Yadda bankin raya Najeriya ke nuna wa Arewacin kasar wariya wajen bayar da rancen kudade - Ndume

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike a kan zargin cewa Bankin Raya Kasa, wato Nigeria Development Bank yana nuna wariya ga arewacin kasar wajen ba da rancen bunƙasa ƙanana da manyan masana`antu.

A muhawarar da ta gudanar kan batun ranar Laraba, Majalisar ta kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.

Dan majalisar dattawan kasar daga jihar Borno, Sanata Mohammed Ali Ndume ne ya gabatar da ƙudurin, wanda kuma ya ce daga cikin kusan naira miliyan dubu ɗari biyar da bankin ya raba, kashi goma sha ɗaya kacal ya bai wa jihohin arewa.

A cewarsa jihar Legas kaɗai ta samu kashi arba`in da bakwai cikin ɗari na rancen.

Dan majalisar dattawan ya shaida wa BBC cewa hakan ba karamin rashin adalci ba ne idan aka yi la'akari da dimbin talaucin da arewacin Najeriya yake fama da shi.

"Wannan ba zargi ba ne; akwai bankin da ake kira Nigeria Development Bank of Nigeria wanda aka kirkiro domin ya bayar da tallafi ga kanana da matsakaita da manyan masana'antu domin su farfado da tattalin arziki.

"Binciken da na yi ya nuna cewa a kashi 47 bisa 100 na kudin da ya raba - kusan rabin tiriliyan, wato biliyan dari hudu da tamanin da uku, sun bayar da shi ne ga mutane da masana'antu a Legas," in ji Sanata Ndume.

Ya kara da cewa kashi daya cikin dari kacal aka bai wa yankin arewa maso gabas, wato naira biliyan hudu da miliyan dari takwas.

Sanata Ndume ya ce "sa'annan jihohi 19 na arewa sun samu kashi 11 ne cikin dari, wato biliyan hamsin da hudu. Ka ga akwai rashin adalci a ciki. Idan ana magana a game da farfado da tatalin arziki, ya kamata a saka kudi a inda ya fi talauci, kuma kowa ya san a arewa aka fi talauci."

Za a hukunta masu laifi

Dan majalisar dattawan ya dora alhakin wannan matsala kan masu ruwa da tsaki da suka hada da bankin na raya kasa da 'yan majalisar dokoki na tarayya da kuma gwamnatin tarayya.

"Dama idan ka duba wadannan bakuna, gwamnati za ta bayar da kudi makudan kudi [don a bayar da rance], amma aiwatarwa sai ya zama matsala. Kuma 'yan majalisar kamar mu da ya kamata mu sa ido da kuma gwamnatin da ta sa su aikin su sa ido a kai, ba a yi," a cewar Sanata Ndume.

Ya ce yana cikin 'yan kwamitin da za su gudanar da bincike a kan batun kuma idan sun gama za su gabatar wa majalisa, yana mai cewa za a hukunta duk wanda aka samu da lafi.

Ya kara da cewa idan ana so a zauna lafiya ya kamata a mayar da hankali wajen ceto yankin da ya fi talauci daga ukuba.