'Tun suna ciki ake cinikinsu': Yadda aka bankaɗo ƙungiyar safarar jarirai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Quinawaty Pasaribu & Gavin Butler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Jakarta and Singapore
- Lokacin karatu: Minti 3
'Yansandan Indonesiya sun bankaɗo wani gungun masu safarar jarirai na duniya da ake zargi da sayar da aƙalla jarirai 25 ga masu saye a kasar Singapore tun daga shekarar 2023.
Hukumomi sun kama mutum 13 da ke da alaka da ƙungiyar a biranen Pontianak da Tangerang na Indonesiya a wannan makon, kuma sun ceto jarirai shida da ake shirin safararsu – dukkaninsu kusan shekara ɗaya da haihuwarsu.
"Ana fara ajiye jariran ne a Pontianak, sannan a shirya musu takardun izinin fita kafin a tura su zuwa Singapore," in ji Surawan, daraktan sashen binciken manyan laifuka na 'yansandan Yammacin Java, kamar yadda ya shaida wa BBC.
BBC ta tuntuɓi rundunar ƴansandan Singapore da ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar domin jin ta bakinsu, amma ba a samu amsa ba tukuna.
Rundunar 'yansandan Indonesiya ta bayyana cewa ƙungiyar safarar jariran na amfani da wata dabara ta neman iyaye ko mata masu juna biyu da ba sa da niyyar rainon jariransu – a wasu lokuta suna fara tuntuɓar su ta Facebook kafin su koma a asirce zuwa WhatsApp.
"Wasu daga cikin jariran ma an yi cinikinsu tun suna cikin mahaifa," in ji Surawan.
"Bayan sun haihu, sukan biya kuɗin haihuwa gaba ɗaya, sannan su biya uwar kuɗin kuma su ɗauki jaririn."
'Yansanda sun ce mambobin ƙungiyar sun haɗa da masu neman jarirai da za a yi safarar su da masu kula da su da wuraren da ake ajiye su; da kuma waɗanda ke shirya takardun bogi kamar katin iyali da fasfo.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan an ɗauke su daga hannun iyayensu, ana miƙa jariran ga masu kula da su na tsawon wata biyu zuwa uku, kafin a tura su zuwa Jakarta sannan Pontianak, inda ake shirya musu takardun haihuwa da fasfo, in ji 'yansanda.
An ce ana sayar da kowanne jariri tsakanin rupiah miliyan 11 na Indonesiya kimanin dala 673 kenan zuwa miliyan 16.
Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun ce ƙungiyar ta sayar da aƙalla jarirai maza 12 da mata 13, cikin ƙasar da kuma waje – mafi yawansu daga sassa daban-daban na lardin Yammacin Java a Indonesiya.
A ranar Alhamis, 'yansanda suka bayyana cewa suna aiki matuƙa domin gano masu safarar jariran a Singapore.
"Za mu sake duba bayanan jariran da aka tafi da su don sanin su wadanda suka tafi da su da yaushe suka tafi, da kuma ko su wane ne suka karɓe su a can," in ji Surawan ga manema labarai.
Ya ƙara da cewa mafi yawan bayanan da suka tattara na nuna cewa jariran sun sauya ƙasa kuma har yanzu hukumomi na neman fasfo ɗinsu.
Surawan ya shaida wa BBC cewa jariran ana samun su ne ta hanyar yarjejeniya tsakanin masu safarar da iyayensu, ba ta hanyar sace su ba.
Ya ce iyayen da suka kai ƙara cewa an sace jariransu sun yi hakan ne saboda ba a biya su kuɗin da aka yi alƙawari ba.
Ana zargin wasu daga cikin iyayen sun amince su sayar da jariransu saboda matsin tattalin arziƙi. Surawan ya ce idan aka tabbatar da yarjejeniya tsakaninsu da masu safarar, za a iya gurfanar da su kan laifin safarar mutane da karya dokar kare haƙƙin yara.
'Yansandan Indonesia sun nemi taimakon rundunar ‘yansandan duniya (Interpol) da 'yansandan Singapore don kama sauran mambobin ƙungiyar da ke waje, gami da masu sayen jariran. Za a fitar da sunayensu a matsayin waɗanda ake nema ruwa jallo tare da neman takardar kama su ta duniya.
Ai Rahmayanti daga Hukumar Kare Haƙƙin Yara ta KPAI ta ce ƙungiyoyin safarar yara na nemo mata da suka ɗauki ciki babu shiri, ko mata masu juna biyu da mazansu suka gudu suka bari da dai sauran su.
Suna amfani da harshen tausayi kamar: "Za ki iya haihuwa ki tafi da jaririnki," amma a zahiri suna bayar da kuɗi suna kuma safarar jariran ba bisa ƙa'ida ba.
Duk da cewa babu cikakken bayani daga gwamnati, KPAI ta ce safarar yara na ƙaruwa. A shekarar 2020, an samu rahoton safarar yara 11 ba bisa ƙa'ida ba yayin da a 2023, adadin ya ƙaru zuwa 59.
A cikin 2024 kuma, an gano jariran da ake shirin sayarwa a wurare kamar Depok, Yammacin Java da Bali.











