Malamai 'yan kwantiragi a Nijar na cikin tsaka mai wuya saboda rashin biyansu albashi

Lokacin karatu: Minti 2

Malaman makaranta 'yan kwantaragi a Jamhuriyar Nijar na cikin hali na jiran tsammani inda wasunsu har yanzu ba a biya su albashin watan Agusta ba.

Malaman sun ce ba a biyasu albashin watan daya gabata ba gashi kuma watan Satumba na dab da karewa.

Suka ce kulluma cikin jiran tsammani suke ko za a biya su albashin na sa na watan Agusta.

Malam Lawwali Issufou, shi ne magatakardan kungiyar malamai ta kasar wato SNEN, ya shaida wa BBC cewa, suna kyauta tsammanin nan ba da jima wa ba za a biya kowanne malami dan kwantiragi albashinsa.

Ya ce," Dama dai a kodayaushe 'yan kwantiragi su ne ake biya a karshe, ana fara biyan malamai na dindindin albashi ne sai kuma a baiaya wadanda suka biyo baya, to amma damuwa ita ce a wannan karon har an shiga wani watan kuma shi ma yana dab da karewa. Amma dai mun san za a biya biya "

"Mu yanzu bukatunmu da muke son gwamnati ta cika mana su ne a mayar da wasu 'yan kwantiragin malamai na dindindin, sannan gwamnati ta rika biyanmu alawus alawus din da ya mata a biyamu." In ji shi.

Malam Lawwali Issufou, ya ce,"Abin damuwar shi ne yanzu muna dab da komawa makaranta amma kuma har yanzu ba a mayar da malamai 'yan kwantiragi na dindindin ba."

Ya ce," Baya ga wannan damuwa tamu akwai batun azuzuwa da muke gwamnati ta kara gina mana a makarantunmu, sannan a samar mana da kayan aiki a makarantu."

Magatakardan kungiyar malamai ta Nijar din wato SNEN, ya ce " Yanzu dai muna jira mu ga ko gwamnati zata cika mana alkawuran data daukar mana, ta biya malamai albashinsu wadanda ba a biya ba sannan a mayar da wasu malamai 'yan kwantiragi na dindindin da kuma biya mana alawus alawus dinmu da suka makale."

A Jamhuriyar ta nijar gwamnatin kasar ta dage lokacin komawa domin fara karatun zangon farko na 2025 zuwa 2026 zuwa ranar 1 ga watan Oktoban 2025.

Fatan malaman makarantun kasar shi ne a biya musu bukatunsu da kuma samar da yanayin karatu mai kyau ta yadda dalibai za su ji dadin karatun.

Ilimi dai shi ne ginshinkin rayuwar dand adam.

Ya ce " Idan har gwamnati ta cika mana wadannan alkawura, to muma zamu aiki cikin jin dadi da walwala mu ka yi abin da ya kamata ayi."