Ana kashe mata 140 kullum a duniya - MDD

Mace na cikin takaici

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Rahoto, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A duk minti 10 ana kashe mace ɗaya a faɗin duniyar nan - kamar yadda rahoto na baya-bayan nan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar daga alƙalumanta na 2023, a kan kisan mata a duniya - hakan na nufin a kullum ana kashe mata da 'yan mata 140 kenan.

Bugu da ƙari rahoton ya ƙalailaice cewa kashi 60 cikin ɗari na matan da ke gamuwa da wannan ta'addanci na kisa, suna samunsa ne ta hannun namijin da ya kasance miji ko abokin alaƙarta ko ma danginta.

Majalisar ta fitar da wannan rahoto ne yayin tunawa da ranar cin zarafin mata ta duniya - 25 ga watan Nuwamba.

Wannan ta'ada ta kisan mata wadda ita ce mafi ƙololuwar cin zarafin mata da 'yan mata, duk da irin matakan da ake ɗauka tana ci gaba da ta'azzara a sassan duniya da dama.

A faɗin duniya mata da 'yan mata 85,000 aka kashe da niyya a shekarar ta 2023.

Alƙaluman sun nuna cewa nahiyar Afirka ita ce ta farko wajen yawan matan da ake kashewa ta wannan hanya, sai kuma Amurka ta Arewa da ta Kudu ke bi mata baya sannan sai nahiyar Osheniya (Oceania) da ke zaman ta uku.

A Turai da yankin nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu yawancin mata ana kashe su ne a gida, wato mazajensu ko samarinsu ne ke kashe su, yayin da a sauran wurare kuma 'yan uwa ko danginsu ne ke kashe su.

Halin da mata suke ciki a Najeriya

Taro na kallon wata mace

Asalin hoton, Getty Images

Kasancewar rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa a Afirka matsalar ta cin zarafin mata da ma kashe su take, BBC ta tattauna da wasu matan da suka gamu da matsalar ta cin zarafi a hannun waɗanda suke tare da su - a nan mazajensu na aure ne.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata uwargida daga jihar Kaduna wadda muka sakaya sunanta ta sheda wa BBC cewa ita ta fara samun saɓani ne da mijinta bayan da suka je ƙauye suka zauna sakamakon rikicin addini da ƙabilanci a birnin da suke da zama, wannan ya sa mijinta ya neme su ci gaba da zama a ƙauyen maimakon su koma bayan ƙura ta lafa.

''Muna zaman lafiya da mijina a cikin gari amma lokacin da muka je ƙauye bayan da aka yi rikici, wannan zama da muka yi ina ganin 'yan uwanshi da danginsa ne suka ba shi shawara mu bar gari mu zauna a wannan ƙauye,'' in ji ta.

Ta ce ganin ita tana aiki a wani kamfani kuma kafin aurensu ba su yi cewa a ƙauye za su zauna ba, wannan ne ya sa ta bijire wa mijin nata ta shirya komawa birni, daga nan ne ta fara samun saɓani da mijin nata da kuma iyayensa har ma da danginsa.

Matar ta sheda wa BBC cewa tun daga wannan lokaci da suka fara samun saɓani da mijin ya zama kamar yana jin haushinta kodayaushe har ta kai yana zagi da farfasa kayan gidan har ma wata rana ya ɗauki rufan zafi ya watsa mata da ita da jaririnta a kan wani ɗan saɓani.

Matsalar Uwar Miji

Matar ta sheda wa BBC cewa a lokacin da ta kai ƙara wajen mahaifiyar mijinta kan abubuwan da yake yi mata ta ce ta yi mamaki kan yadda surukartata ta goyi bayan mijinta a kan sabanin da suke samu.

''Kai ni ina ganin matar da take da aiki ko kuma sana'a akwai kamar baƙin ciki ko ƙyashi da ake yi mata, ni ina ganin abin da na samu kaina a ciki kenan,'' in ji ta.

Ta ce saboda ita tana aiki duk da shi ma mijin yana aiki to amma ana ganin aikin da take yi zai sa ta rena shi, wannan ne ya sa danginsa da iyayensa suke nuna mata tsana, har ta kai shi ma mijin daga baya ya bi bayan dangin nasa suka fara samun saɓani, inda yake yawan hantararta.

Fakewa da addini

A tattaunawar da BBC matar ta ce wani abu da ake amfani da shi wajen hana mata neman 'yancinsu ko fitar da su daga cikin matsala ta cin zarafi shi ne yadda ta ce ana fakewa da addini ana hana mata fitowa fili su bayyana halin da suke ciki a zamantakewar musamman aure.

''An cika amfani da addini nan da nan sai a karanto ma aya a ce ba ka yi haka ba ka yi haka ba,'' in ji ta.

Shiga tsakani na hukumomi

Halin da wannan mata ta samu kanta na saɓani da mijinta abin da ya kai ga tsangwama da cin zarafi da duka daga mijin nata ta ce ya kai da har sai da suka ƙaurace wa juna na wasu watanni kafin daga bisani suka koma suka zauna tare bayan abu ya lafa.

To amma wannan ya kasance ne bayan da hukumomi da masu kare haƙƙin ɗan'Adam suka shiga lamarin, inda a yanzu aka samu maslaha da zaman lafiya tsakanin matar da mijin nata.

Ta ƙara da cewa: ''Har yanzu wasu suna zagina, wai me ya sa ban rufa asiri ba na je na tona wa mijina asiri har yanzu wata shugabarmu a wurin aiki ta ce ta ji labari ai na ba mata kunya abin nan da na yi, na kai ƙarar mijina.''

''Ni dai na gode a yanzu muna zaman lafiya matakin da na ɗauka duk da cewa ba a rasa saɓani amma ba maganar ɗaga hannu a yi duka.''

Ƙarin aure ne ya janyo saɓani har mijina ya mare ni :

Ita kuwa wata matar da BBC ta tattauna da ita, wadda ita ma muka ɓoye sunanta domin sirrintawa, ta ce suna zaune lami lafiya da mijinta har da 'ya'ya biyu sai kawai ya ƙara aure, lamarin da ya kai ga saɓani tsakaninta da mijin.

''Tun da ya ƙara aure dai ban gane komai ba dai haka, maganar yara ma dai babu kula ba wani abin kirki har ya kai dai wata rana ya mare ni, fuskata ta tashi, sakamakon sa-in-sa da muke yi'' in ji ta.

Matar ta ce daga nan ne ta garzaya wajen ƙungiyar kare haƙƙin mata da yara da ke jihar Kaduna - GIWAC (Global Initiative for Women and Children), inda aka sasanta su.

''A yanzu muna zaune lafiya duk da cewa ba a rasa 'yan matsaloli nan da can amma dai lafiya muke kuma hatta wasu abubuwan na kyautata da da ba ya min ya yi min bayan da aka shiga tsakani.'' Kamar yadda ta sheda wa BBC