Ambaliya a Kebbi: 'Ban taɓa ganin asara irin wannan ba'

Lokacin karatu: Minti 3

Ɗaruruwan manoman shinkafa a jihar Kebbi da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da ƙirga asara bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta lalata musu gonaki.

Manoman waɗanda suka fito daga yankunan ƙananan hukumomin Yauri da Ngaski da kuma Shanga a jihar sun shiga mummunar damuwar sakamakon ambaliyar da ta haddasa musu asarar miliyoyin naira.

Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke kan gaba a noman shinkafa.

Ambaliyar - wadda ta auku sakamakon tumbatsar kogin Neja - ta shafe ɗaruruwan gonakin shinkafa, lamarin da ya dakushe fatan manoman.

Girman matsalar

Shugaban ƙaramar hukumar Yauri, Hon. Abubakar Shu'aibu ya ce ambaliyar ta cinye gonakin manoma masu dimbin yawa.

"Garin Yauri gari ne da ya yi fice a harkar noman shinkafa a fadin Najeriya, amma kusan duk inda ake noman shinkafa a garin ambaliyar ta shiga tare da cinye gonaki''.

Hon. Abubakar ya ce a tarihinsa bai taɓa ganin ambaliyar da ta haddasar hasarar dukiya kamar wannan ba.

''Akwai manoman da ke noma buhu 500 ko 400 ko 300, amma wani ko buhu biyar ba zai samu ba a bana'', in ji shi.

A nasa ɓangare sarkin Noman Jihar Kebbi, Abdullahi Argungu mai Gandu ya ce matsalar ta munana, saboda gonaki amsu yawan gaske sun salwanta.

''Zai yi wahala mutum ya iya ƙiyasta irin asarar da manoma suka tafka sakamakon wannan ambaliya'', in ji shi.

Me ya janyo ambaliyar?

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce abin da ya janyo ambaliyar shi ne yanayin lokacin damina.

Sai dai ya alaƙanta ambaliyar da karyewar gadojin da ke yankin.

''Ruwa ne da ya taho ba daga jiharmu kaɗai ba, ruwa ne da ya taho daga jihohin Zamfara da Neja'', in ji shi.

Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa tumbatsar kogin Neja ne ta haddasa wannan ambaliya.

Hon Abubakar ya ce kuma dama tuni gwamnatin jihar ke aikin kwashe kwatocin da ke faɗin jihar, a wani mataki na ƙoƙarin daƙile ambaliyar.

Ta yaya hakan zai shafi noman shinfaka a Kebbi?

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce ambaliya ta janyo mummunar asara ga harkar noman shinkafa a yankin.

Ya ƙara da cewa noma shi ne babban abin da al'ummar yankin Yauri suka dogara da shi.

''Muna yin noma har sau uku a kowace damina, za mu yi na damina, sannan mu yi na rani har guda biyu kafin kewayowar damina'', in ji shi.

To amma ya ce wannan iftila'i dole zai shafi sauran noman sakamakon asarar da manoman suka yi.

''Dama daga wannan noman ne manoma ke samun kuɗin da za su sayi takin wani noman da ke tafe'', in ji shi.

Ya ce a lokacin shinkafa a kowace rana akan samu tirela kimanin 50 zuwa 60 masu ɗaukar buhun shinkafa 500 zuwa 600, da ke fita da shinkafa daga kasuwar.

''Wannan baya ga ƙananan motoci da kuma kanta-kanta masu fita da shinkafa'', in ji shi.

Ya ce mutanen yankin na noma kuma suna samun amfanin da ba za su iya cinsa ba, sai dai su sayar domin biyan buƙatunsu na rayuwa.