Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda gyaran dokar zaɓen Najeriya ke ci gaba da janyo takaddama
Manyan jam'iiyun adawa a Najeriya sun soki gyaran da majalisar dokokin ƙasar ta yi wa dokar zaɓe, musamman rashin amincewa da aike sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet daga runfunan zaɓen.
Jam'iyyun adawa sun bayyana matakin a amatsayin babbar barazana ga turbar dimokuraɗiyyar Najeriya.
A ranar Laraba 4 ga watan Faburairu majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin dokar zaɓe ta 2022, bayan gyaran da ta yi mata.
Majalisar ta gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokar zaɓen, amma ga alama abin da ya fi ɗaukar hankalin ƴan adawa shi ne dambarwar tura sakamakon zaɓen kai tsaye ta na'ura daga runfunan da aka kaɗa ƙuri'u, wani abu da suke ganin an tsara shi ne domin biyan buƙatun jam'iyya mai mulki.
Jam'iyyun da suka haɗa da PDP da ADC da kuma NNPP sun fitar da wata sanarwar mai nuni da gyaran dokar zaɓen bai tafi kamar yadda ƴan Najeriya ke fata ba.
Sakataren Sanata Umar Tsauri ɗan kwamitin amintattu ne na jam'iyyar PDP na ƙasa, kuma ya shaidawa BBC cewa wannan yunƙuri ne na samar da hanyar magudin zaɓe.
Ya ce ''ba mu yi mamamkin wannan ba, da ma haka muke tsammani, haka aka aikata, amma dai ba za a yi shiru ba,''
Itama jam'iyar ADC ta yi irin wannan ƙarafi, inda Faisal Kabir, ɗaya daga cikin masu magana da yawunta ya ce ''matakin kamar mayar da hannun agogo baya ne.''
''Duk wata hanya da za ta inganta zaɓen Najeriya, mun san dama wannan gwamnatin ba za ta yi ba domin cewa idan dai aka yi zaɓe sahihi a Najeriya, to wannan gwamnatin ƙarshen ta ya zo.'' in ji Faisal Kabir.
Jam'iyyun adawar sun yi misali da yadda a kwanan nan Jam'iyyar APC mai mulki ta ƙaddamar da aikin sabinta rijistar mambobinta, wanda kuma aiki ne mai gudana a sassan Najeriya ta hanyar amfani da na'ura, tsarin da suke ganin za a iya amfani da shi wajen aikewa da sakamakon zaɓe.
Ƴan adawar sun yi iƙirarin cewa jam'iyyar ACP wadda ke da rinjaye a majalisar dokokin tarayya, ta razana da zaɓe mai zuwa domin haka ta ke zaƙulo hanyoyin magudi.
A cewar su wannan na faruwa ne saboda jama'a sun dawo daga rakiyar APC.
Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa'adin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar jadawalin zaɓe daga kwana 360 zuwa 180.
Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar na rage kwanakin da ake buƙatar hukumar INEC ta fitar da sanarwar zaɓe.
Monguno ya bayyana cewa rage wa'adin kwanakin ya zama dole domin hukumar INEC ta cika sharuɗɗan da ake buƙata wajen fitar da sanarwar, inda ya ce tuni aka makara idan aka yi amfani da kwana 360 bisa la'akari da babban zaɓe mai zuwa.
Majalisar dai ta fuskanci matsin lamba kan abin da wasu suka bayyana a matsayin jan ƙafa wurin amincewa da ƙudirin dokar zaɓen.
Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta arewa, kuma wakili a kwamitin majalisar dattawa kan gyare-gyare dokar zaɓen ya shaida wa BBC cewa tun bayan zaɓen 2023 ne aka fara nazarin tsohuwar dokar zaɓen domin aiwatar da gyare-gyaren da aka buƙata domin ƙara inganta sahihancin zaɓukan ƙasar.
"Tun bayan zaɓen 2023 aka fara wannan aiki. Sannan an zauna tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ciki har da ƙungiyoyin mata da matasa da sauran su kafin muka kai ga wannan matakin da ake ciki."
Ya ƙara da cewa sun yi aiki tare da majalisar wakilai, "muna aikinmu, a can majalisar wakilai ma sun zauna domin aiwatar da gyare-gyaren da suka ga sun dace."