Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samar da sabon maganin da zai yi gaggawar magance ciwon sanyi
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital health editor, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Masana kimiyya sun ce sun samar da wani sabon maganin ciwon sanyi na gonorrhea, wanda suka ce zai zama mafi inganci cikin shekaru da dama.
Maganin mai suna Gepotidacin zai iya magancewa da kawar da ciwon wanda ake ɗauka ta hanyar jima'i.
Kuma masanan a mujallar The Lancet sun ce maganin yana da ƙarfin magance ƙwayar cutar da ke bijerewa magani.
Kamfani haɗa magunguna na GSK ne ya ɗauki nauyin binciken da kuma samar da sabon maganin.
Ciwon sanyin Gonorrhoea yana cikin manyan cututtukan da ake ɗauka wurin jima'i kuma ya yi ƙamari a Birtaniya, kuma yawan masu kamuwa da ciwon na ƙaruwa.
A 2023, an bayar da rahoton ciwon sanyin 85,000 a Ingila kawai, adadi mafi girma tun 1918.
Galibi ana magance matsalar, amma kuma akwai ƙaruwar fargaba kan tirjewar ƙwayar cutar.
A lokaci da dama ƙwayar cutar na bijerewa magani kuma masana na fargabar cewa nan gaba ba za a iya warkewa daga cutar ba saboda gagarar magani, idan har ba a samar da wani sabon maganin ba.
Rashin gaggawar magance ciwon sanyin kan iya haifar da wata illa ga lafiya, daga ciki akwai haifar matsalar rashin haihuwa.
An bayyana cewa aikin maganin Gepotidacin ya bambanta da sauran magungunan kuma yana gaggawar kawar da ciwon sanyin.
Tuni aka amince da maganin a Amurka wajen magance cututtukan sanyi.
An yi gwajin maganin ga marar lafiya 628, inda aka gwada aikin Gepotidacin da kuma sauran magungunan sanyi.
Maganin yana da ingancin gaggawar magance ciwon sanyi na gonorrhoea da sauran cututtukan sanyi da ke bijerewa magani kamar ceftriaxone.
An bayar da rahoton illolin da ake iya fuskanta idan an sha gepotidacin, amma an bayyana cewa ƙanana ne, kamar tashin zuciya da kuma ciwon ciki.
Gepotidacine dai ba shi ne kaɗai maganin sanyi da masana ke bincike a kai ba
Akwai wani da ake kira zoliflodacin wanda ake da tabbaci a kansa bayan tsallake mataki na uku na gwaji.
Sai dai a Birtaniya ana tunanin riga-kafi domin rage yaɗuwar ciwon sanyi.
A watan Nuwamban 2023, hukumomin riga-kafi JCVI sun bayar da shawarar amfani da riga-kafin MenB.
Riga-kafin da aka tsara domin magance ƙyanda ga yara JCVI ta gano cewa riga-kafin na da ingancin hana yaɗuwar ciwon sanyi da kashi 40 tsakanin mutane.
Dr Katy Sinka, shugabar sashen kula da cututtukan sanyi a UKHSA ta ce abin alfahari ne samar da sabon maganin ciwon sanyi.
"Yayin da magani ke ci gaba da bijere wa ciwon sanyi, za a iya rasa maganin warkar da ciwon a nan gaba tare da haifar da matsala ga mahaifa."
Ta ce hanya mafi ingance ta hana ciwon sanyi ita ce ta amfani da kororon roba. Idan mutum ya yi jima'i ba tare da kororon roba ba, za a yi masu gwaji.
Muhimman bayanai game da ciwon sanyi
- Ana kamuwa da ciwon sanyi tsakanin mutum da mutum ta hanyar jima'in da aka yi ba kariya
- Kusan namiji ɗaya cikin maza 10 da suka kamu da kuma rabin matan da suka kamu ba za su ji alamomin ciwon ba
- Mace mai ciki na iya yaɗa ciwon zuwa jaririnta, kuma idan ba a yi magani ba zai iya haifar da makanta ga jaririn.
- Ba za iya yaɗa ciwon ta hanyar rungumar juna
- Ba a kamuwa da ciwon ta hanyar ban-ɗaki, ko kofin shan ruwa ko kwanon cin abinci
- Ana iya sake kamuwa da ciwon duk da an magance shi a baya
Madogara: NHS
Za a iya samun ƙarin bayani a shafin NHS