Ban sauya matsaya kan cire tallafin man fetur ba - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Asalin hoton, fb/Bola Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta sauya matsayarta ba game da cire tallafin man fetur, kamar yadda shugaban ƙasar ya sanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa: “Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023”

“Zamanin tallafin man fetur ya ƙare.

“Ba a ware naira tiriliyan 5.4 kan tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2024, kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a kai”.

Wannan sanarwa na zuwa ne bayan da wasu mkafafen yaɗa labaru suka bayyana cewa Najeriya na ci gaba da biyan kuɗin tallafin man fetur ta ƙarƙashin ƙasa.

Labarin ya ce wasu bayanai da aka samu sun nuna cewa gwamnati ta ware kuɗi sama da waɗanda aka ware domin biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.

Sai dai sanarwar da gwamnatin ta fitar a yau Alhamis ta ce bayanin da ake ta maganganu a kai wasu shawarwari ne kawai kan tsare-tsaren kuɗi da aka gabatar wa shugaban ƙasa domin yin nazari.

Waɗannen shawarwari ne suka janyo ruɗani?

Tun farko dai bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar Najeriya ta kashe kuɗi har naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 kan tallafin man fetur, wanda hakan ya nunka abin da ƙasar ta kashe a 2023 kan tallafin na man fetur.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sannan gwamnatin Najeriyar za ta ranto ƙarin kuɗi naira tiriliyan 6.6 domin cike giɓin kasafin kuɗin ƙasar – in ji kamfani dillancin labaru na Reuters.

Shawarwarin da aka miƙa wa shugaban ƙasar kan tsarin daidaitawa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa wanda aka yi wa take ‘Accelerated Stabilisation and Advancement Plan’ a turance – wanda ma’aikatar kuɗi tare da ɓangaren ƴan kasuwa suka rubuta, na da manufar magance ƙalubalen da suka shafi sauye-sauyen da gwamnati ta kawo domin bunƙasa ci gaban ƙasa.

A watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke tallafin man fetur, wani mataki da masu zuba jari suka jinjina mawa.

Sai dai hakan ya jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali, inda farashin sufuri da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi.

Tun daga wancan lokacin Tinubu ke fuskantar matsi daga al’umma da ƙungiyoyin ƙwadago.

Haka nan an riƙa raɗe-raɗin cewa gwamnatin na biyan tallafin man fetur ɗin a ɓoye, sai dai ta musanta hakan.

Wani abu da ya haifar da tababa kan iƙirarin gwamnatin Najeriyar kan cire tallafin man fetur shi ne yadda farashin litar man fetur bai sauya ba tun cikin watan Yulin 2023, duk kuwa da cewa an saukar da darajar naira sau biyu a hukumance.

Wani ɓangare na shawarwarin da ma'aikatar kuɗin ta gabatar wa Tinubu na cewa: "A farashin da ake yanzu, akwai hasashen cewa abin da za a kashe kan tallafin man fetur zai kai naira tiriliyan 5.4 nan da ƙarshen 2024. Wannan ya zarce abin da aka kashe - naira tiriliyan 3.6 a 2023 da kuma naira tiriliyan 2.0 a 2022".

Sai kuma ɓangaren da ya buƙaci gwamnati ta sayar da wani ɓangare na jarinta a matatun man fetur na ƙasar nan da watan Mayun 2026.

Haka nan akwai shawarar cewa gwamnati ta ƙara harajin da take karɓa daga kamfanonin yin lemon kwalba da kuma karɓar haraji kan robobin da ake amfani da su lokaci ɗaya a jefar.

Haka nan akwai shawarar cewa ya kamata gwamnati ta yi ƙoƙarin ganin an riƙa haƙo gangar man fetur miliyan biyu a kowace rana nan da watan Disamba domin bunƙasa kuɗaɗen shiga.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Duk da sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Alhamis masu nazari na cewa idan Shugaba Bola Tinubu ya amince da shawarwarin da aka gabatar masa, zai iya sanya hannu kan dokar da za ta bayar da damar fara aiwatar da su.

Kuma shawarwarin za su shafi ɓangaren lantarki da man fetur da gas da aikin gona da kiwon lafiya da kuma kasuwanci.

Najeriya na fama da tafiyar hawainiya a ɓangaren bunƙasar tattalin arziƙi, kuma na tunanin zai gaza hasashen da Tinubu ya yi na bunƙasar tattalin arziƙi da kashi shida cikin 100 a wannan shekarar.