Haɗarin da ke tattare da shan maganin gyambon ciki na tsawon lokaci

Asalin hoton, Getty Images
Omeprazole wanda ya kasance a kasuwa na tsawon shekara 30, magani ne da yake magance matsalar zafin ciki da kuma ciwon kirji wanda yawan sinadarin acid a ciki ke haddasawa.
Hukumar sanya ido kan harkokin lafiya ta National Health Surveillance Agency ta kiyasta cewa an sha ƙwayar maganin omeprazole da ya kai miliyan 64.9 a Brazil a 2022 kaɗai.
Abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, waɗannan magunguna ana amfani da su na lokaci ƙanƙani ne kawai, aƙalla cikin wata biyu zuwa uku.
Sai dai ga mutanen da ke fama da kansa da kuma wasu cutuka, likitoci sun ce za su iya ci gaba da shan maganin ko ma wasu magunguna fiye da wannan lokaci.
Kamar yadda za ku fahimta a cikin wannan labari, shan omeprazole da kuma dangoginsa na tsawon lokaci - kamar yadda mutane suka koma yi a kowace rana ba tare da shawara daga likita ba - na da alaƙa da matsaloli da ake samu a ciki, abin da ke janyo wahala wajen narkar da sinadaran ƙara lafiyar jiki na vitamins.
Wasu bincike-bincike sun nuna cewa waɗannan matsaloli da ake samu sakamakon shan magani barkatai kan iya janyo tsananin ciwo, kamar tsananin ciwon ciki, kansa da kuma cutar mantuwa.
Sai dai, ba a karkare kan waɗannan cutuka ba a kimiyyance kuma akwai buƙatar cikakken bincike kansu.
Yawan sinadarin narkar da abinci (acid)

Asalin hoton, Getty Images
Cikinmu ya dogara ne da sinadarin acid wajen narkar da abinci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yana niƙa abinci ne yadda zai yi laushi, sannan ya narke zuwa cikin hanji.
Sai dai, a wajen wasu mutane, sinadarin yana yawa saboda yanayin cikinsu.
Ga wasu kuma, wannan zafi da suke ji yana fitowa ne a ciki a matsayin ciwon ciki ko kuma cutar gyambon ciki da ake ce wa olsa - waɗanda ke zagaye ƙewayen cikin mutum.
Har ila yau, ga wasu mutane kuma, matsalar ta wuce nan. Daga cikinsu ya yi sama zuwa wurin makoshi ne yake sanya sinadarin acid ɗin ya karu zuwa kirji da maƙogoro.
Saboda maƙogwaro ba a yi shi don riƙe sinadarin narkar da abinci na acid ba kamar ciki, hakan yake sa ya samu matsala. Hakan ne yake sa mutum ya ji zafi a kirji, tsananin zafi ko zugi a ciki zuwa makoshi da kuma tari.
A nan aikin maganin omeprazole ya fara: inda ake shan sa domin rage sinadarin acid ɗin. Sakamakon haka, ciki da hanji ba zai samu wata matsala ba saboda zafin zai ragu.
"Waɗannan magunguna na rage yawan sinadarin acid a ciki da kuma rage mutum raɗaɗin zafi," a cewar Moraes Filho wani malami a jami'ar birnin São Paulo a ƙasar Brazil.
Likitan ya ƙara da cewa, a wasu lokuta ana iya shan maganin omeprazole da wasu na'ukansa har na tsawon makonni huɗu zuwa takwas.
Ana kuma saka wannan bayani a cikin kwalayen maganin.
"An ba da shawarar shan omeprazole mai nauyin miligram 10 zuwa 20, ana kuma son a riƙa sha kafin a yi ƙarin kumallo na tsawon makonni huɗu," kamar yadda wata takarda a cikin ƙwalin maganin ta bayyana, amma ya bambanta da kamfanin da suka buga maganin.
Barazanar shan maganin na tsawon lokaci

Asalin hoton, Getty Images
Maganar ita ce: kamar yadda likitan ya bayyana, omeprazole da wasu na'ukansa na maganin abu ɗaya, sai dai ba sa magance asalin ciwo.
Batun shi ne raguwar yawan sinadarin acid ɗin da ke janyo zafi a ciki na iya ƙara ingiza shi. Sai dai, bayan lokaci na warkaswa, komai na iya komawa baya muddin ba a sauya salon rayuwa ba.
Sakamakon haka, mutane da dama na ɗaukar tsawon lokaci wajen shan maganin bisa raɗin kansu, domin rage raɗaɗin da suke ji.
Wannan yana faruwa ne ganin cewa masu shan maganin na iya samun su a kowane lokaci suke buƙata - duk da cewa ana bayyana cewa kada a sha maganin har sai likita ya rubuta wa mutum ya yi haka.
Sai dai, shan omeprazole ba tare da umarnin likita ba, yana da haɗarin kansa.
Wani bincike da aka gudanar wanda aka wallafa a 2022, ya yi kiyasin cewa akwai barazanar kamuwa da cutar kansar ciki da kashi 45 ga waɗanda suke yawan shan omeprazole idan aka kwatanta da waɗanda ba su yin haka.
Haka kuma bincike da aka yi a shekarun 1990 zuwa 2000, sun nuna cewa waɗannan magunguna suna katsalanda a wajen narkar da sinadarin vitamin B12, wanda yana da muhimmanci wajen aikin ƙwaƙwalwa.
Sakamakon haka, wasu ƙwararru na fargabar cewa ɗaukar tsawon shekaru ana shan magungunan zai iya haifar da cutar mantuwa, musamman wajen tsofaffi.
Sashen BBC Brazil ya tuntuɓi kamfanonin harhaɗa magungunan domin ji daga gare su kan damuwa da aka nuna.
Kamfanin buga magunguna na Pharmaceutical Products Industry Union, ya bayyana cewa "yana da tarihi na sharuɗa" da yake bayarwa kan yadda za a yi amfani da irin waɗannan magunguna.
"Kowane magani yana buƙatar umarni ko kuma yanda za a yi amfani da shi daga wajen likita ko kuma hukumomi."











