Man United da Aston Villa na hamayya kan Endrick, Napoli na zawarcin Mainoo

Endrick

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa ta bi sahun Manchester United wajen neman ɗaukar aron ɗan wasan gaba na Brazil Endrick mai shekara 19 daga Real Madrid a watan Janairu. (Daily Star on Sunday)

Sai dai kuma Lyon ce ke kan gaba wajen ganin ta ɗauki Endrick, wanda ke da sha'awar tafiya don samun gurbin buga wasanni da kuma inganta damarsa ta shiga tawagar Brazil da za ta buga gasar cin kofin duniya a 2026. (Foot Mercato)

Napoli ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a matsayin aro a watan Janairu. (Mirror)

Manchester United na shirin kara kaimi wajen neman ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22, daga Nottingham Forest a watan Janairu, amma za ta iya fuskantar hamayya daga Chelsea da Manchester City da kuma Newcastle United. (Caught Offside)

Wakilan ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford sun riga sun tattauna da Barcelona game da sharuɗɗan kwantiragi, idan har kulob ɗin na Sifaniya ya yanke shawarar mayar da zaman aron ɗan wasan mai shekara 28 daga Manchester United zuwa na dindindin. (Sport)

Ana tunanin zai zame wa Aston Villa dole na mayar da zaman aron ɗan wasan Ingila Harvey Elliott daga Liverpool zuwa na dindindin idan har dan wasan mai shekara 22 ya buga wasanni 10 a kungiyar ta Midlands. (Independent).

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Paris FC na zawarcin ɗan wasan tsakiyar ƙasar Faransa N'Golo Kante mai shekara 34, wanda kwantiraginsa da Al-Ittihad zai ƙare a bazara mai zuwa. (Foot Mercato)

Ɗan wasan gaban Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 24, yana da har zuwa kasuwar musayar ƴanwasa ta watan Janairu don gamsar da AC Milan cewa ya cancanci ci gaba da zama a ƙungiyar idan ba haka ba za a sanya shi a kasuwa. (Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan gaba na Italiya Lorenzo Insigne, mai shekara 34, ya kasance ɗan wasa mai zaman kansa bayan ya bar Toronto FC, amma ya nuna sha'awarsa ta komawa Lazio. (Football Italia)