Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce inshorar motoci da 'yansandan Najeriya ke kame a kai?
A ƙarshen makon da ya gabata ne rundunar 'yansanda Najeriya ta fitar da wani umarni da ke tilastawa dukkan ɗan ƙasar amfani da inshorar motoci da ake yi wa laƙabi da 'Third party Insurance' a turance.
Wannan tsari na Inshora ba wai sabon abu ne ko wanda ba a taba ji ko gani ba, kusan kowanne mai motar idan ya je yin takardu ko sabunta takardu ana yinta.
Sai dai wasu bayanai na nuna cewa a shekarun baya-bayan nan tsarin Inshorar ya sauya, inda ake samun jihohi da ke bai wa masu mota zabi kan yin inshorar ko kuma tsallake ta a lokacin sabunta takardu.
Kowacce kasa na da tsarinta na inshora da ake yi wa ababen hawa, sannan inshorar mataki-mataki ne.
Tun bayan fitar da umarni tilasta dole kowane mai abun hawa ya rinka sabunta ko yin inshorar, mutane da dama suka shiga kafafan sada zumunta suna bayyana mabanbanta ra'ayi, wasu ma na ganin kamar wani sabon salo ne na tatsar kudi daga wurin jama'a.
Ko da yake rundunar 'yansanda ta ce ta tilasta mallakar inshorora ne saboda tsaro a kan tittunan Najeriya.
To shin mece ce wannan inshorar kuma ya aikinta ke kasancewa? Mun tattauna da wani masani kan takardun mota, Shamsudden Kabir wanda ya fede mana komai.
Tantance aikin inshora
Shamsudden ya ce a dokar Najeriya ba a amince kowacce mota ta hau titi babu inshora ba, saboda haka yake bisa tsari da dokoki na kasa da kasa.
Sannan Inshorar da ake magana na "Third Party" ita ce mafi kankanta da kowa ya wajaba ya mallaka.
Sannan abin da ake nufi da 'Third Party', shi ne idan ka yi hadari ko wani ya goga ma mota ko motar da ka goga to inshorar ce za ta yi ma gyara.
Sannan bayan wannan akwai manyan inshora da mutum ke iya yin ta bisa radi ko ganin dama, saboda kiyaye asara wanda galibi manyan kamfanoni ke yi wa motoci da kuma masu manyan motoci.
Manyan inshora na da tsada saboda kusan idan an samu matsala da mota ko sauran ababen hawa komai zai dawo kashi 100 bisa 100. Amma wannan ra'ayi ne ba wai jawabi ba.
Sai dai inshora da ta wajaba ita ce ta 'Third Party' wanda ake cewa dole kowacce mota ta kasance tana da shi kafin hawa titi.
Shamsudden ya fadamun cewa a arewacin Najeriya mutane sun yarda ko sun yi imani da kaddara don haka ba su wani damu da bibbiyar tsarin inshora ba.
Sannan akwai kamfanonin da ke yaudara su na karba kudi su bada inshora ta jabu.
Akwai kuma masu mallakar inshora saboda kada a tuhumesu a titi ba wai saboda kariya ba.
Gane inshorar kwarai
Wata babbar matsala da ake fama da ita a Najeriya ita ce rashin tsari na adana bayanai da takardun mota a kundi guda, wanda hakan ke zama kalubale wajen tattara bayanai da inshorar mutane.
Sai dai Shamsudden na cewa, akwai inshora ta kwarai da indai kana da ita akwai shafin da ake shiga na NIID sai a gani kuma ya yi amfani idan bukatar hakan ta taso.
Harkar Inshora dama kamfanoni masu zaman kansu aka barwa harkar, don haka in dai ishora ka ta gaskiya ce idan ka yi za ta hau shafin NIID na tsawon kwanaki 365.
Sannan wasu jihohin abin da ke faruwa shi ne, ana la'akari da yanayin mutane da cigaban alummarta, shiyasa wasu yankunan arewacin Najeriya ba a yinta. Amma da zaran sun tsallaka zuwa wasu jihohin ko birnin tarayya ana kame.
Sannan an shigo da 'yansanda tsarin ne domin tabbatar da kowa ya mallaki inshorar.
Akwai shafin WWW.ASKNIID.ORG wanda mutum zai iya ziyarta domin tantace kamfanonin kirki da za ka yi inshora da kuma tabbatar da cewa kayi inshorar gaskiya.
Inshorar hawa-hawa ce amma mafi kankanta na somawa ne daga naira dubu goma sha biyar, sannan duk wanda ya yi maka na da kwamisho na kashi 2.5 cikin 100 na kudin da ka biya.
Bibiyar haƙƙoƙin inshora
Shamsudden, ya ce a bisa tsari na dokar inshora ana ƙayyade kudin da inshorarka za ta ci a shekara guda.
Misali idan inshorarka gyaran da za ta yi ma bai haura dubu 100 ba, idan aka samu hadari to za a auna a gani, idan kudin ya zarta to mutum ne zai biya cikon.
Sannan kafin a biya kudin sai an duba an yi nazari an tabbatar da cewa eh lallai hadari ka yi, saboda masu zuwa da labari na daban ko rashin gaskiya.
Ya ce, "matsalar gaskiya akwai rashin wayewa kan batun inshora, sanna akwai batun addini dangane da halascinsa".
"Akwai hanyoyin bin inshora da kuma bin hakki idan mutum na ganin kamfanin da yake aiki da shi ya cuce shi ko ya jima kudinsa bai fito ba".
Shamsudden na ganin akwai bukatar mutane suke bibbiya hakki da mutunta tsarin inshora saboda yana taimakawa wajen rage asara da kuma sa mutane su kasance cikin takatsan-tsan.
Me ya sa inshora ta zama tilas?
Rundunar 'yansanda Najeriya ta ce lura da yanayin hadura da rashin kiyayye dokokin tittuna suka sanya babban sufetan 'yansanda tilasta kowa ya mallaki wannan inshorar.
Sannan an fahimci akwai masu yi na jabun, don haka wannan wata hanya ce ta sake gyara da inganta tsarin inshora da dokokin tittuna da tsaro
Kuma dokar a yanzu ta sanya kame da cin tarar duk wanda ya hau hanya da motarsa ba tare da ya mallaki inshora ba.
Duk da dai wannan umarni bai yi wa wasu 'yan kasar dadi ba musamman wadanda ba su fahimci yadda tsarin yake aiki ba, akwai masu ganin ya kamata a sake fadakarwa da kuma bibiyar kamfanonin inshorar wajen tabbatar da cewa suna aikinsu yadda ya kamata.
Akwai zarge-zarge sosai a harkar inshorar motoci, sai dai kwararu irin su Shamsudden na ganin mutane ya kamata su tashi tsaye su bibbiye lamari, sanna su ke cin gajiyar tsarin da kuma kai kara kamfanin da ya saba yarjejeniya ko tsarin da suke kai.