ba," ta faɗa mana. "Ina godiya ga dukkan wanda ya taimaka mana fita daga can kuma ba su watsar da mu ba. Mun san cewa ba kowace ƙasa ce za ta yi haka ba."

Elmira, wadda a yanzu ke ɗinka tufafi, ta buƙaci kada mu bayyana sunanta na asali. Bayan ganin martanin wasu kan mutanen da aka mayar gida daga Kyrgyz a kafafen sada zumunta, ta yanke shawarar kin faɗa wa kowaye abin da ta fuskanta a baya.

"Me ya sa zan faɗa wa mutane, bayan ni kaina ina son manta komai?" Elmira ta ƙara da cewa. "Ina da shekara 18 a lokacin. Yanzu shekarata 27. Na koyi cewa kada in zama irin wata bagidajiya haka."

IS Families

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Da yawan iyalan mayaƙan IS na ƙasashen waje, waɗanda rikici ya raba da muhallansu, ana riƙe da su a sansanin al-Hol na Siriya

Mahaifiyar Elmira, Hamida Yusupova, ta shafe tsawon shekara goma da ta wuce tana roƙon hukumomin Kirgistan su dawo mata da 'yarta da jikarta, har ma ta kafa wata ƙungiyar fafutuka ga iyayen 'yan matan da su

"Mun san cewa Siriya na iya kasancewa tafiyar da ba dawowa. Za ka fara fahimtar cewa mai yiwuwa ne ɗanka ba zai taɓa dawowa gida ba," in ji ta.

"Ina gode wa Allah, da ya dawo min da ita gida kuma a ƙarshe, na yi ido biyu da jikata. Sai dai Elmira ta rasa shekara tara na ƙuruciyarta. Wannan lokaci ne mai tsawo."

Lokacin da Hamida ta je don karɓar su daga cibiyar da aka tsugunnar da su, kuka da hawayen da sharɓa sun fi kalamansu yawa bayan sun yi sake haɗa fuskoki.

"Elmira ta zama uwa. Ta fahimci wahalar da ake sha wajen tarbiyyar yaro har ya kai shekara 18, amma kwatsam rana ɗaya, sai ya faɗa maka cewa zai 'tafi wurin aiki', ya rufe ƙofa, ya ɓata ɓat sai ƙasar Siriya. Ba zan yi fatan haka a kan kowacce irin uwa ba," Hamida ta ce.

"Abin da kawai Elmira take iya faɗa shi ne: 'Mama, ki gafarce ni, ki yi min afuwa.' Babu wani abu. Daga nan, sai ta fara faɗa mini yadda ta ga duk na tsufa!"

Elmira da Hamida sun kwan da sanin cewa ba kowa ba ne a kewaye da su, zai iya yafiya.

Kamar sauran maƙwabtanta ƙasashen tsakiyar Asiya, Kyrgyzstan - inda kashi 90 na al'ummar ƙasar ke amsa sunan Musulmai - ta kasance wata babbar kafa ta ɗaukar mayaƙa ga IS, ƙungiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, lokacin da take kan ganiyarta.

Hamida na jin cewa 'yarta maza ne kawa masu iya hure kunne suka ingiza ta, kuma idan tana da wani laifi, to bai wuce na sakarcin da ta nuna wajen biye musu ba. Sai dai mun yi magana da wasu Matan Kirgistan masu shekaru irin na Elmira da suka ce suna cikin ɗar-ɗar saboda waɗanda suka dawo ɗin suna iya kangaras da wasu, musamman bayan sun ga yadda Taliban ta sake ƙwace Afghanistan.

"A matsayina na mahaifiya, na sha ruwan zagi da habaici. Ba na son 'yata ta ji irin abin da na ji. Ba na son mutane su dinga nuna 'yata da yatsa, suna cewa ga 'yar ta'adda nan," in ji Hamida.

Hamida
Bayanan hoto, Hamida Yusupova ta kafa ƙungiyar fafutuka ga iyayen da 'ya'yansu mata suka je Siriya

Mataimakin Firaministan, Edil Baisalov yana da sha'awar nuna manufofin mayar da ƴan ƙasashen waje gida na gwamnati a matsayin hujjar cewa Kyrgyzstan ƙasa ce mai dimokuraɗiyyada ke kula da dukkan 'yan ƙasarta.

"Na yi imanin cewa abu mafi kyau shi ne su manta da irin wahalhalun da suka shiga, kuma babu wani a cikin iyalansu da kuma al'ummarsu da ke tunawa da wannan halin da ake ciki. Cewa kowaye ɗan ƙasa ne na kwarai," ya faɗa mana.

Mista Baisalov ya san cewa wannan batu ne mai tada hankali, musamman a wasu ƙasashen yammacin duniya. Tsohuwar jakadiyar a ƙasar Birtaniya, Shamima Begum, ɗaya daga cikin 'yan matan makarantar London uku da suka bar ƙungiyar IS ta rasa damarta na zama 'yar Birtaniya.

Mataimakin firaministan ya kuma so aike da sakon siyasa. Ƙungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna shakku kan martabar Kyrgyzstan a matsayin tsibiri na dimokuradiyya a tsakiyar Asiya, tun bayan zaɓukan shekarar 2020 da ake takaddama a kai da kuma ɓullo da sabbin dokoki.

"Ga Kyrgyzstan, wannan ba abu ne mai sauƙi ba," in ji shi. "Tabbas irin Musuluncinmu ba mai tsattsauran ra'ayi ba ne, Musulunci ne mai juriya, mai girmama sauran addinai, mu al'umma ce karama da ke buƙatar kula da juna, har ma da masu yin kuskure."

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) da Sylvi Hill, waɗanda ke jagorantar yunkurin mayar da su gida daga Kyrgyzstan, sun bayyana shirin a matsayin abin a yaba. Ta ce Unicef tana kira ga "dukkan gwamnatoci da su sauƙaƙe komawa, gyara da kuma mayar da 'ya'yansu da rikici ya shafa".

Matan da muka tattauna da su sun ce sun yi godiya da aka ba su wannan dama ta biyu, kuma suna sane da cewa akwai wasu kusan 50,000 daga sassa daban-daban na duniya da har yanzu suke maƙale a sansanoni a arewacin Siriya, ba tare da wata mafita ba.