Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan matan Sakandiren Yawuri 4 sun kuɓuta a hannun 'yan fashin daji
An sako ɗaliban sakandiren Yawuri huɗu a cikin mata 11 da suka rage a hannu ƙasurgumin ɗan fashin daji, Dogo Giɗe.
Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban da suka rage a hannun 'yan fashin daji, Salim Ka'oje ne ya tabbatar da haka, inda ya ce 'yan matan huɗu sun kuɓuta ne sanadin wani ƙoƙari daga mahaifan ɗaliban da kuma masu tallafa musu.
Cikin 'yan matan da suka kuɓuta in ji Salim Ka'oje, akwai Fa'iza Ahmed da Hafsat Idris da Bilham Musa da kuma Rahama Abdullahi.
Ya ce sun yi nasarar karɓo 'ya'yan nasu ne, kuma yanzu haka sun isa Birnin Kebbi a ƙoƙarin da suke yi na kai su asibiti a bincika lafiyarsu. "An sako su ne ranar Juma'a da misalin ƙarfe 4:30 ."
Ɗaliban huɗu sun shaƙi iskar 'yanci ne bayan sun kwashe kimanin shekara biyu a daji ta hanyar wata gidauniya da iyayen suka kafa.
"Sai da muka kwashe tsawon kwana shida a cikin daji, kafin mu iya karɓar su," in ji Ka'oje.
A watan Yunin 2021 ne, ƴan fashin dai a kan babura suka kutsa Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yawuri suna harbi da bindiga, kafin su kwashe ɗalibai kimanin 100 bayan sun kashe malami ɗaya.
An sako mafi yawan ɗaliban ne rukuni-rukuni bayan mahaifansu sun biya kuɗin fansa, amma 'yan fashin suka ci gaba da riƙe ɗalibai mata 11, waɗanda har rahotanni suka ce har an aurar da su.
"Da ma idan ka tuna can baya, akwai gidauniya da muka nema wurin jama'a su taimaka mana domin mu kai ƙarshen wannan matsala".
Ya ce da suka ji shiru ya yi yawa daga ɓangaren gwamnati, sai suka shiga fafutuka a matsayinsu na iyaye da kansu don ganin sun kuɓutar da 'ya'yansu.
Salim Ka'oje ya ce ta hanyar kwamitin da iyaye ne mai mutum 11 suka fara tattaunawa da ɗan fashin dajin.
"Inda muka yi ainihin shawara gaba ɗaya uwaye da mu je mu sayar da ƙaddarorinmu, mai gida mai gona, sannan mu nemi taimako wurin al'umma.
Domin mu haɗa wa'yannan kuɗaɗe da ya nema a kai mishi naira miliyan 100 domin a sako wa'yannan yara 11".
Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban Yawurin ya ce daga ƙarshe dai Allah ya ba mu sa'a, sun haɗa kuɗin da Dogo Giɗe ya nema a matsayin diyya.
Ya ce matsalar canjin kuɗi da aka yi kafin babban zaɓen Najeriya ya kawo musu cikas, inda suka ci gaba da sauraro har aka samu hukuncin Kotun Ƙoli.
Salim Ka'oje ya ce sun so karɓo 'ya'yansu kafin bikin Ƙaramar Sallah, amma matsalolin da suka gamu da su, suka kawo jinkiri.
Mun tuntuɓi gwamnati kafin mu je
A cewarsa, sun rubuta wa gwamnati wasiƙa don a ba su tsaro, su kai wa 'yan fashin daji kuɗin, amma tsawon mako biyu ba su ji wani martani ba. Matakin da ya sa suka yanke ƙaunar samun goyon bayan da suka nema daga hukumomi.
Ya ce baƙin ciki da damuwar da iyayen suke ciki, sun sanya su ɗaura ɗamar cewa ba za su taɓa dawowa gida ba, matuƙar ba a sako musu 'ya'yan nasu ba. "A can ma muka yi Sallar Idi. Inda kwamitinmu mai mutum biyar da nake jagoranta, ya yi ta gudanar da tuntuɓa".
"Mu mun tafi ne da zimmar in ma musanya ne za a yi da yaranmu, ko kuma ya ba mu yaran. Kai in ma mutuwa ne, za mu mutu saboda baƙin ciki da damuwa da suka yi wa iyaye yawa," in ji Salim Ka'oje.
Ya ce irin gudunmawar da suka samu daga hannun jama'a ta sake ƙarfafa musu gwiwar cewa duk rintsi duk wuya, "sai mun kai ga waɗannan 'ya'yan namu".
Ya ce sauran 'yan matan suna can hannun masu garkuwar a cikin daji.
A cewar Salim Ka'oje ba su yi nasarar karɓo dukkan ɗaliban ba. Ya ce shi ma 'yarsa tana cikin waɗanda suka rage a hannun 'yan fashin daji.
"Akwai wasu matsaloli ne da suka taso", in ji shi, "waɗanda bai sanar da mu ba, sai da muke je can daji".
A cewarsa, sun fuskanci turjiya da wahalhalu iri-iri da damuwa a can.
"Shi (Dogo Giɗe ne) ya tilata mu dole, dole mu karɓi mutum huɗu, mu taho da su".
Sai dai ya ce ya baro wasu iyayen a can cikin daji don su ci gaba da bibiyar sauran 'ya'yan nasu.