Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake fama da karancin likitocin kula da masu larurar kwakwalwa a Afirka
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar kula da lafiyar kwakwalwa ta duniya, ta kuma koka game da karancin likitoci a wannan bangare.
Majalisar ta ce duk da yake ana samun masu fama da wannan lalurar a tsakanin al’umma musamman a nahiyar Afirka, likitocin da ke kula da masu wannan lalura ba su da yawa musamman a Afirkan in da ta kiyasta cewa likita guda ne ke kula da masu irin wannan lalurar dubu 500 a wadan nan kasashen.
Wannan dalili ne ya sa Majalisar ta ce shi ya sa ake samun yawan samun masu kashe kansu a irin wadan nan kasashe da ba su da wadatattun likitocin kwakwalwa.
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da ke fuskantar karancin likitocin kula da masu lalurar kwakwalwa kamar yadda farfesa Shehu Sani, shugaban asibitin masu lalurar kwakwalwa da ke Sokoto, ya shaida wa BBC.
Ya ce akwai dalilan da ya sa ake karancin likitocin kwakwalwa a Najeriya wanda suka hada da rashin wadanda ke karatu a wannan bangare da kuma yadda irin wadan nan likitocin a baya bayan nan ke tafiya kasashen waje don su yi aiki a can.
Likitan ya ce likitocin na tafiya kasashen waje su yi aiki ne don an fi biyan kudi.
Farfesa Shehu Sani, ya ce saboda karancin likitocin kwakwalwa masu fama da lalurar kwakwalwa a Najeriya basa samun kulawar da ta dace sam. Ya ce,” Abu na biyu kuma yawancin asibitoci kula da masu lalurar kwakwalwa a birane suke, ba kowa ya san da su ba musamman mutanen karkara.”
Likitan ya ce, a yanzu haka Najeriya na da mutane sun kai miliyan 60 da ke fama da lalurar kwakwalwa, kuma a cikin miliyan 60 din, kashi 10 ne cikin 100 kawai ke samun kulawar da ta dace.
Dr Shehu Sani, ya ce abin takaicin shi ne da yawa daga cikin masu irin wannan lalurar basu ma san in da za su je ayi musu magani ba. Ya ce,” Idan har ana so a samu saukin masu fama da irin wannan lalura ta kwakwalwa ya kamata wadanda suke da wadata su rinka taimakawa masu karamin karfin da ke da wannan lalura. Sannan gwamnati ma ta rinka taimakawa, sai a samu sauki.”
A shekarar 2022, ranar kula da masu lalurar kwakwalwa zata mayar da hankali ne wajen ganin gwamnatoci da hukumomi da kuma daidaikun mutane sun bai wa lafiyar kwakwalwa muhimmanci domin kowa ya tsira daga tabin hankali.