Wace ce Kamala Harris, Shin za ta iya maye gurbin Shugaba Jo Biden?

US Vice President Kamala Harris speaks on reproductive freedom at El Rio Neighborhood Center in Tucson, Arizona, on April 12, 2024

Asalin hoton, Getty Images

Manyam mambobin jam'iyyar Democrat a Amurka na ta fama tattaunawa dangane da wanda zai maye gurbin Joe Biden a matsayin ɗan takarar shugabancin Amurka idan aka samu yanayin da ya haƙura da takarar - kuma ana ta samu kiraye-kiraye dangane da mataimakiyar shugaban, Kamala Harris a matsayin wadda za ta maye gurbin nasa.

Ana dai tunanin cewa shekarun Biden ba za su hana a zaɓe shi ba, sannan wasu kuma na cewa ya kamata a samu sabon jini a yaƙin neman zaɓe ta hanyar ɗaukar Misis Harris mai shekaru 59.

To sai dai har yanzu ba ta gama samun karɓuwa ba sannan akwai tantamar cewa ko za ta samu kwarjini da farin jinin da ake son shugaban da za a zaɓa ya kasance da shi, a aikin da ya fi kowanne girma a kasar.

Ta yaya Kamala Harris ta shiga siyasa?

Kamala Harris ta kafa tarihi a zaɓen shugaban ƙasa na 2020 ta hanyar kasancewarta mace kuma baƙa mai jinin Asiya ta farko da ta zamo mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka.

A watan Nuwamban 2021, ta yi riƙon ƙwaryar shugabancin ƙasar na mintuna 75, lokacin da likotoci ke duba Mista Biden.

Kamala Harris, left, and her younger sister Maya with their mother, Shyamala Gopalan Harris

Asalin hoton, Kamala Harris

Bayanan hoto, Kamala lokacin da take ƙarama tare da mahaifiyarta da yar uwarta Maya

An dai haifi Misi Harris ne a Oakland da ke jihar California, kuma iyayenta sun kasance ƴan cirani - mahaifinta ya kasance ɗan Jamaica inda kuma mahaifiyarta ta kasance ƴar Indiya.

To sai dai mahaifan na Kamala Harris sun rabu a lokacin tana ƴan shekara biyar inda mahaifiyarta, Shyamala Gopalan Harris wadda mai bincike ce kan cutar daji sannan kuma mai rajin kare ƴancin ɗan'adam.

Misis Harris ta ce mahaifiyarta ce ta sa ta ita da ƴaruwarta a harkoki yankin baƙar fata a Oakland.

"Mahaifiyata ta fahimci cewa tana renon ƴan mata biyu baƙar fata," kamar yadda Kamala ta rubuta a littafin tarihinta mai taken "Muna riƙe da Gaskiya". "ta gano cewa yankin da take zaune zai samar da ƴan mata baƙar fata inda ta tabbatar da mun tashi a matsayin baƙar fata masu ƙwarin gwiwa da alfahari."

Kamala ta halarci jami'ar Howard University, ɗaya daga cikin kwalejojin da a tarihi na baƙar fata ne, inda kuma ta shiga harkar siyasa kamar batutuwan da suka shafi wariyar launin fata a Afirka ta Kudu da kuma nazarin alaƙa tsakanin ƙabilun Amurka.

Alameda County deputy district attorney Kamala Harris in court in Oakland, California in 1997.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamala Harris ta zama ƙwararriyar lauya bayan kammala jami'ar University of California sannan kuma ta yi aiki a kotuna da dama a California inda har ta zama babbar mai shari'ar ta California a 2010. An kuma zaɓe ta a matsayin yar majalisar dattawa a 2016.

A 2020 Kamala ta yi takarar neman jam'iyyar Democrat ta tsayar da ita a matsayin ƴar takarar shugabancin Amurka to amma ta ajiye muradin nata tun ba a je ko'ina ba.

To sai kuma Joe Biden ya zaɓe ta a matsayin mataimakiyarsa bayan zaɓen sa da Democrat ta yi.

Joe ya bayyana ta da "Kamala gogaggiya ce, ƙwararriya, tsayayyiya kuma wadda ta tabbata mai fafutuka."

Kamala da Biden sun samu nasarar kayar da shugaba mai ci, Donald Trump da Mike Pence.

Duk da cewa ba ta kasance a gaba-gaba ba lokacin gangamin yaƙin neman zaɓenna Biden ba, sai dai kasancewar misis Harris baƙar fata ta taka rawa wajen nasarar da Biden ya samu, saboda jam'iyyar tasu ta samu kaso 90 na kuri'ar baƙar fata a ƙasar.

Me Kamala Harris ta yi a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa?

Kamala Harris and Joe Biden at a campaign event in 2020

Asalin hoton, Getty Images

A matsayinta na mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris kuma kasance shugabar majalisar dattawa sannan kuma tana da damar kaɗa kuri'a a lokacin da aka rasa rinjaye a majlaisar.

Ta kafa tarihi ta hanyar amfani da karfin iko sau 33 fiye da kowanne mataimakin shugaban ƙasar Amurka.

Mista Biden ya yi ƙarin hake kan aikin nata na mataimakiyar shugaban ƙasa, inda ya ce "Kamala Harris za ta kasance murya ta ƙarshe a cikin aji amma za ta ƙaluablanci ra'ayoyi sannan kuma ta yi tambayoyi masu wuyar sha'ani."

Ta samu ƙima ta hanyar yin ran-gadi a faɗin ƙasar daga 2022 har zuwa yanzu domin ta kare ƴancin mata na zubar da ciki tun bayan hukuncin kotun ƙoli na hana zubar da cikin.

Asylum-seekers from Central America, including children, at the US border in Texas, 2021.

Asalin hoton, Reuters

To sai dai kuma yawan abubuwan da Misis Harris ta amince da su a matsayinta na mataimakiyar shugaban ƙasa ba su taka kara sun karya ba a tsawon lokacin da ta kwashe a kujerar mataimakiyar shugaban na Amurka, inda kaso 51 na Amurkawa suke bayyana rashin kataɓus ɗinta sannan kaso 37 ne kawai suka amince ta taɓuka wani abu, kamar dai yadda wata ƙuri'ar jin ra'ayin mutanen ta nuna da kamfanin FiveThirtyEight ya haɗa.

Wakilin BBC na musamman a Amurka, Katty Kay ta ce hakan zai iya yiwuwa saboda muhimmin aikin da Biden ya ba ta shi ne na rage yawan shigar ƴan cirani da ke kwarar zuwa ƙasar daga iyakar kudu, inda kuma ta gaza cimma warware matsalar.

Me Kamala Harris ke cewa dangane da maye gurbin Joe Biden?

Wasu mambobin jam'iyyar Democrat guda biyar da ke majalisar wakilan Amurka sun yi kira a bayyane ga shugaban ƙasar mai shekaru 81 wato Joe Biden da ya haƙura da takar da yake yi ta neman tazarce a zaɓen watan Nuwamba saboda irin rashin kataɓus ɗin da ya yi a lokacin mahawarar da ya yi da Donald Trump wadda suka yi a watan Yuni.

Tim Ryan, ɗan majalisa mai wakiltar Ohio yana goyon bayan Kamala Harris ta maye gurbin Biden.

"Na yi amannar cewa makomarmu ɗoɗar ita ce Kamala Harris," kamar yadda ya rubuta a wata mujalla mai suna Newsweek. "Waɗanda suke cewa takarar Kamala Harris ta fi ta Joe Biden zamowa mai haɗari kamar yadda muka gani a wani daren daban...ba sa cikin rayuwa ta haƙiƙa."

Shi ma ɗn majalisar wakilan mai wakiltar California, Adam Schiff ya ce misis Harris za ta kasance "shugaba ta daban" kuma za ta iya kayar da Donald Trump "wanwar".

Ƙuri'ar baya-bayan nan ta nuna cewa Harris za ta iya fin Biden domin kara wa Trump na jam'iyyar Republican, duk da dai za ta fuskanci zazzafar takara.

Wata ƙuri'ar da gidan talbijin na CNN ya fitar a ranar 2 ga watan Yuli na nuni da cewa kaso 43 na masu kaɗa ƙuri'a za su ƙaunaci mista Biden ya zamo shugaban ƙasa, inda kaso 49 suka fi ƙaunar mista Trump. Ƙuri'ar ta ce idan misis Harris ce ƴar takara kaso 45 za su zaɓe ta inda kuma kaso 47 za su zaɓi mista Trump.

Sauran mutanen da ake ambato a matsayin waɗanda za su iya maye gurbin Joe Biden su ne gwamnan California, Gavin Newsom da gwamnan Michigan, Gretchen Whitmer da kuma sakataren sufurin Amurka, Pete Buttigieg.

To sai dai misis Harris ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Joe Biden, inda ta ce "Joe Biden ne ɗn takararmu. Mun yi galaba a kan Trump a baya za kuma mu sake samun nasarar a kansa, faƙad."